Luke 19 – NIV & HCB

New International Version

Luke 19:1-48

Zacchaeus the Tax Collector

1Jesus entered Jericho and was passing through. 2A man was there by the name of Zacchaeus; he was a chief tax collector and was wealthy. 3He wanted to see who Jesus was, but because he was short he could not see over the crowd. 4So he ran ahead and climbed a sycamore-fig tree to see him, since Jesus was coming that way.

5When Jesus reached the spot, he looked up and said to him, “Zacchaeus, come down immediately. I must stay at your house today.” 6So he came down at once and welcomed him gladly.

7All the people saw this and began to mutter, “He has gone to be the guest of a sinner.”

8But Zacchaeus stood up and said to the Lord, “Look, Lord! Here and now I give half of my possessions to the poor, and if I have cheated anybody out of anything, I will pay back four times the amount.”

9Jesus said to him, “Today salvation has come to this house, because this man, too, is a son of Abraham. 10For the Son of Man came to seek and to save the lost.”

The Parable of the Ten Minas

11While they were listening to this, he went on to tell them a parable, because he was near Jerusalem and the people thought that the kingdom of God was going to appear at once. 12He said: “A man of noble birth went to a distant country to have himself appointed king and then to return. 13So he called ten of his servants and gave them ten minas.19:13 A mina was about three months’ wages. ‘Put this money to work,’ he said, ‘until I come back.’

14“But his subjects hated him and sent a delegation after him to say, ‘We don’t want this man to be our king.’

15“He was made king, however, and returned home. Then he sent for the servants to whom he had given the money, in order to find out what they had gained with it.

16“The first one came and said, ‘Sir, your mina has earned ten more.’

17“ ‘Well done, my good servant!’ his master replied. ‘Because you have been trustworthy in a very small matter, take charge of ten cities.’

18“The second came and said, ‘Sir, your mina has earned five more.’

19“His master answered, ‘You take charge of five cities.’

20“Then another servant came and said, ‘Sir, here is your mina; I have kept it laid away in a piece of cloth. 21I was afraid of you, because you are a hard man. You take out what you did not put in and reap what you did not sow.’

22“His master replied, ‘I will judge you by your own words, you wicked servant! You knew, did you, that I am a hard man, taking out what I did not put in, and reaping what I did not sow? 23Why then didn’t you put my money on deposit, so that when I came back, I could have collected it with interest?’

24“Then he said to those standing by, ‘Take his mina away from him and give it to the one who has ten minas.’

25“ ‘Sir,’ they said, ‘he already has ten!’

26“He replied, ‘I tell you that to everyone who has, more will be given, but as for the one who has nothing, even what they have will be taken away. 27But those enemies of mine who did not want me to be king over them—bring them here and kill them in front of me.’ ”

Jesus Comes to Jerusalem as King

28After Jesus had said this, he went on ahead, going up to Jerusalem. 29As he approached Bethphage and Bethany at the hill called the Mount of Olives, he sent two of his disciples, saying to them, 30“Go to the village ahead of you, and as you enter it, you will find a colt tied there, which no one has ever ridden. Untie it and bring it here. 31If anyone asks you, ‘Why are you untying it?’ say, ‘The Lord needs it.’ ”

32Those who were sent ahead went and found it just as he had told them. 33As they were untying the colt, its owners asked them, “Why are you untying the colt?”

34They replied, “The Lord needs it.”

35They brought it to Jesus, threw their cloaks on the colt and put Jesus on it. 36As he went along, people spread their cloaks on the road.

37When he came near the place where the road goes down the Mount of Olives, the whole crowd of disciples began joyfully to praise God in loud voices for all the miracles they had seen:

38“Blessed is the king who comes in the name of the Lord!”19:38 Psalm 118:26

“Peace in heaven and glory in the highest!”

39Some of the Pharisees in the crowd said to Jesus, “Teacher, rebuke your disciples!”

40“I tell you,” he replied, “if they keep quiet, the stones will cry out.”

41As he approached Jerusalem and saw the city, he wept over it 42and said, “If you, even you, had only known on this day what would bring you peace—but now it is hidden from your eyes. 43The days will come upon you when your enemies will build an embankment against you and encircle you and hem you in on every side. 44They will dash you to the ground, you and the children within your walls. They will not leave one stone on another, because you did not recognize the time of God’s coming to you.”

Jesus at the Temple

45When Jesus entered the temple courts, he began to drive out those who were selling. 46“It is written,” he said to them, “ ‘My house will be a house of prayer’19:46 Isaiah 56:7; but you have made it ‘a den of robbers.’19:46 Jer. 7:11

47Every day he was teaching at the temple. But the chief priests, the teachers of the law and the leaders among the people were trying to kill him. 48Yet they could not find any way to do it, because all the people hung on his words.

Hausa Contemporary Bible

Luka 19:1-48

Zakka mai karɓar haraji

1Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta. 2Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. 3Ya so yă ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne. 4Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.

5Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.” 6Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.

7Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ ”

8Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”

9Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne. 10Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”

Misalin mina goma

(Mattiyu 25.14-30)

11Yayinda suna cikin sauraron wannan, sai ya ci gaba da gaya musu wani misali, domin ya yi kusa da Urushalima, kuma mutanen suna tsammani mulkin Allah zai bayyana, nan da nan. 12Ya ce, “Wani mutum mai martaba ya tafi wata ƙasa mai nisa don a naɗa shi sarki sa’an nan ya dawo. 13Saboda haka ya kira bayinsa goma ya ba su mina goma. Ya ce, ‘Ku yi kasuwanci da kuɗin nan, sai na dawo.’

