Matthew 12 – NIV & HCB

New International Version

Matthew 12:1-50

Jesus Is Lord of the Sabbath

1At that time Jesus went through the grainfields on the Sabbath. His disciples were hungry and began to pick some heads of grain and eat them. 2When the Pharisees saw this, they said to him, “Look! Your disciples are doing what is unlawful on the Sabbath.”

3He answered, “Haven’t you read what David did when he and his companions were hungry? 4He entered the house of God, and he and his companions ate the consecrated bread—which was not lawful for them to do, but only for the priests. 5Or haven’t you read in the Law that the priests on Sabbath duty in the temple desecrate the Sabbath and yet are innocent? 6I tell you that something greater than the temple is here. 7If you had known what these words mean, ‘I desire mercy, not sacrifice,’12:7 Hosea 6:6 you would not have condemned the innocent. 8For the Son of Man is Lord of the Sabbath.”

9Going on from that place, he went into their synagogue, 10and a man with a shriveled hand was there. Looking for a reason to bring charges against Jesus, they asked him, “Is it lawful to heal on the Sabbath?”

11He said to them, “If any of you has a sheep and it falls into a pit on the Sabbath, will you not take hold of it and lift it out? 12How much more valuable is a person than a sheep! Therefore it is lawful to do good on the Sabbath.”

13Then he said to the man, “Stretch out your hand.” So he stretched it out and it was completely restored, just as sound as the other. 14But the Pharisees went out and plotted how they might kill Jesus.

God’s Chosen Servant

15Aware of this, Jesus withdrew from that place. A large crowd followed him, and he healed all who were ill. 16He warned them not to tell others about him. 17This was to fulfill what was spoken through the prophet Isaiah:

18“Here is my servant whom I have chosen,

the one I love, in whom I delight;

I will put my Spirit on him,

and he will proclaim justice to the nations.

19He will not quarrel or cry out;

no one will hear his voice in the streets.

20A bruised reed he will not break,

and a smoldering wick he will not snuff out,

till he has brought justice through to victory.

21In his name the nations will put their hope.”12:21 Isaiah 42:1-4

Jesus and Beelzebul

22Then they brought him a demon-possessed man who was blind and mute, and Jesus healed him, so that he could both talk and see. 23All the people were astonished and said, “Could this be the Son of David?”

24But when the Pharisees heard this, they said, “It is only by Beelzebul, the prince of demons, that this fellow drives out demons.”

25Jesus knew their thoughts and said to them, “Every kingdom divided against itself will be ruined, and every city or household divided against itself will not stand. 26If Satan drives out Satan, he is divided against himself. How then can his kingdom stand? 27And if I drive out demons by Beelzebul, by whom do your people drive them out? So then, they will be your judges. 28But if it is by the Spirit of God that I drive out demons, then the kingdom of God has come upon you.

29“Or again, how can anyone enter a strong man’s house and carry off his possessions unless he first ties up the strong man? Then he can plunder his house.

30“Whoever is not with me is against me, and whoever does not gather with me scatters. 31And so I tell you, every kind of sin and slander can be forgiven, but blasphemy against the Spirit will not be forgiven. 32Anyone who speaks a word against the Son of Man will be forgiven, but anyone who speaks against the Holy Spirit will not be forgiven, either in this age or in the age to come.

33“Make a tree good and its fruit will be good, or make a tree bad and its fruit will be bad, for a tree is recognized by its fruit. 34You brood of vipers, how can you who are evil say anything good? For the mouth speaks what the heart is full of. 35A good man brings good things out of the good stored up in him, and an evil man brings evil things out of the evil stored up in him. 36But I tell you that everyone will have to give account on the day of judgment for every empty word they have spoken. 37For by your words you will be acquitted, and by your words you will be condemned.”

The Sign of Jonah

38Then some of the Pharisees and teachers of the law said to him, “Teacher, we want to see a sign from you.”

39He answered, “A wicked and adulterous generation asks for a sign! But none will be given it except the sign of the prophet Jonah. 40For as Jonah was three days and three nights in the belly of a huge fish, so the Son of Man will be three days and three nights in the heart of the earth. 41The men of Nineveh will stand up at the judgment with this generation and condemn it; for they repented at the preaching of Jonah, and now something greater than Jonah is here. 42The Queen of the South will rise at the judgment with this generation and condemn it; for she came from the ends of the earth to listen to Solomon’s wisdom, and now something greater than Solomon is here.

