Mark 15 – NIV & HCB

New International Version

Mark 15:1-47

Jesus Before Pilate

1Very early in the morning, the chief priests, with the elders, the teachers of the law and the whole Sanhedrin, made their plans. So they bound Jesus, led him away and handed him over to Pilate.

2“Are you the king of the Jews?” asked Pilate.

“You have said so,” Jesus replied.

3The chief priests accused him of many things. 4So again Pilate asked him, “Aren’t you going to answer? See how many things they are accusing you of.”

5But Jesus still made no reply, and Pilate was amazed.

6Now it was the custom at the festival to release a prisoner whom the people requested. 7A man called Barabbas was in prison with the insurrectionists who had committed murder in the uprising. 8The crowd came up and asked Pilate to do for them what he usually did.

9“Do you want me to release to you the king of the Jews?” asked Pilate, 10knowing it was out of self-interest that the chief priests had handed Jesus over to him. 11But the chief priests stirred up the crowd to have Pilate release Barabbas instead.

12“What shall I do, then, with the one you call the king of the Jews?” Pilate asked them.

13“Crucify him!” they shouted.

14“Why? What crime has he committed?” asked Pilate.

But they shouted all the louder, “Crucify him!”

15Wanting to satisfy the crowd, Pilate released Barabbas to them. He had Jesus flogged, and handed him over to be crucified.

The Soldiers Mock Jesus

16The soldiers led Jesus away into the palace (that is, the Praetorium) and called together the whole company of soldiers. 17They put a purple robe on him, then twisted together a crown of thorns and set it on him. 18And they began to call out to him, “Hail, king of the Jews!” 19Again and again they struck him on the head with a staff and spit on him. Falling on their knees, they paid homage to him. 20And when they had mocked him, they took off the purple robe and put his own clothes on him. Then they led him out to crucify him.

The Crucifixion of Jesus

21A certain man from Cyrene, Simon, the father of Alexander and Rufus, was passing by on his way in from the country, and they forced him to carry the cross. 22They brought Jesus to the place called Golgotha (which means “the place of the skull”). 23Then they offered him wine mixed with myrrh, but he did not take it. 24And they crucified him. Dividing up his clothes, they cast lots to see what each would get.

25It was nine in the morning when they crucified him. 26The written notice of the charge against him read: the king of the jews.

27They crucified two rebels with him, one on his right and one on his left. 2815:28 Some manuscripts include here words similar to Luke 22:37. 29Those who passed by hurled insults at him, shaking their heads and saying, “So! You who are going to destroy the temple and build it in three days, 30come down from the cross and save yourself!” 31In the same way the chief priests and the teachers of the law mocked him among themselves. “He saved others,” they said, “but he can’t save himself! 32Let this Messiah, this king of Israel, come down now from the cross, that we may see and believe.” Those crucified with him also heaped insults on him.

The Death of Jesus

33At noon, darkness came over the whole land until three in the afternoon. 34And at three in the afternoon Jesus cried out in a loud voice, “Eloi, Eloi, lema sabachthani?” (which means “My God, my God, why have you forsaken me?”).15:34 Psalm 22:1

35When some of those standing near heard this, they said, “Listen, he’s calling Elijah.”

36Someone ran, filled a sponge with wine vinegar, put it on a staff, and offered it to Jesus to drink. “Now leave him alone. Let’s see if Elijah comes to take him down,” he said.

37With a loud cry, Jesus breathed his last.

38The curtain of the temple was torn in two from top to bottom. 39And when the centurion, who stood there in front of Jesus, saw how he died,15:39 Some manuscripts saw that he died with such a cry he said, “Surely this man was the Son of God!”

40Some women were watching from a distance. Among them were Mary Magdalene, Mary the mother of James the younger and of Joseph,15:40 Greek Joses, a variant of Joseph; also in verse 47 and Salome. 41In Galilee these women had followed him and cared for his needs. Many other women who had come up with him to Jerusalem were also there.

The Burial of Jesus

42It was Preparation Day (that is, the day before the Sabbath). So as evening approached, 43Joseph of Arimathea, a prominent member of the Council, who was himself waiting for the kingdom of God, went boldly to Pilate and asked for Jesus’ body. 44Pilate was surprised to hear that he was already dead. Summoning the centurion, he asked him if Jesus had already died. 45When he learned from the centurion that it was so, he gave the body to Joseph. 46So Joseph bought some linen cloth, took down the body, wrapped it in the linen, and placed it in a tomb cut out of rock. Then he rolled a stone against the entrance of the tomb. 47Mary Magdalene and Mary the mother of Joseph saw where he was laid.

Hausa Contemporary Bible

Markus 15:1-47

Yesu a gaban Bilatus

(Mattiyu 27.1,2,11-14; Luka 23.1-5; Yohanna 18.28-38)

1Da sassafe, sai manyan firistoci da dattawa, da malaman dokoki, da dukan Majalisa, suka yanke shawara. Suka daure Yesu, suka kai shi, suka miƙa shi ga Bilatus.

2Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kai ne Sarkin Yahudawa?”

Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”

3Manyan firistoci suka zarge shi a kan abubuwa da yawa. 4Don haka Bilatus ya sāke tambayarsa ya ce, “Ba za ka amsa ba? Dubi abubuwa da yawa da suke zarginka da su.”

