Mark 12 – NIVUK & HCB

New International Version – UK

Mark 12:1-44

The parable of the tenants

1Jesus then began to speak to them in parables: ‘A man planted a vineyard. He put a wall round it, dug a pit for the winepress and built a watchtower. Then he rented the vineyard to some farmers and moved to another place. 2At harvest time he sent a servant to the tenants to collect from them some of the fruit of the vineyard. 3But they seized him, beat him and sent him away empty-handed. 4Then he sent another servant to them; they struck this man on the head and treated him shamefully. 5He sent still another, and that one they killed. He sent many others; some of them they beat, others they killed.

6‘He had one left to send, a son, whom he loved. He sent him last of all, saying, “They will respect my son.”

7‘But the tenants said to one another, “This is the heir. Come, let’s kill him, and the inheritance will be ours.” 8So they took him and killed him, and threw him out of the vineyard.

9‘What then will the owner of the vineyard do? He will come and kill those tenants and give the vineyard to others. 10Haven’t you read this passage of Scripture:

‘ “The stone the builders rejected

has become the cornerstone;

11the Lord has done this,

and it is marvellous in our eyes”12:11 Psalm 118:22,23?’

12Then the chief priests, the teachers of the law and the elders looked for a way to arrest him because they knew he had spoken the parable against them. But they were afraid of the crowd; so they left him and went away.

Paying the poll-tax to Caesar

13Later they sent some of the Pharisees and Herodians to Jesus to catch him in his words. 14They came to him and said, ‘Teacher, we know that you are a man of integrity. You aren’t swayed by others, because you pay no attention to who they are; but you teach the way of God in accordance with the truth. Is it right to pay the poll-tax12:14 A special tax levied on subject peoples, not on Roman citizens to Caesar or not? 15Should we pay or shouldn’t we?’

But Jesus knew their hypocrisy. ‘Why are you trying to trap me?’ he asked. ‘Bring me a denarius and let me look at it.’ 16They brought the coin, and he asked them, ‘Whose image is this? And whose inscription?’

‘Caesar’s,’ they replied.

17Then Jesus said to them, ‘Give back to Caesar what is Caesar’s and to God what is God’s.’

And they were amazed at him.

Marriage at the resurrection

18Then the Sadducees, who say there is no resurrection, came to him with a question. 19‘Teacher,’ they said, ‘Moses wrote for us that if a man’s brother dies and leaves a wife but no children, the man must marry the widow and raise up offspring for his brother. 20Now there were seven brothers. The first one married and died without leaving any children. 21The second one married the widow, but he also died, leaving no child. It was the same with the third. 22In fact, none of the seven left any children. Last of all, the woman died too. 23At the resurrection12:23 Some manuscripts resurrection, when people rise from the dead, whose wife will she be, since the seven were married to her?’

24Jesus replied, ‘Are you not in error because you do not know the Scriptures or the power of God? 25When the dead rise, they will neither marry nor be given in marriage; they will be like the angels in heaven. 26Now about the dead rising – have you not read in the Book of Moses, in the account of the burning bush, how God said to him, “I am the God of Abraham, the God of Isaac, and the God of Jacob”12:26 Exodus 3:6? 27He is not the God of the dead, but of the living. You are badly mistaken!’

The greatest commandment

28One of the teachers of the law came and heard them debating. Noticing that Jesus had given them a good answer, he asked him, ‘Of all the commandments, which is the most important?’

29‘The most important one,’ answered Jesus, ‘is this: “Hear, O Israel: the Lord our God, the Lord is one.12:29 Or the Lord our God is one Lord 30Love the Lord your God with all your heart and with all your soul and with all your mind and with all your strength.”12:30 Deut. 6:4,5 31The second is this: “Love your neighbour as yourself.”12:31 Lev. 19:18 There is no commandment greater than these.’

32‘Well said, teacher,’ the man replied. ‘You are right in saying that God is one and there is no other but him. 33To love him with all your heart, with all your understanding and with all your strength, and to love your neighbour as yourself is more important than all burnt offerings and sacrifices.’

34When Jesus saw that he had answered wisely, he said to him, ‘You are not far from the kingdom of God.’ And from then on no-one dared ask him any more questions.

Whose son is the Messiah?

35While Jesus was teaching in the temple courts, he asked, ‘Why do the teachers of the law say that the Messiah is the son of David? 36David himself, speaking by the Holy Spirit, declared:

‘ “The Lord said to my Lord:

‘Sit at my right hand

until I put your enemies

under your feet.’ ”12:36 Psalm 110:1

37David himself calls him “Lord”. How then can he be his son?’

