1 Peter 5 – NIV & HCB

New International Version

1 Peter 5:1-14

To the Elders and the Flock

1To the elders among you, I appeal as a fellow elder and a witness of Christ’s sufferings who also will share in the glory to be revealed: 2Be shepherds of God’s flock that is under your care, watching over them—not because you must, but because you are willing, as God wants you to be; not pursuing dishonest gain, but eager to serve; 3not lording it over those entrusted to you, but being examples to the flock. 4And when the Chief Shepherd appears, you will receive the crown of glory that will never fade away.

5In the same way, you who are younger, submit yourselves to your elders. All of you, clothe yourselves with humility toward one another, because,

“God opposes the proud

but shows favor to the humble.”5:5 Prov. 3:34

6Humble yourselves, therefore, under God’s mighty hand, that he may lift you up in due time. 7Cast all your anxiety on him because he cares for you.

8Be alert and of sober mind. Your enemy the devil prowls around like a roaring lion looking for someone to devour. 9Resist him, standing firm in the faith, because you know that the family of believers throughout the world is undergoing the same kind of sufferings.

10And the God of all grace, who called you to his eternal glory in Christ, after you have suffered a little while, will himself restore you and make you strong, firm and steadfast. 11To him be the power for ever and ever. Amen.

Final Greetings

12With the help of Silas,5:12 Greek Silvanus, a variant of Silas whom I regard as a faithful brother, I have written to you briefly, encouraging you and testifying that this is the true grace of God. Stand fast in it.

13She who is in Babylon, chosen together with you, sends you her greetings, and so does my son Mark. 14Greet one another with a kiss of love.

Peace to all of you who are in Christ.

Hausa Contemporary Bible

1 Bitrus 5:1-14

Zuwa ga dattawa da kuma samari

1Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana. 2Ku zama makiyayan garken Allah da yake a ƙarƙashin kulawarku, kuna hidima kamar masu kula, ba kan dole ba, sai dai da yardar rai, yadda Allah yake so ku zama; ban da kwaɗayin kuɗi, sai dai marmarin yin hidima; 3ban da nuna iko a kan waɗanda aka danƙa muku amana, sai dai ku zama gurbi ga garken. 4Sa’ad da kuwa Babban Makiyayin ya bayyana, za ku karɓi rawanin ɗaukaka marar koɗewa.

5Samari, ku ma, ku yi biyayya ga waɗanda suka girme ku. Dukanku, ku yafa sauƙinkai ga juna, domin,

“Allah yana gāba da mai girman kai,

amma yakan yi alheri ga mai sauƙinkai.”5.5 K Mag 3.34

6Saboda haka, ku ƙasƙantar da kanku a ƙarƙashin hannun Allah mai ƙarfi, don yă ɗaukaka ku a lokacin da ya ga dama. 7Ku danƙa masa dukan damuwarku, domin shi ne yake lura da ku.

8Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye. 9Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

10Allah mai dukan alheri, wanda ya kira ku ga madawwamiyar ɗaukaka cikin Kiristi, bayan kun sha wahala na ɗan lokaci, shi da kansa zai raya ku, yă kuma sa ku yi ƙarfi, ku kahu, ku kuma tsaya daram. 11Gare shi bari iko yă tabbata har abada abadin. Amin.

Gaisuwar ƙarshe

12Da taimakon Sila, wanda na ɗauka a matsayin ɗan’uwa mai aminci, na rubuta muku a taƙaice, ina ƙarfafa ku ina kuma shaida muku cewa wannan shi ne alherin Allah na gaske. Ku tsaya daram a cikinsa.

13Ita wadda take a Babilon, zaɓaɓɓiya tare da ku, tana gaishe ku, haka ma ɗana Markus.

14Ku gai da juna da sumbar ƙauna.

Salama gare ku duka da kuke cikin Kiristi.