2 Coríntios 8 – NVI-PT & HCB

Nova Versão Internacional

2 Coríntios 8:1-24

Incentivo à Contribuição

1Agora, irmãos, queremos que vocês tomem conhecimento da graça que Deus concedeu às igrejas da Macedônia. 2No meio da mais severa tribulação, a grande alegria e a extrema pobreza deles transbordaram em rica generosidade. 3Pois dou testemunho de que eles deram tudo quanto podiam e até além do que podiam. Por iniciativa própria 4eles nos suplicaram insistentemente o privilégio de participar da assistência aos santos. 5E não somente fizeram o que esperávamos, mas entregaram-se primeiramente a si mesmos ao Senhor e, depois, a nós, pela vontade de Deus. 6Assim, recomendamos a Tito que, assim como ele já havia começado, também completasse esse ato de graça da parte de vocês. 7Todavia, assim como vocês se destacam em tudo: na fé, na palavra, no conhecimento, na dedicação completa e no amor que vocês têm por nós8.7 Alguns manuscritos dizem e em nosso amor por vocês., destaquem-se também neste privilégio de contribuir.

8Não estou dando uma ordem, mas quero verificar a sinceridade do amor de vocês, comparando-o com a dedicação dos outros. 9Pois vocês conhecem a graça de nosso Senhor Jesus Cristo que, sendo rico, se fez pobre por amor de vocês, para que por meio de sua pobreza vocês se tornassem ricos.

10Este é meu conselho: convém que vocês contribuam, já que desde o ano passado vocês foram os primeiros, não somente a contribuir, mas também a propor esse plano. 11Agora, completem a obra, para que a forte disposição de realizá-la seja igualada pelo zelo em concluí-la, de acordo com os bens que vocês possuem. 12Porque, se há prontidão, a contribuição é aceitável de acordo com aquilo que alguém tem, e não de acordo com o que não tem.

13Nosso desejo não é que outros sejam aliviados enquanto vocês são sobrecarregados, mas que haja igualdade. 14No presente momento, a fartura de vocês suprirá a necessidade deles, para que, por sua vez, a fartura deles supra a necessidade de vocês. Então haverá igualdade, 15como está escrito: “Quem tinha recolhido muito não teve demais, e não faltou a quem tinha recolhido pouco”8.15 Êx 16.18.

A Coleta para os Crentes da Judeia

16Agradeço a Deus ter ele posto no coração de Tito o mesmo cuidado que tenho por vocês, 17pois Tito não apenas aceitou o nosso pedido, mas está indo até vocês, com muito entusiasmo e por iniciativa própria. 18Com ele estamos enviando o irmão que é recomendado por todas as igrejas por seu serviço no evangelho. 19Não só por isso, mas ele também foi escolhido pelas igrejas para nos acompanhar quando formos ministrar esta doação, o que fazemos para honrar o próprio Senhor e mostrar a nossa disposição. 20Queremos evitar que alguém nos critique quanto ao nosso modo de administrar essa generosa oferta, 21pois estamos tendo o cuidado de fazer o que é correto, não apenas aos olhos do Senhor, mas também aos olhos dos homens.

22Além disso, estamos enviando com eles o nosso irmão que muitas vezes e de muitas maneiras já nos provou que é muito dedicado, e agora ainda mais, por causa da grande confiança que ele tem em vocês. 23Quanto a Tito, ele é meu companheiro e cooperador entre vocês; quanto a nossos irmãos, eles são representantes das igrejas e uma honra para Cristo. 24Portanto, diante das demais igrejas, demonstrem a esses irmãos a prova do amor que vocês têm e a razão do orgulho que temos de vocês.

Hausa Contemporary Bible

2 Korintiyawa 8:1-24

An ƙarfafa bayarwa

1To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya. 2Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci. 3Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu, 4sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka. 5Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah. 6Ganin haka sai muka roƙi Titus, da yake shi ne ya riga ya tsiro da wannan aikin alheri a cikinku, sai yă ƙarasa shi. 7To, da yake kun fiffita a kowane abu cikin bangaskiya, cikin magana, cikin sani, cikin dukan ƙwazo, da kuma cikin ƙaunarku dominmu, sai ku fiffita a wannan aikin alheri ma.

8Ba umarni nake ba ku ba, sai dai ina so in gwada gaskiyar ƙaunarku ne, ta wurin kwatanta ta da aniyar waɗansu. 9Gama kun san alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi cewa ko da yake shi mawadaci ne, duk da haka, ya zama matalauci saboda ku, domin ta wurin talaucinsa, ku zama mawadata.

10Ga shawarata a kan abin da ya fi muku kyau a wannan al’amari. Bara ku kuka fara bayarwa, kuka kuma zama na farko wajen niyyar yin haka. 11Yanzu sai ku ƙarasa aikin da irin niyyar da kuka fara, ku yi haka gwargwadon ƙarfinku. 12Gama in da niyyar bayarwa, za a karɓi bayarwa bisa ga abin da mutum yake da shi, ba bisa ga abin da ba shi da shi ba.

13Ba nufi nake yi a sawwaƙe wa waɗansu, ku kuwa a jibga muku nauyin ba. Amma ya yi kyau dai 14a raba daidai wa daida, sai ku taimake su a yanzu da yalwarku saboda rashinsu. Wata rana su ma su taimake ku da yalwarsu saboda rashinku, don a daidaita al’amari, 15kamar yadda yake a rubuce cewa, “Wanda ya tara da yawa, bai tara fiye da bukatarsa ba, wanda kuma ya tara kaɗan, bai kāsa masa ba.”8.15 Fit 16.18

An aika Titus zuwa Korint

16Ina gode wa Allah, wanda ya sa a zuciyar Titus, irin kula da nake da shi dominku. 17Ba kawai ya yarda yă je wurinku kamar yadda muka roƙe shi yă yi ba, amma ya so yă zo kamar yadda ya riga ya yi niyya. 18Ga shi mun aiko ɗan’uwanmu nan tare da shi, wanda ikkilisiyoyi duka suna yabo saboda hidimarsa ga bishara. 19Ba kuwa haka kaɗai ba, har ma ikkilisiyoyi sun zaɓe shi yă riƙa tafiya tare da mu kan wannan aikin alheri da muke yi saboda ɗaukakar Ubangiji, da kuma nuna kyakkyawar niyyarmu. 20Muna gudu kada wani yă zarge mu, a kan yadda muke gudanar da wannan kyautar da aka bayar hannu sake. 21Gama muna iya ƙoƙari mu yi abin da yake daidai, ba a gaban Ubangiji kaɗai ba, amma a gaban mutane ma.

22Ban da wannan kuma, mun aiko da ɗan’uwanmu tare da su, wanda ya sha tabbatar mana da ƙwazonsa ta hanyoyi iri-iri, musamman yanzu, domin ya amince da ku da gaske. 23Game da Titus kuma, shi abokin tarayyata ne, da kuma abokin aikina a cikinku; game da ’yan’uwanmu kuwa, su wakilai ne na ikkilisiyoyi, kuma su masu ɗaukaka Kiristi ne. 24Saboda haka, ku nuna wa waɗannan mutane shaidar ƙaunarku, da kuma dalilin taƙamarmu da ku, domin ikkilisiyoyi su gani.