The large crowd listened to him with delight.

Warning against the teachers of the law

38As he taught, Jesus said, ‘Watch out for the teachers of the law. They like to walk around in flowing robes and be greeted with respect in the market-places, 39and have the most important seats in the synagogues and the places of honour at banquets. 40They devour widows’ houses and for a show make lengthy prayers. These men will be punished most severely.’

The widow’s offering

41Jesus sat down opposite the place where the offerings were put and watched the crowd putting their money into the temple treasury. Many rich people threw in large amounts. 42But a poor widow came and put in two very small copper coins, worth only a few pence.

43Calling his disciples to him, Jesus said, ‘Truly I tell you, this poor widow has put more into the treasury than all the others. 44They all gave out of their wealth; but she, out of her poverty, put in everything – all she had to live on.’

Hausa Contemporary Bible

Markus 12:1-44

Misalin ’yan haya

(Mattiyu 21.33-46; Luka 20.9-19)

1Sa’an nan ya fara yi musu magana da misalai ya ce, “Wani mutum ya shuka gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa rami domin matsin inabin, ya kuma gina ɗakin gadi. Sai ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, sa’an nan ya yi tafiya. 2Da lokacin girbi ya yi, sai ya aiki wani bawa wajen ’yan hayan, don yă karɓo masa ’ya’yan inabin daga wurinsu. 3Amma suka kama shi, suka yi masa dūka, suka kore shi hannun wofi. 4Sai ya sāke aikan wani bawa wurinsu, amma suka bugi wannan mutum a kai, suka wulaƙanta shi. 5Har yanzu ya sāke aikan wani. Wannan kuwa suka kashe. Ya aika waɗansu da yawa; suka bubbuge waɗansu, sauran kuwa suka kashe.

6“Sauran mutum ɗaya da ya rage ya aika, ɗa, da yake ƙauna. Daga ƙarshe sai ya aike shi, yana cewa, ‘Za su girmama ɗana.’

7“Amma ’yan hayan suka ce wa juna, ‘Aha! Wannan shi ne magājin. Ku zo mu kashe shi, gādon kuma yă zama namu.’ 8Sai suka kama shi suka kashe, suka jefa shi bayan gonar inabin.

9“To, me, mai gonar inabin zai yi ke nan? Zai zo yă karkashe dukan ’yan hayan nan, ya kuma ba wa waɗansu gonar inabin. 10Ba ku taɓa karanta wannan Nassi ba,

“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,

shi ne kuwa ya zama dutsen kusurwan gini.

11Ubangiji ya yi wannan,

ya kuma yi kyau a idanunmu’?”12.11 Zab 118.22,23

12Sai manyan Firistoci da malaman dokoki da shugabanni suka nemi hanyar da za su kama shi, domin sun gane ya yi misalin a kansu ne. Amma suka ji tsoron taron, saboda haka suka bar shi suka yi tafiyarsu.

Biyan haraji ga Kaisar

(Mattiyu 22.15-22; Luka 20.20-26)

13Daga baya, sai suka tura waɗansu Farisiyawa da mutanen Hiridus zuwa wurin Yesu, domin su sa masa tarko a cikin maganarsa. 14Suka zo wurinsa suka ce, “Malam, mun san kai mutum ne mai mutunci. Ba ka bin ra’ayin mutane, don ba ka nuna bambanci. Amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. Daidai ne a biya wa Kaisar haraji, ko babu? 15Mu biya ko kada mu biya?”

Amma Yesu ya san munafuncinsu, sai ya yi tambaya ya ce, “Don me kuke ƙoƙarin sa mini tarko? Ku kawo mini dinari in ga.” 16Suka kawo masa kuɗin, sai ya tambaye, su ya ce, “Hoton wane ne wannan? Kuma rubutun wane ne wannan?”

Suka ce, “Na Kaisar.”

17Sai Yesu ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku ba wa Allah kuma abin da yake na Allah.”

Suka yi mamakinsa ƙwarai.

