Galatians 5 – NIV & HCB

New International Version

Galatians 5:1-26

Freedom in Christ

1It is for freedom that Christ has set us free. Stand firm, then, and do not let yourselves be burdened again by a yoke of slavery.

2Mark my words! I, Paul, tell you that if you let yourselves be circumcised, Christ will be of no value to you at all. 3Again I declare to every man who lets himself be circumcised that he is obligated to obey the whole law. 4You who are trying to be justified by the law have been alienated from Christ; you have fallen away from grace. 5For through the Spirit we eagerly await by faith the righteousness for which we hope. 6For in Christ Jesus neither circumcision nor uncircumcision has any value. The only thing that counts is faith expressing itself through love.

7You were running a good race. Who cut in on you to keep you from obeying the truth? 8That kind of persuasion does not come from the one who calls you. 9“A little yeast works through the whole batch of dough.” 10I am confident in the Lord that you will take no other view. The one who is throwing you into confusion, whoever that may be, will have to pay the penalty. 11Brothers and sisters, if I am still preaching circumcision, why am I still being persecuted? In that case the offense of the cross has been abolished. 12As for those agitators, I wish they would go the whole way and emasculate themselves!

Life by the Spirit

13You, my brothers and sisters, were called to be free. But do not use your freedom to indulge the flesh5:13 In contexts like this, the Greek word for flesh (sarx) refers to the sinful state of human beings, often presented as a power in opposition to the Spirit; also in verses 16, 17, 19 and 24; and in 6:8.; rather, serve one another humbly in love. 14For the entire law is fulfilled in keeping this one command: “Love your neighbor as yourself.”5:14 Lev. 19:18 15If you bite and devour each other, watch out or you will be destroyed by each other.

16So I say, walk by the Spirit, and you will not gratify the desires of the flesh. 17For the flesh desires what is contrary to the Spirit, and the Spirit what is contrary to the flesh. They are in conflict with each other, so that you are not to do whatever5:17 Or you do not do what you want. 18But if you are led by the Spirit, you are not under the law.

19The acts of the flesh are obvious: sexual immorality, impurity and debauchery; 20idolatry and witchcraft; hatred, discord, jealousy, fits of rage, selfish ambition, dissensions, factions 21and envy; drunkenness, orgies, and the like. I warn you, as I did before, that those who live like this will not inherit the kingdom of God.

22But the fruit of the Spirit is love, joy, peace, forbearance, kindness, goodness, faithfulness, 23gentleness and self-control. Against such things there is no law. 24Those who belong to Christ Jesus have crucified the flesh with its passions and desires. 25Since we live by the Spirit, let us keep in step with the Spirit. 26Let us not become conceited, provoking and envying each other.

Hausa Contemporary Bible

Galatiyawa 5:1-26

’Yanci cikin Kiristi

1Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.

2Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kuka yarda aka yi muku kaciya, wannan ya nuna Kiristi ba shi da amfani a gare ku ba ko kaɗan. 3Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yă kiyaye dukan Doka. 4Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi ke nan; kuka kuma fāɗi daga alheri. 5Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu. 6Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.

7Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku ya hana ku bin gaskiya? 8Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne. 9“Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.” 10Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne. 11’Yan’uwa, da a ce har yanzu ina wa’azin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan. 12Da ma a ce masu tā da hankalinku ɗin nan su yanke gabansu gaba ɗaya mana!

13Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka5.13 Ko kuwa na jiki; haka ma a ayoyi 16, 17, 19 da 24 a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna. 14Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”5.14 Fir 19.18 15In kun ci gaba da cizo, kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna.

Rayuwa ta wurin Ruhu

16Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba. 17Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so. 18Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan.

19Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata; 20bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya, 21da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.

22Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, 23sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa. 24Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa. 25Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu. 26Kada mu zama masu girman kai, muna tsokana muna kuma jin kishin juna.