5Amma har yanzu, Yesu bai ba da amsa ba, Bilatus ya yi mamaki.

(Mattiyu 27.15-26; Luka 23.13-25; Yohanna 18.39–19.16)

6Yanzu fa, al’ada ce a lokacin Bikin, a saki ɗan kurkuku guda wanda mutane suka roƙa. 7Wani mutumin da ake kira Barabbas, yana a kurkuku, tare da waɗansu ’yan tawaye da suka yi kisankai a lokacin wani hargitsi. 8Taron suka matso, suka ce roƙi Bilatus yă yi musu abin da ya saba yi.

9Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Kuna so in sakar muku Sarkin Yahudawa?” 10Don ya san saboda sonkai ne manyan firistoci suka ba da Yesu a gare shi. 11Amma manyan firistoci suka zuga taron su sa a saki Barabbas, a maimakon Yesu.

12Bilatus ya tambaye su ya ce, “To, me zan yi da wanda kuke ce da shi, sarkin Yahudawa?”

13Suka yi ihu, suka ce, “A gicciye shi!”

14Bilatus ya yi tambaya ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”

Amma suka ƙara yin ihu suna cewa, “A gicciye shi!”

15Don son yă faranta wa taron rai, sai Bilatus ya sakar musu Barabbas. Ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

Sojoji sun yi wa Yesu ba’a

(Mattiyu 27.27-30; Yohanna 19.2,3)

16Sojojin suka tafi da Yesu cikin fadar gwamna (wato, Firetoriyum), suka kira dukan kamfanin sojoji wuri ɗaya. 17Suka sa masa wata riga mai ruwan shunayya, suka kuma tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa. 18Sai suka fara ce masa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” 19Suka dinga bugunsa a kā da sanda, suka tattofa masa miyau. Suka durƙusa suka yi masa bangirma na ba’a. 20Bayan da suka gama yin masa ba’a, suka tuɓe rigar mai ruwan shunayyar, suka sa masa nasa tufafi. Sai suka tafi da shi don a gicciye shi.

Gicciyewa

(Mattiyu 27.27-30; Yohanna 19.2,3)

21Sai ga wani mutum daga Sairin da ake kira Siman, mahaifin Alekzanda da Rufus, yana wucewa kan hanyarsa daga ƙauye. Sai suka tilasta shi yă ɗauki gicciyen. 22Suka kawo Yesu a wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). 23Sai suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da mur, don yă rage zafi, amma bai sha ba. 24Sai suka gicciye shi. Suka rarraba tufafinsa, suka jefa ƙuri’a a kansu don su ga abin da kowa zai samu.

25Sa’a ta uku na safe ce kuwa aka gicciye shi. 26Akwai rubutu na zarginsa, da ya ce,

Sarkin Yahudawa.

27Suka gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗayan kuma a hagunsa.15.27 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da hagu, 28 Nassin nan kuwa ya cika da ya ce, “An lasafta shi a cikin masu laifi.” (Ish 53.12) 29Masu wucewa suka zazzage shi. Suka kaɗa kai suna cewa, “To, kai da za ka rushe haikali ka kuma gina shi a kwana uku, 30sai ka sauko daga gicciyen, ka ceci kanka!”

31Haka kuma, manyan firistoci da malaman dokoki suka yi masa ba’a a junansu, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! 32Bari wannan Kiristi, wannan Sarkin Isra’ila, yă sauko yanzu daga gicciye, don mu ga mu kuma gaskata.” Waɗanda aka gicciye tare da shi ma suka zazzage shi.

Mutuwar Yesu

(Mattiyu 27.45-56; Luka 23.44-49; Yohanna 19.28-30)

33Daga sa’a ta shida har zuwa sa’a ta tara na rana, duhu ya rufe dukan ƙasar. 34A daidai sa’a ta tara na rana, sai Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi, lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).15.34 Zab 22.1

35Da waɗansu cikin waɗanda suke tsattsaye kusa da wurin suka ji haka, suka ce, “Ku saurara, yana kiran Iliya.”

36Wani mutum ya ruga ya je ya jiƙo soso da ruwan tsami, ya soka a sanda ya miƙa wa Yesu yă sha. Ya ce, “Ku ƙyale shi. Bari mu ga ko Iliya zai zo yă saukar da shi.”

37Da murya mai ƙarfi, Yesu ya ja numfashinsa na ƙarshe.

38Labulen haikali kuwa ya yage kashi biyu, daga sama har ƙasa. 39Da jarumin da yake tsaye a gaban Yesu ya ji muryarsa, ya kuma ga yadda ya mutu, sai ya ce, “Gaskiya, wannan mutum Ɗan Allah ne!”

40Waɗansu mata suna kallo daga nesa. A cikinsu kuwa akwai Maryamu Magdalin, Maryamu mahaifiyar Yaƙub ƙarami da Yusuf,15.40 Girik Yosi, wani sunan Yusuf; haka ma a aya 47 da kuma Salome. 41A Galili waɗannan mata ne suka riƙa bin sa suna yin masa hidima. Waɗansu mata da yawa da suka zo tare da shi daga Urushalima, su ma suna nan a can.

Jana’izar Yesu

(Mattiyu 27.57-61; Luka 23.50-56; Yohanna 19.38-42)

42Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai 43Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 44Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu. 45Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin. 46Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin. 47Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.