Mark 14 – NIV & HCB

New International Version

Mark 14:1-72

Jesus Anointed at Bethany

1Now the Passover and the Festival of Unleavened Bread were only two days away, and the chief priests and the teachers of the law were scheming to arrest Jesus secretly and kill him. 2“But not during the festival,” they said, “or the people may riot.”

3While he was in Bethany, reclining at the table in the home of Simon the Leper, a woman came with an alabaster jar of very expensive perfume, made of pure nard. She broke the jar and poured the perfume on his head.

4Some of those present were saying indignantly to one another, “Why this waste of perfume? 5It could have been sold for more than a year’s wages14:5 Greek than three hundred denarii and the money given to the poor.” And they rebuked her harshly.

6“Leave her alone,” said Jesus. “Why are you bothering her? She has done a beautiful thing to me. 7The poor you will always have with you,14:7 See Deut. 15:11. and you can help them any time you want. But you will not always have me. 8She did what she could. She poured perfume on my body beforehand to prepare for my burial. 9Truly I tell you, wherever the gospel is preached throughout the world, what she has done will also be told, in memory of her.”

10Then Judas Iscariot, one of the Twelve, went to the chief priests to betray Jesus to them. 11They were delighted to hear this and promised to give him money. So he watched for an opportunity to hand him over.

The Last Supper

12On the first day of the Festival of Unleavened Bread, when it was customary to sacrifice the Passover lamb, Jesus’ disciples asked him, “Where do you want us to go and make preparations for you to eat the Passover?”

13So he sent two of his disciples, telling them, “Go into the city, and a man carrying a jar of water will meet you. Follow him. 14Say to the owner of the house he enters, ‘The Teacher asks: Where is my guest room, where I may eat the Passover with my disciples?’ 15He will show you a large room upstairs, furnished and ready. Make preparations for us there.”

16The disciples left, went into the city and found things just as Jesus had told them. So they prepared the Passover.

17When evening came, Jesus arrived with the Twelve. 18While they were reclining at the table eating, he said, “Truly I tell you, one of you will betray me—one who is eating with me.”

19They were saddened, and one by one they said to him, “Surely you don’t mean me?”

20“It is one of the Twelve,” he replied, “one who dips bread into the bowl with me. 21The Son of Man will go just as it is written about him. But woe to that man who betrays the Son of Man! It would be better for him if he had not been born.”

22While they were eating, Jesus took bread, and when he had given thanks, he broke it and gave it to his disciples, saying, “Take it; this is my body.”

23Then he took a cup, and when he had given thanks, he gave it to them, and they all drank from it.

24“This is my blood of the14:24 Some manuscripts the new covenant, which is poured out for many,” he said to them. 25“Truly I tell you, I will not drink again from the fruit of the vine until that day when I drink it new in the kingdom of God.”

26When they had sung a hymn, they went out to the Mount of Olives.

Jesus Predicts Peter’s Denial

27“You will all fall away,” Jesus told them, “for it is written:

“ ‘I will strike the shepherd,

and the sheep will be scattered.’14:27 Zech. 13:7

28But after I have risen, I will go ahead of you into Galilee.”

29Peter declared, “Even if all fall away, I will not.”

30“Truly I tell you,” Jesus answered, “today—yes, tonight—before the rooster crows twice14:30 Some early manuscripts do not have twice. you yourself will disown me three times.”

31But Peter insisted emphatically, “Even if I have to die with you, I will never disown you.” And all the others said the same.

Gethsemane

32They went to a place called Gethsemane, and Jesus said to his disciples, “Sit here while I pray.” 33He took Peter, James and John along with him, and he began to be deeply distressed and troubled. 34“My soul is overwhelmed with sorrow to the point of death,” he said to them. “Stay here and keep watch.”

35Going a little farther, he fell to the ground and prayed that if possible the hour might pass from him. 36“Abba, 14:36 Aramaic for father Father,” he said, “everything is possible for you. Take this cup from me. Yet not what I will, but what you will.”

37Then he returned to his disciples and found them sleeping. “Simon,” he said to Peter, “are you asleep? Couldn’t you keep watch for one hour? 38Watch and pray so that you will not fall into temptation. The spirit is willing, but the flesh is weak.”

39Once more he went away and prayed the same thing. 40When he came back, he again found them sleeping, because their eyes were heavy. They did not know what to say to him.

41Returning the third time, he said to them, “Are you still sleeping and resting? Enough! The hour has come. Look, the Son of Man is delivered into the hands of sinners. 42Rise! Let us go! Here comes my betrayer!”

Jesus Arrested

43Just as he was speaking, Judas, one of the Twelve, appeared. With him was a crowd armed with swords and clubs, sent from the chief priests, the teachers of the law, and the elders.