Aure a tashin matattu

(Mattiyu 22.23-33; Luka 20.27-40)

18Sa’an nan Sadukiyawa da suke cewa, babu tashin matattu, suka zo masa da tambaya. 19Suka ce, “Malam, Musa ya rubuta mana cewa, in ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata babu ’ya’ya, dole mutumin ya auri gwauruwar, yă kuma samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya. 20To, an yi waɗansu ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu babu ’ya’ya. 21Na biyun ya auri gwauruwar, sai shi ma ya mutu, babu ’ya’ya. Haka kuma na ukun. 22A gaskiya, ba ko ɗaya daga cikin bakwai ɗin da ya bar ’ya’ya. Daga ƙarshe, macen ta mutu. 23To, a tashin matattu, matar wa za tă zama, don duk su bakwai nan sun aure ta?”

24Yesu ya ce, “Ashe, ba a cikin kuskure kuke ba saboda rashin sanin Nassi, ko ikon Allah? 25Sa’ad da matattu suka tashi, ba za su yi aure ba, ba kuwa za a ba da su ga aure ba. Za su zama kamar yadda mala’iku suke a cikin sama. 26Game da tashin matattu kuwa, ashe, ba ku karanta a cikin littafin Musa ba, game da labarin ɗan kurmin nan mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, yadda Allah ya yi magana da shi ya ce, ‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’?12.26 Fit 3.6 27Shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne. Kun yi mummunan kuskure!”

Dokar da ta fi girma duka

(Mattiyu 22.23-33; Luka 20.27-40)

28Wani daga cikin malaman dokoki ya zo ya ji suna muhawwara. Da ya lura cewa Yesu ya amsa musu daidai, sai ya tambaye shi ya ce, “A cikin dukan dokoki, wacce ta fi girma duka?”

29Yesu ya ce, “Wadda ta fi girma duka, ita ce wannan. ‘Ku saurara, ya Isra’ila, Ubangiji Allahnmu, Ubangiji ɗaya ne. 30Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan hankalinka, da kuma dukan ƙarfinka.’12.30 M Sh 6.4,5 31Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’12.31 Fir 19.18 Ba wata doka da ta fi waɗannan.”

32Mutumin ya ce, “Malam, ka faɗi daidai. Daidai ne da ka ce, Allah ɗaya ne, babu kuma wani sai shi. 33Nuna ƙauna ga Allah da dukan zuciyarka, da dukan ganewarka, da dukan ƙarfinka, da kuma nuna ƙauna ga maƙwabcinka kamar kanka, ya fi dukan hadayun ƙonawa da sadakoki.”

34Da Yesu ya ga ya amsa da hikima, sai ya ce masa, “Ba ka da nisa da mulkin Allah.” Daga lokacin, ba wanda ya yi karambani yin masa wata tambaya.

Kiristi ɗan wane ne?

(Mattiyu 22.41-46; Luka 20.41-44)

35Yayinda Yesu yake koyarwa a filin haikalin, sai ya yi tambaya ya ce, “Yaya malaman dokoki suke cewa Kiristi ɗan Dawuda ne? 36Dawuda da kansa ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki ya ce,

“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,

“Zauna a hannun damana

sai na sa abokan gābanka

a ƙarƙashin sawunka.” ’12.36 Zab 110.1

37Dawuda da kansa ya kira shi ‘Ubangiji.’ To, ta yaya zai zama ɗansa?”

Taro mai yawa suka saurare shi da murna.

(Mattiyu 23.1-36; Luka 20.45-47)

38Sa’ad da Yesu yake koyarwa ya ce, “Ku lura da malaman dokoki. Sukan so yin tafiya a manyan riguna, a kuma dinga gaishe su a wuraren kasuwanci. 39Sukan kuma nemi wuraren zama mafi daraja a majami’u, da kuma wuraren zaman manya a bukukkuwa. 40Suna ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sukan yi dogayen addu’o’i. Irin mutanen nan, za su sha hukunci mai tsanani sosai.”

Bayarwar gwauruwa

41Yesu ya zauna ɗaura da inda ake bayarwa, ya kuma dubi yadda taron suke sa kuɗinsu a cikin ɗakunan ajiya haikali. Masu arziki da yawa suka zuba kuɗaɗe masu yawa. 42Amma wata matalauciya gwauruwa, ta zo ta saka anini biyu, da suka yi daidai da rabin kobo.

43Yesu ya kira almajiransa wurinsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, abin da matalauciya gwauruwan nan ta zuba cikin ɗakunan ajiya nan ya fi na sauran dukan. 44Dukansu sun bayar ne daga cikin arzikinsu; ita kuwa, daga cikin talaucinta, ta ba da kome, duk abin da take da shi na rayuwa.”