43“When an impure spirit comes out of a person, it goes through arid places seeking rest and does not find it. 44Then it says, ‘I will return to the house I left.’ When it arrives, it finds the house unoccupied, swept clean and put in order. 45Then it goes and takes with it seven other spirits more wicked than itself, and they go in and live there. And the final condition of that person is worse than the first. That is how it will be with this wicked generation.”

Jesus’ Mother and Brothers

46While Jesus was still talking to the crowd, his mother and brothers stood outside, wanting to speak to him. 47Someone told him, “Your mother and brothers are standing outside, wanting to speak to you.”

48He replied to him, “Who is my mother, and who are my brothers?” 49Pointing to his disciples, he said, “Here are my mother and my brothers. 50For whoever does the will of my Father in heaven is my brother and sister and mother.”

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 12:1-50

Ubangijin Asabbaci

(Markus 2.23-28; Luka 6.1-5)

1A lokacin nan Yesu ya bi ta gonakin hatsi a ranar Asabbaci. Almajiransa kuwa suna jin yunwa, sai suka fara kakkarya kan hatsi suna ci. 2Sa’ad da Farisiyawa suka ga wannan, sai suka ce masa, “Duba! Almajiranka suna yin abin da doka ta hana a yi a ranar Asabbaci.”

3Sai ya amsa ya ce, “Ba ku karanta abin da Dawuda ya yi ba ne sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa? 4Ya shiga gidan Allah, da shi da abokan tafiyarsa suka ci keɓaɓɓen burodin, wanda doka ta hana su yi, sai firistoci kaɗai. 5Ko kuwa ba ku karanta a Doka cewa a ranar Asabbaci firistoci sukan karya dokar Asabbaci duk da haka ba da yin wani laifi ba? 6Ina faɗa muku cewa wani12.6 Ko kuwa a wani abu; haka ma a ayoyi 41 da 42 wanda ya fi haikali yana a nan. 7Da a ce kun san abin da waɗannan kalmomi suke nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba,’12.7 Hos 6.6 da ba ku zargi marar laifi ba. 8Gama Ɗan Mutum shi ne Ubangijin Asabbaci.”

(Markus 3.1-6; Luka 6.6-11)

9Da ya ci gaba daga wurin, sai ya shiga majami’arsu, 10a nan kuwa akwai wani mutum mai shanyayyen hannu. Don neman dalili su zargi Yesu, sai suka tambaye shi suka ce, “Ya dace a warkar a ranar Asabbaci?”

11Ya ce musu, “In waninku yana da tunkiya, ta kuma fāɗa a rami ran Asabbaci, ba zai cire ta daga ramin ba? 12Sau nawa mutum ya fi tunkiya daraja! Saboda haka ya dace a aikata alheri ran Asabbaci.”

13Sa’an nan ya ce wa mutumin, “Miƙa hannunka.” Sai ya miƙa, hannunsa kuwa ya koma lafiyayye, kamar dai ɗayan. 14Amma Farisiyawa suka fita suka ƙulla shawara yadda za su kashe Yesu.

Zaɓaɓɓen bawan Allah

15Da ya gane wannan, sai Yesu ya janye daga wurin. Da yawa suka bi shi, ya kuwa warkar da dukan masu ciwonsu, 16yana jan musu kunne kada su faɗa wa kowa akan ko shi wane ne. 17Wannan kuwa domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya ne cewa,

18“Ga bawana da na zaɓa,

ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi;

zan sa Ruhuna a kansa,

zai kuma yi shelar adalci ga al’ummai.

19Ba zai yi faɗa ko yă ɗaga murya ba,

ba kuwa wanda zai ji muryarsa a kan tituna.

20Kyauron da ya tanƙwasa ba zai karye shi ba.

Fitilar da ta yi kusan mutuwa ba zai kashe ta ba,

sai ya jagoranci adalci zuwa ga nasara.

21Cikin sunansa al’ummai za su dogara.”12.21 Ish 42.1-4

Yesu da Be’elzebub

(Markus 3.20-30; Luka 11.14-23; 12.10)

22Sai aka kawo masa wani bebe kuma makaho mai aljani, Yesu kuwa ya warkar da shi, har ya iya magana ya kuma sami ganin gari. 23Dukan mutane suka yi mamaki, suka ce, “Wannan Ɗan Dawuda ne kuwa?”

24Amma da Farisiyawa suka ji haka, sai suka ce, “Ahab, da Be’elzebub12.24 Da Girik Be’elzebul Ko kuwa Be’elzebul; haka ma a aya 27 sarkin aljanu ne kaɗai, wannan mutum yake fitar da aljanu.”