44Now the betrayer had arranged a signal with them: “The one I kiss is the man; arrest him and lead him away under guard.” 45Going at once to Jesus, Judas said, “Rabbi!” and kissed him. 46The men seized Jesus and arrested him. 47Then one of those standing near drew his sword and struck the servant of the high priest, cutting off his ear.

48“Am I leading a rebellion,” said Jesus, “that you have come out with swords and clubs to capture me? 49Every day I was with you, teaching in the temple courts, and you did not arrest me. But the Scriptures must be fulfilled.” 50Then everyone deserted him and fled.

51A young man, wearing nothing but a linen garment, was following Jesus. When they seized him, 52he fled naked, leaving his garment behind.

Jesus Before the Sanhedrin

53They took Jesus to the high priest, and all the chief priests, the elders and the teachers of the law came together. 54Peter followed him at a distance, right into the courtyard of the high priest. There he sat with the guards and warmed himself at the fire.

55The chief priests and the whole Sanhedrin were looking for evidence against Jesus so that they could put him to death, but they did not find any. 56Many testified falsely against him, but their statements did not agree.

57Then some stood up and gave this false testimony against him: 58“We heard him say, ‘I will destroy this temple made with human hands and in three days will build another, not made with hands.’ ” 59Yet even then their testimony did not agree.

60Then the high priest stood up before them and asked Jesus, “Are you not going to answer? What is this testimony that these men are bringing against you?” 61But Jesus remained silent and gave no answer.

Again the high priest asked him, “Are you the Messiah, the Son of the Blessed One?”

62“I am,” said Jesus. “And you will see the Son of Man sitting at the right hand of the Mighty One and coming on the clouds of heaven.”

63The high priest tore his clothes. “Why do we need any more witnesses?” he asked. 64“You have heard the blasphemy. What do you think?”

They all condemned him as worthy of death. 65Then some began to spit at him; they blindfolded him, struck him with their fists, and said, “Prophesy!” And the guards took him and beat him.

Peter Disowns Jesus

66While Peter was below in the courtyard, one of the servant girls of the high priest came by. 67When she saw Peter warming himself, she looked closely at him.

“You also were with that Nazarene, Jesus,” she said.

68But he denied it. “I don’t know or understand what you’re talking about,” he said, and went out into the entryway.14:68 Some early manuscripts entryway and the rooster crowed

69When the servant girl saw him there, she said again to those standing around, “This fellow is one of them.” 70Again he denied it.

After a little while, those standing near said to Peter, “Surely you are one of them, for you are a Galilean.”

71He began to call down curses, and he swore to them, “I don’t know this man you’re talking about.”

72Immediately the rooster crowed the second time.14:72 Some early manuscripts do not have the second time. Then Peter remembered the word Jesus had spoken to him: “Before the rooster crows twice14:72 Some early manuscripts do not have twice. you will disown me three times.” And he broke down and wept.

Hausa Contemporary Bible

Markus 14:1-72

An shafe Yesu a Betani

(Mattiyu 26.1-5; Luka 22.1,2; Yohanna 11.45-53)

1To, saura kwana biyu ne kaɗai a yi Bikin Ƙetarewa da Bikin Burodi Marar Yisti, sai manyan firistoci da malaman dokoki, suka nemi wani dalili su kama Yesu a ɓoye, su kashe. 2Suka ce, “Ba a lokacin Biki ba, don kada mutane su yi tawaye.”

(Mattiyu 26.6-13; Yohanna 12.1-8)

3Yayinda yake a Betani, a gidan wani mutumin da ake kira Siman Kuturu, yana cin abinci, sai wata mace ta zo da wani ɗan tulu na turaren alabasta da aka yi da nardi zalla, mai tsadan gaske. Ta fasa tulun, ta kuma zuba turaren a kansa.

4Waɗansu daga cikin waɗanda suke wurin, suka ji haushi, suka ce wa juna, “Me ya sa za a ɓata turaren nan haka? 5Da an sayar da shi, ai, da an sami kuɗi fiye da albashi14.5 Girik fiye da dinari ɗari uku ma’aikaci na shekara guda, a ba wa matalauta. Sai suka tsawata mata da zafi.”

6Yesu ya ce, “Ku ƙyale ta mana. Don me kuke damunta? Ta yi abu mai kyau a gare ni. 7Matalauta dai suna tare da ku kullum, za ku kuma iya taimakonsu a duk lokacin da kuke so. Amma ni ba zan kasance da ku kullum ba. 8Ta yi abin da ta iya yi. Ta zuba turare a jikina kafin lokaci, don shirin jana’izata. 9Gaskiya nake gaya muku, duk inda aka yi wa’azin bishara ko’ina a duniya, za a faɗi abin da ta yi, domin tunawa da ita.”

