Mark 2 – NIV & HCB

New International Version

Mark 2:1-28

Jesus Forgives and Heals a Paralyzed Man

1A few days later, when Jesus again entered Capernaum, the people heard that he had come home. 2They gathered in such large numbers that there was no room left, not even outside the door, and he preached the word to them. 3Some men came, bringing to him a paralyzed man, carried by four of them. 4Since they could not get him to Jesus because of the crowd, they made an opening in the roof above Jesus by digging through it and then lowered the mat the man was lying on. 5When Jesus saw their faith, he said to the paralyzed man, “Son, your sins are forgiven.”

6Now some teachers of the law were sitting there, thinking to themselves, 7“Why does this fellow talk like that? He’s blaspheming! Who can forgive sins but God alone?”

8Immediately Jesus knew in his spirit that this was what they were thinking in their hearts, and he said to them, “Why are you thinking these things? 9Which is easier: to say to this paralyzed man, ‘Your sins are forgiven,’ or to say, ‘Get up, take your mat and walk’? 10But I want you to know that the Son of Man has authority on earth to forgive sins.” So he said to the man, 11“I tell you, get up, take your mat and go home.” 12He got up, took his mat and walked out in full view of them all. This amazed everyone and they praised God, saying, “We have never seen anything like this!”

Jesus Calls Levi and Eats With Sinners

13Once again Jesus went out beside the lake. A large crowd came to him, and he began to teach them. 14As he walked along, he saw Levi son of Alphaeus sitting at the tax collector’s booth. “Follow me,” Jesus told him, and Levi got up and followed him.

15While Jesus was having dinner at Levi’s house, many tax collectors and sinners were eating with him and his disciples, for there were many who followed him. 16When the teachers of the law who were Pharisees saw him eating with the sinners and tax collectors, they asked his disciples: “Why does he eat with tax collectors and sinners?”

17On hearing this, Jesus said to them, “It is not the healthy who need a doctor, but the sick. I have not come to call the righteous, but sinners.”

Jesus Questioned About Fasting

18Now John’s disciples and the Pharisees were fasting. Some people came and asked Jesus, “How is it that John’s disciples and the disciples of the Pharisees are fasting, but yours are not?”

19Jesus answered, “How can the guests of the bridegroom fast while he is with them? They cannot, so long as they have him with them. 20But the time will come when the bridegroom will be taken from them, and on that day they will fast.

21“No one sews a patch of unshrunk cloth on an old garment. Otherwise, the new piece will pull away from the old, making the tear worse. 22And no one pours new wine into old wineskins. Otherwise, the wine will burst the skins, and both the wine and the wineskins will be ruined. No, they pour new wine into new wineskins.”

Jesus Is Lord of the Sabbath

23One Sabbath Jesus was going through the grainfields, and as his disciples walked along, they began to pick some heads of grain. 24The Pharisees said to him, “Look, why are they doing what is unlawful on the Sabbath?”

25He answered, “Have you never read what David did when he and his companions were hungry and in need? 26In the days of Abiathar the high priest, he entered the house of God and ate the consecrated bread, which is lawful only for priests to eat. And he also gave some to his companions.”

27Then he said to them, “The Sabbath was made for man, not man for the Sabbath. 28So the Son of Man is Lord even of the Sabbath.”

Hausa Contemporary Bible

Markus 2:1-28

Yesu ya warkar da shanyayye

(Mattiyu 9.1-8; Luka 5.17-26)

1Bayan ’yan kwanaki, da Yesu ya sāke shiga Kafarnahum, sai mutane suka ji labarin zuwansa gida. 2Mutane suka taru da yawa har ma babu wuri, ko a bakin ƙofa ma, sai ya yi musu wa’azin bishara. 3Waɗansu mutum huɗu suka zo wajensa ɗauke da wani shanyayye. 4Da ba su iya kai shi wurin Yesu ba, saboda taron, sai suka buɗe rufin gidan saman, bisa daidai inda Yesu yake. Bayan da suka huda rami, sai suka saukar da shanyayyen, kwance a kan tabarmarsa. 5Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Saurayi, an gafarta zunubanka.”