14“Amma talakawansa suka ƙi shi, sai suka aikar da wakilai bayansa, domin su ce, ‘Ba mu son wannan mutum ya zama sarkinmu.’

15“Duk da haka, aka naɗa shi sarki, sa’an nan ya dawo gida. Sai ya aika aka kira bayin da ya ba su kuɗin, don yă san ribar da suka samu.

16“Na fari ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar goma.’

17“Maigidan ya amsa ya ce, ‘Madalla, bawana mai kirki! Tun da ka yi aminci a kan abu ƙanƙani, ka yi riƙon birane goma.’

18“Na biyun ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, minarka ya sami ribar biyar.’

19“Maigidansa ya ce, ‘Kai ka yi riƙon birane biyar.’

20“Sai wani bawan ya zo ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ga minarka. Na ɓoye shi a wani ɗan tsumma. 21Na ji tsoronka, don kai mai wuyan sha’ani ne. Kakan ɗauki abin da ba ka ajiye ba, kakan kuma yi girbin abin da ba ka shuka ba.’

22“Sai maigidansa, ya amsa ya ce, ‘Zan hukunta ka a kan kalmominka, kai mugun bawa! Ashe, ka san cewa ni mai wuyan sha’ani ne, nakan ɗauka abin da ban ajiye ba, ina kuma girbin abin da ban shuka ba? 23Don me ba ka sa kuɗina a wajen ajiya, don in na dawo, in sami riba a kai ba?’

24“Sai ya ce wa waɗanda suke tsaye a wajen, ‘Ku karɓi minarsa ku ba wa wanda yake da mina goma.’

25“Suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ai, yana da guda goma ko!’

26“Ya amsa ya ce, ‘Ina gaya muku, duk wanda yake da abu, za a ƙara masa. Amma wanda ba shi da shi kuwa, ko abin da yake da shi ma, za a karɓe. 27Amma waɗannan abokan gābana, waɗanda ba su so in zama sarkinsu ba, ku kawo su nan, ku karkashe su, a gabana.’ ”

Shiga mai nasara

(Mattiyu 21.1-11; Markus 11.1-11; Yohanna 12.12-19)

28Bayan Yesu ya yi wannan magana, sai ya yi gaba zuwa Urushalima. 29Da ya kai kusa da Betfaji da Betani, a tudun da ake kira Dutsen Zaitun, sai ya aiki almajiransa guda biyu, ya ce musu, 30“Ku je ƙauyen da yake gaba da ku. Da kuna shiga, za ku tarar da wani ɗan jaki, wadda ba wanda ya taɓa hawa, a daure a wurin. Ku kunce shi ku kawo nan. 31In wani ya tambaye ku, ‘Don me kuke kunce shi?’ Ku ce masa, ‘Ubangiji yana bukatarsa.’ ”

32Waɗanda aka aika su yi gaba suka tafi, suka kuwa tarar kamar yadda ya gaya musu. 33Suna cikin kunce ɗan jakin, sai masu ɗan jakin suka ce musu, “Don me kuke kunce shi?”

34Suka amsa suka ce, “Ubangiji ne na bukatarsa.”

35Suka kawo shi wurin Yesu. Suka sa rigunarsu a kan ɗan jakin, sa’an nan suka sa Yesu a kai. 36Yana cikin tafiya, sai mutane suka shimfiɗa rigunarsu a kan hanya.

37Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,

38“Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”

“Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!”

39Sai waɗansu Farisiyawa a cikin taron suka ce wa Yesu, “Malam, ka kwaɓi almajiranka!”

40Ya amsa ya ce, “Ina gaya muku, ko da sun yi shiru, duwatsu za su fara kirari.”

41Da ya yi kusa da Urushalima, ya kuma ga birnin, sai ya yi kuka a kanta, 42kuma ya ce, “In ke, ko ke ɗin ma, dā ma kin san abin da zai kawo miki salama a wannan rana, amma yanzu an ɓoye shi daga idanunki. 43Ranakun za su auko miki, a lokacin da abokan gābanki za su gina bango gāba da ke, su kuma kewaye inda kike, za su kuma tsare kowane gefenki, su sa ke a tsakiya. 44Za su fyaɗa ke a ƙasa, ke da ’ya’yan da suke cikin katanganki. Ba za su bar wani dutse a kan wani ba, saboda ba ki gane da lokacin da Allah zai ziyarce ki ba.”

Yesu a haikali

(Mattiyu 21.12-17; Markus 11.15-19; Yohanna 2.13-22)

45Sai ya shiga filin haikali, ya fara korar masu sayar da kaya. 46Ya ce musu, “A rubuce, yake cewa, ‘Gidana, zai zama gidan addu’a,’19.46 Ish 56.7 amma ga shi kun mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”19.46 Irm 7.11

47Kowace rana, ya yi ta koyarwa a haikalin. Amma manyan firistoci, da malaman dokoki, da shugabannin mutane, suna ƙoƙarin kashe shi. 48Amma ba su sami hanyar yin haka ba, domin kalmominsa sun kama hankalin dukan mutanen.