Mark 13 – NIVUK & HCB

New International Version – UK

Mark 13:1-37

The destruction of the temple and signs of the end times

1As Jesus was leaving the temple, one of his disciples said to him, ‘Look, Teacher! What massive stones! What magnificent buildings!’

2‘Do you see all these great buildings?’ replied Jesus. ‘Not one stone here will be left on another; every one will be thrown down.’

3As Jesus was sitting on the Mount of Olives opposite the temple, Peter, James, John and Andrew asked him privately, 4‘Tell us, when will these things happen? And what will be the sign that they are all about to be fulfilled?’

5Jesus said to them: ‘Watch out that no-one deceives you. 6Many will come in my name, claiming, “I am he,” and will deceive many. 7When you hear of wars and rumours of wars, do not be alarmed. Such things must happen, but the end is still to come. 8Nation will rise against nation, and kingdom against kingdom. There will be earthquakes in various places, and famines. These are the beginning of birth-pains.

9‘You must be on your guard. You will be handed over to the local councils and flogged in the synagogues. On account of me you will stand before governors and kings as witnesses to them. 10And the gospel must first be preached to all nations. 11Whenever you are arrested and brought to trial, do not worry beforehand about what to say. Just say whatever is given you at the time, for it is not you speaking, but the Holy Spirit.

12‘Brother will betray brother to death, and a father his child. Children will rebel against their parents and have them put to death. 13Everyone will hate you because of me, but the one who stands firm to the end will be saved.

14‘When you see “the abomination that causes desolation”13:14 Daniel 9:27; 11:31; 12:11 standing where it13:14 Or he does not belong – let the reader understand – then let those who are in Judea flee to the mountains. 15Let no-one on the housetop go down or enter the house to take anything out. 16Let no-one in the field go back to get their cloak. 17How dreadful it will be in those days for pregnant women and nursing mothers! 18Pray that this will not take place in winter, 19because those will be days of distress unequalled from the beginning, when God created the world, until now – and never to be equalled again.

20‘If the Lord had not cut short those days, no-one would survive. But for the sake of the elect, whom he has chosen, he has shortened them. 21At that time if anyone says to you, “Look, here is the Messiah!” or, “Look, there he is!” do not believe it. 22For false messiahs and false prophets will appear and perform signs and wonders to deceive, if possible, even the elect. 23So be on your guard; I have told you everything in advance.

24‘But in those days, following that distress,

‘ “the sun will be darkened,

and the moon will not give its light;

25the stars will fall from the sky,

and the heavenly bodies will be shaken.”13:25 Isaiah 13:10; 34:4

26‘At that time people will see the Son of Man coming in clouds with great power and glory. 27And he will send his angels and gather his elect from the four winds, from the ends of the earth to the ends of the heavens.

28‘Now learn this lesson from the fig-tree: As soon as its twigs get tender and its leaves come out, you know that summer is near. 29Even so, when you see these things happening, you know that it13:29 Or he is near, right at the door. 30Truly I tell you, this generation will certainly not pass away until all these things have happened. 31Heaven and earth will pass away, but my words will never pass away.

The day and hour unknown

32‘But about that day or hour no-one knows, not even the angels in heaven, nor the Son, but only the Father. 33Be on guard! Be alert13:33 Some manuscripts alert and pray! You do not know when that time will come. 34It’s like a man going away: he leaves his house and puts his servants in charge, each with their assigned task, and tells the one at the door to keep watch.

35‘Therefore keep watch because you do not know when the owner of the house will come back – whether in the evening, or at midnight, or when the cock crows, or at dawn. 36If he comes suddenly, do not let him find you sleeping. 37What I say to you, I say to everyone: “Watch!” ’

Hausa Contemporary Bible

Markus 13:1-37

Alamun ƙarshen zamani

(Mattiyu 24.1,2; Luka 21.5,6)

1Da yake barin haikalin, sai ɗaya daga cikin almajiransa ya ce masa, “Malam! Dubi irin manya-manyan duwatsun nan! Ka ga irin gine-ginen nan masu kyau mana!”

2Yesu ya amsa ya ce, “Ka ga dukan manyan gine-ginen nan? Ba wani dutse a nan, da za a bari kan wani da ba za a rushe ba.”

(Mattiyu 24.3-14; Luka 21.7-19)

3Da Yesu yana zaune a kan Dutsen Zaitun da yake ɗaura da haikali, sai Bitrus, Yaƙub, Yohanna da kuma Andarawus, suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, 4“Ka gaya mana, yaushe waɗannan abubuwa za su faru? Wace alama ce kuma za tă nuna cewa, duk waɗannan suna dab da cikawa?”