6To, waɗansu malaman dokoki da suke zaune a wurin, suka yi tunani a zuciyarsu, suna cewa, 7“Me ya sa mutumin nan yake magana haka? Yana saɓo! Wane ne zai iya gafarta zunubai, in ba Allah kaɗai ba?”

8Nan da nan, Yesu ya gane a ruhunsa abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya ce musu, “Me ya sa kuke tunanin waɗannan abubuwa? 9Wanne ya fi sauƙi, a ce wa shanyayyen, ‘An gafarta zunubanka,’ ko a ce, ‘Tashi, ɗauki tabarmarka ka yi tafiya’? 10Amma don ku san cewa, Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, 11“Ina ce maka, tashi, ɗauki tabarmarka, ka tafi gida.” 12Sai ya tashi, ya ɗauki tabarmarsa, ya yi tafiyarsa a gabansu duka. Wannan ya ba wa kowa mamaki, suka kuma ɗaukaka Allah suna cewa, “Ba mu taɓa ganin abu haka ba!”

Kiran Lawi

(Mattiyu 9.9-13; Luka 5.27-32)

13Yesu ya sāke tafiya bakin tafkin. Taro mai yawa ya zo wurinsa, sai ya fara koya musu. 14Yana cikin tafiya, sai ya ga Lawi, ɗan Alfayus zaune a inda ake karɓar haraji. Yesu ya ce masa, “Bi ni.” Sai Lawi ya tashi, ya bi shi.

15Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Lawi, sai masu karɓar haraji da “masu zunubi” da yawa, suka zo suka ci tare da shi da almajiransa, gama akwai mutane da yawa da suka bi shi. 16Da malaman dokoki, waɗanda su ma Farisiyawa ne, suka ga yana ci tare da masu “zunubi” da masu karɓar haraji, sai suka tambayi almajiransa, suka ce, “Me ya sa yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

17Da jin wannan, Yesu ya ce musu, “Ai, masu lafiya ba sa bukatar likita, sai dai marasa lafiya. Ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”

An tuhumi Yesu game da azumi

(Mattiyu 9.14-17; Luka 5.33-39)

18To, almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, sai waɗansu mutane suka zo suka tambayi Yesu, suka ce, “Yaya almajiran Yohanna da na Farisiyawa suna azumi, amma almajiranka ba sa yi?”

19Yesu ya amsa ya ce, “Yaya abokan ango za su yi azumi, sa’ad da yana tare da su? Ai, ba za su yi ba, muddin yana tare da su. 20Ai, lokaci yana zuwa da za a ɗauke musu angon. A sa’an nan ne fa za su yi azumi.

21“Ba mai facin sabon ƙyalle a tsohuwar riga. In ya yi haka, sabon ƙyallen zai yage daga tsohuwar, yagewar kuwa za tă zama da muni. 22Ba wanda yakan zuba sabon ruwan inabi a tsofaffin salkuna. In ya yi haka, ruwan inabin zai farfashe salkunan, yă yi hasarar ruwan inabin, salkunan kuma su lalace. A’a, yakan zuba sabon ruwan inabin a sababbin salkuna.”

Ubangijin Asabbaci

(Mattiyu 12.1-8; Luka 6.1-5)

23Wata ranar Asabbaci, Yesu yana ratsa gonakin hatsi, sai almajiransa da suke tafiya tare da shi, suka fara kakkarya waɗansu kan hatsi. 24Farisiyawa suka ce masa, “Duba, me ya sa suke yin abin da doka ta hana a yi, a ranar Asabbaci?”

25Ya amsa ya ce, “Ashe, ba ku taɓa karanta abin da Dawuda ya yi ba, sa’ad da shi da abokan tafiyarsa suka ji yunwa, suna kuma cikin bukata? 26Ya shiga gidan Allah a zamanin Abiyatar babban firist, ya ci keɓaɓɓen burodin nan, ya kuma ba wa abokan tafiyarsa abin da firistoci kaɗai sukan ci bisa ga doka?”

27Sai ya ce musu, “An yi Asabbaci saboda mutum ne, ba mutum saboda Asabbaci ba. 28Don haka, Ɗan Mutum Ubangiji ne, har ma da na Asabbaci.”