(Mattiyu 26.14-16; Luka 22.3-6)

10Sai Yahuda Iskariyot, ɗaya daga cikin Sha Biyun nan, ya je wajen manyan firistoci don yă bashe Yesu a gare su. 11Suka yi murna da jin haka, suka yi alkawari za su ba shi kuɗi. Don haka, ya fara neman zarafi yă ba da shi.

Abincin yamma na Ubangiji

(Mattiyu 26.17-25; Luka 22.7-14,21-23; Yohanna 13.21-30)

12A rana ta fari ta Bikin Burodi Marar Yisti, lokacin da akan yanka ɗan ragon hadayar kafara, bisa ga al’ada ta tunawa da Bikin Ƙetarewa, sai almajiran Yesu suka tambaye shi, suka ce, “Ina kake so mu je mu shirya maka wurin da za ka ci Bikin Ƙetarewa?”

13Sai ya aiki biyu daga cikin almajiransa ya ce, “Ku shiga cikin birni, za ku sadu da wani ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi. 14Gidan da ya shiga, ku gaya wa maigidan cewa, ‘Malam yana tambaya, ina ɗakin baƙina, inda zan ci Bikin Ƙetarewa tare da almajiraina?’ 15Zai nuna muku wani babban ɗakin sama da aka shirya domin baƙi. Ku yi mana shirin a can.”

16Almajiran suka tafi, suka shiga cikin birnin, suka kuwa tarar da kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.

17Da yamma ta yi, sai Yesu ya zo tare da Sha Biyun. 18Yayinda suke cin abinci a tebur, sai ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, ɗaya daga cikinku zai bashe ni, wani wanda yake ci tare da ni.”

19Suka cika da baƙin ciki, da ɗaya-ɗaya suka ce masa, “Tabbatacce, ba ni ba ne, ko?”

20Ya ce, “Ɗaya daga cikin Sha Biyun ne, wanda yake ci tare da ni a kwano. 21Ɗan Mutum zai tafi kamar yadda yake a rubuce game da shi, amma kaiton mutumin da ya bashe Ɗan Mutum! Zai fi masa, da ba a haife shi ba.”

(Mattiyu 26.26-30; Luka 22.14-23; 1 Korintiyawa 11.23-25)

22Yayinda suke cin abinci, sai Yesu ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya, ya ba wa almajiransa, yana cewa, “Ku karɓa, wannan jikina ne.”

23Sai kuma ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, ya kuma miƙa musu, dukansu suka sha daga ciki.

24Sai ya ce musu, “Wannan jinina ne na alkawari, wanda aka zubar da shi saboda mutane da yawa. 25Gaskiya nake gaya muku, ‘Ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai ranan nan, da zan sha shi sabo a mulkin Allah.’ ”

26Da suka rera waƙa, sai suka fita, suka tafi Dutsen Zaitun.

Yesu ya yi magana a kan mūsun Bitrus

(Mattiyu 26.31-35; Luka 22.31-34; Yohanna 13.36-38)

27Yesu ya ce musu, “Dukanku za ku ja da baya ku bar ni, gama yana a rubuce cewa,

“ ‘Zan bugi makiyayin tumaki,

tumakin kuwa za su warwatse.’14.27 Zak 13.7

28Amma bayan na tashi, zan sha gabanku zuwa Galili.”

29Bitrus ya ce, “Ko da duka sun ja da baya suka bar ka, ba zan bar ka ba.”

30Yesu ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, yau, tabbatacce, a daren nan, kafin zakara yă yi cara sau biyu14.30 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau biyu. kai da kanka za ka yi mūsun sanina sau uku.”

31Amma Bitrus ya yi ta nanatawa da ƙarfi ya ce, “Ko da zan mutu tare da kai, ba zan taɓa yin mūsun saninka ba.” Duk sauran ma suka ce haka.

Getsemane

(Mattiyu 26.36-46; Luka 22.39-46)

32Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.” 33Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai. 34Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”

35Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a. 36Ya ce, “Ya Abba,14.36 Da Arameyik na Baba Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”

37Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na sa’a ɗaya? 38Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”

39Ya sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi. 40Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.

41Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi. 42Ku tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!”

An kama Yesu

(Mattiyu 26.47-56; Luka 22.47-53; Yohanna 18.3-12)

43Yana cikin magana ke nan, sai Yahuda, ɗaya daga cikin Sha Biyun ya bayyana. Ya zo tare da taro da suke riƙe da takuba da sanduna. Manyan firistoci da malaman dokoki, da kuma dattawa ne suka turo taron.