25Yesu kuwa ya san tunaninsu sai ya ce musu, “Duk mulkin da yake gāba da kansa zai lalace, kuma duk birni ko gidan da yake rabe gāba da kansa ba zai ɗore ba. 26In Shaiɗan yana fitar da Shaiɗan, ai, ya rabu yana gāba da kansa ke nan. Yaya kuwa mulkinsa zai ɗore? 27In kuwa ta wurin Be’elzebub nake fitar da aljanu, to, ta wa mutanenku suke fitar da su? Saboda haka, su ne za su zama alƙalanku. 28Amma in ina fitar da aljanu ta wurin Ruhun Allah ne, to, fa, mulkin Allah ya zo muku ke nan.

29“Ko kuwa, yaya wani zai iya shiga gidan mai ƙarfi yă ƙwace masa kaya ba tare da ya fara daure mai ƙarfin nan tukuna ba? Sa’an nan zai iya washe gidansa.

30“Wanda ba ya tare da ni, yana gāba da ni ne, kuma wanda ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi. 31Saboda haka ina gaya muku, za a gafarta wa mutane kowane zunubi da kuma saɓo, amma saɓo game da Ruhu, ba za a gafarta ba. 32Duk wanda ya zargi Ɗan Mutum, za a gafarta masa, amma duk wanda ya zargi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba, ko a wannan zamani ko a zamani mai zuwa.

(Luka 6.43-45)

33“Itace mai kyau, yakan ba da ’ya’ya masu kyau. Itace marar kyau kuma, yakan ba da ’ya’ya marasa kyau. Itace dai, da irin ’ya’yansa ne ake gane shi. 34Ku macizai, ta yaya ku da kuke mugaye za ku iya magana kirki? Gama daga baki, mutum yakan faɗi abin da yake cikin zuciya. 35Mutumin kirki yakan fito da abubuwa masu kyau daga ajiyar da aka a yi cikinsa, mugun mutum kuwa yakan fito da mugayen abubuwa daga cikin muguntar da aka yi ajiya a cikinsa. 36Amma ina gaya muku cewa mutane za su ba da lissafi a ranar shari’a a kan kowace kalmar banza da suka faɗa. 37Gama ta wurin kalmominka za a kuɓutar da kai, kuma ta wurin kalmominka za a hukunta ka.”

Alamar Yunana

(Markus 8.11,12; Luka 11.29-32)

38Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, “Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka.”

39Sai ya amsa ya ce, “Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana. 40Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa. 41Mutanen Ninebe za su tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, su kuwa hukunta shi; don sun tuba saboda wa’azin Yunana, yanzu kuwa ga wanda ya fi Yunana girma a nan. 42Sarauniyar Sheba za tă tashi a ranar shari’a tare da wannan zamani, tă kuwa hukunta shi; don ta zo daga ƙarshen duniya, ta saurari hikimar Solomon, yanzu kuwa ga wanda ya fi Solomon girma a nan.

(Luka 11.24-26)

43“Sa’ad da mugun ruhu ya fita daga mutum, yakan bi wuraren da ba ruwa yana neman hutu, ba ya kuwa samu. 44Sa’an nan yakan ce, ‘Zan koma gidan da na bari.’ Sa’ad da ya iso, ya tarar da gidan ba kowa a ciki, shararre, kuma a kintse. 45Sai yă je yă ɗebo waɗansu ruhohi bakwai da suka fi shi mugunta, su kuwa zo su shiga su zauna a can. Ƙarshen mutumin nan fa zai fi farkonsa muni. Haka zai zama ga wannan mugun zamani.”

Mahaifiyar Yesu da ’yan’uwansa

(Markus 3.31-35; Luka 8.19-21)

46Yayinda Yesu yake cikin magana da taron, sai ga mahaifiyarsa da ’yan’uwansa tsaye a waje, suna so su yi magana da shi. 47Wani ya ce masa, “Mahaifiyarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje, suna so su yi magana da kai.”12.47 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da aya 47.

48Ya amsa masa ya ce, “Wace ce mahaifiyata, su wane ne kuma ’yan’uwana?” 49Sai ya miƙa hannu wajen almajiransa ya ce, “Ga mahaifiyata da kuma ’yan’uwana. 50Ai, duk wanda yake aikata nufin Ubana wanda yake cikin sama, shi ne ɗan’uwana da ’yar’uwata da kuma mahaifiyata.”