5Sai Yesu ya ce musu, “Ku lura fa kada wani yă ruɗe ku. 6Da yawa za su zo a cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne shi.’ Za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 7Sa’ad da kuka ji labarun yaƙe-yaƙe da jita-jitar yaƙe-yaƙe, kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru. Amma ƙarshen tukuna. 8Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki kuma yă tasar wa mulki. Za a yi girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam, a kuma yi yunwa. Waɗannan dai mafarin azabar naƙuda.

9“Dole ku yi zaman tsaro. Za a ba da ku ga hukuma, a kuma bulale ku a majami’u. Saboda ni kuma, za ku tsaya a gaban gwamnoni da sarakuna, domin ku ba da shaida a gabansu. 10Dole sai an fara yin wa’azin bishara ga dukan al’ummai. 11Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.

12“Ɗan’uwa zai ba da ɗan’uwa a kashe. Mahaifi zai ba da ɗansa. ’Ya’ya za su tayar wa iyayensu, su kuma sa a kashe su. 13Dukan mutane za su ƙi ku saboda ni, amma wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto.

(Mattiyu 24.15-21; Luka 21.20-24)

14“Sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama, mai kawo hallaka’13.14 Dan 9.27; Dan 11.31; Dan 12.11 tsaye inda13.14 Ko kuwa shi; haka ma a aya 29 bai kamata ba (mai karatu ya gane), to, sai waɗanda suke a Yahudiya su gudu zuwa duwatsu. 15Kada wani da yake kan rufin gidansa yă sauka, ko yă shiga gida don yă ɗauki wani abu. 16Kada wani da yake gona kuma yă koma don ɗaukar rigarsa. 17Kaiton mata masu ciki, da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin! 18Ku yi addu’a, kada wannan yă faru a lokacin sanyi. 19Domin waɗancan kwanakin za su zama kwanaki na baƙin ciki, waɗanda ba a taɓa yin irinsa ba tun farkon halitta, har yă zuwa yanzu, ba kuwa za a sāke yin irinsa ba.

20“Da ba don Ubangiji ya rage kwanakin nan ba, da ba wani da zai tsira. Amma saboda zaɓaɓɓu waɗanda ya zaɓa, sai ya rage kwanakin. 21A lokacin nan, in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko kuwa, ‘Duba, ga shi can!’ Kada ku gaskata. 22Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 23Amma ku kula! Na dai gaya muku kome tun da wuri.

(Mattiyu 24.29-31; Luka 21.25-28)

24“Amma waɗancan kwanaki, bayan baƙin azaban nan,

“ ‘rana za tă yi duhu,

wata kuma ba zai ba da haskensa ba;

25taurari za su fāffāɗo daga sararin sama.

Za a kuma girgiza manyan abubuwan da suke a sararin sama.’13.25 Ish 13.10; Ish 34.4

26“Sa’an nan, mutane za su ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin gizagizai da iko, da ɗaukaka mai girma. 27Zai kuma aiko mala’ikunsa su tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga iyakar duniya har yă zuwa iyakar sama.

(Mattiyu 24.32-35; Luka 21.29-33)

28“To, sai ku yi koyi da itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi, ganyayensa kuma suka toho, kun san cewa damina ta yi kusa ke nan. 29Haka ma, in kuka ga waɗannan abubuwa suna faruwa, ku san cewa ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. 30Gaskiya nake gaya muku, zamanin nan ba zai shuɗe ba sai duk abubuwan nan sun faru. 31Sama da ƙasa za su shuɗe, amma kalmomina ba za su taɓa shuɗewa ba.

Ba a san rana ko sa’a ba

(Mattiyu 24.36-44)

32“Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai. 33Ku lura fa! Ku zauna a shirye! Don ba ku san lokacin da shi zai zo ba. 34Yana kama da mutumin da zai yi tafiya. Yakan bar gidansa a hannun bayinsa, kowa da nasa aikin da aka sa shi, yă kuma ce wa wanda yake gadin ƙofa, yă yi tsaro.

35“Saboda haka, sai ku zauna a shirye, domin ba ku san lokacin da maigidan zai dawo ba, ko da yamma ne, ko da tsakar dare ne, ko lokacin da zakara na cara ne, ko kuma da safe ne. 36In ya zo kwaram, kada ka bari yă tarar da kai kana barci. 37Abin da na faɗa muku, na faɗa wa kowa. ‘Ku yi tsaro!’ ”