44Mai bashe shi ɗin ya riga ya shirya alama da su cewa, “Wanda na yi wa sumba, shi ne mutumin, ku kama shi, ku riƙe sosai.” 45Nan da nan Yahuda ya je wurin Yesu ya ce, “Rabbi!” Ya kuma yi masa sumba. 46Mutanen kuwa suka kama Yesu, suka riƙe shi. 47Sai wani cikin waɗanda suke tsattsaye kusa ya zāre takobinsa, ya sare kunnen bawan babban firist.

48Yesu ya ce, “Ina jagoran wani tawaye ne da kuka fito da takuba da kuma sanduna domin ku kama ni? 49Kowace rana ina tare da ku, ina koyarwa a filin haikali, ba ku kama ni ba. Amma dole a cika Nassi.” 50Sai kowa ya yashe shi ya gudu.

51Wani saurayin da ba ya sanye da kome sai rigar lilin, yana bin Yesu. Da suka yi ƙoƙarin kama shi, 52sai ya gudu ya bar rigarsa, ya gudu tsirara.

A gaban majalisa

(Mattiyu 26.57-68; Luka 22.54,55,63-71; Yohanna 18.13,14,19-24)

53Suka kai Yesu wajen babban firist, sai dukan manyan firistoci, dattawa da kuma malaman dokoki suka taru. 54Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin filin gidan babban firist. A can, ya zauna tare da masu gadi, yana jin ɗumin wuta.

55Manyan firistoci da dukan ’yan Majalisa, suka shiga neman shaidar laifin da za a tabbatar a kan Yesu, domin su kashe shi. Amma ba su sami ko ɗaya ba. 56Da yawa suka ba da shaidar ƙarya a kansa, amma shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.

57Sai waɗansu suka miƙe tsaye, suka ba da wannan shaida ƙarya a kansa, suka ce, 58“Mun ji shi ya ce, ‘Zan rushe wannan haikali da mutum ya gina, cikin kwana uku, in sāke gina wani wanda ba ginin mutum ba.’ ” 59Duk da haka ma, shaidarsu ba tă zo ɗaya ba.

60Sai babban firist ya tashi a gabansu, ya tambayi Yesu ya ce, “Ba za ka amsa ba? Wane shaida ke nan waɗannan mutane suke kawowa a kanka?” 61Amma Yesu ya yi shiru, bai kuwa amsa ba.

Babban firist ya sāke tambayarsa ya ce, “Kai ne Kiristi, Ɗan Mai Albarka?”

62Yesu ya ce, “Ni ne. Za ku kuwa ga Ɗan Mutum yana zaune a hannun dama na Mai Iko, yana kuma zuwa a cikin gizagizan sama.”

63Babban firist ya yage tufafinsa, ya yi ce, “Ina dalilin neman waɗansu shaidu kuma? 64Kun dai ji saɓon. Me kuka gani?”

Duka suka yanke masa hukuncin kisa. 65Sai waɗansu suka fara tattofa masa miyau, suka rufe masa idanu, suka bubbuge shi da hannuwansu, suka ce, “Yi annabci!” Masu gadin kuma suka ɗauke shi, suka yi masa duka.

Bitrus ya yi mūsun sanin Yesu

(Mattiyu 26.69-75; Luka 22.56-62; Yohanna 18.15-18,25-27)

66Yayinda Bitrus yake ƙasa a filin gidan, sai wata yarinya, baiwa, ɗaya daga cikin ma’aikatan babban firist, ta zo can. 67Da ta ga Bitrus yana jin ɗumi, sai ta dube shi da kyau.

Ta ce, “Kai ma kana tare da Yesu, Banazare.”

68Amma ya yi mūsu ya ce, “Ban san abin da kike magana ba, balle ma in fahimce ki.” Sai ya fita zuwa zaure.14.68 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko suna da ƙofar shiga zakara kuwa ya yi cara

69Da baiwar ta gan shi a can, sai ta sāke gaya wa waɗanda suke tsattsaye a wurin, ta ce, “Wannan mutum yana ɗaya daga cikinsu.” 70Sai ya sāke yin musu.

Bayan ɗan lokaci kaɗan, sai waɗanda suke tsattsaye kusa suka ce wa Bitrus, “Lalle, kana ɗaya daga cikinsu, gama kai mutumin Galili ne.”

71Sai ya fara la’antar kansa, yana rantsuwa musu, yana cewa, “Ban san wannan mutumin da kuke magana a kai ba.”

72Nan da nan zakara ya yi cara sau na biyu.14.72 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau na biyu. Sai Bitrus ya tuna da maganar da Yesu ya yi masa cewa, “Kafin zakara yă yi cara sau biyu,14.72 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da sau biyu. za ka yi mūsun sanina sau uku.” Sai ya fashe da kuka.