1 Corinthians 12 – NIV & HCB

New International Version

1 Corinthians 12:1-31

Concerning Spiritual Gifts

1Now about the gifts of the Spirit, brothers and sisters, I do not want you to be uninformed. 2You know that when you were pagans, somehow or other you were influenced and led astray to mute idols. 3Therefore I want you to know that no one who is speaking by the Spirit of God says, “Jesus be cursed,” and no one can say, “Jesus is Lord,” except by the Holy Spirit.

4There are different kinds of gifts, but the same Spirit distributes them. 5There are different kinds of service, but the same Lord. 6There are different kinds of working, but in all of them and in everyone it is the same God at work.

7Now to each one the manifestation of the Spirit is given for the common good. 8To one there is given through the Spirit a message of wisdom, to another a message of knowledge by means of the same Spirit, 9to another faith by the same Spirit, to another gifts of healing by that one Spirit, 10to another miraculous powers, to another prophecy, to another distinguishing between spirits, to another speaking in different kinds of tongues,12:10 Or languages; also in verse 28 and to still another the interpretation of tongues.12:10 Or languages; also in verse 28 11All these are the work of one and the same Spirit, and he distributes them to each one, just as he determines.

Unity and Diversity in the Body

12Just as a body, though one, has many parts, but all its many parts form one body, so it is with Christ. 13For we were all baptized by12:13 Or with; or in one Spirit so as to form one body—whether Jews or Gentiles, slave or free—and we were all given the one Spirit to drink. 14Even so the body is not made up of one part but of many.

15Now if the foot should say, “Because I am not a hand, I do not belong to the body,” it would not for that reason stop being part of the body. 16And if the ear should say, “Because I am not an eye, I do not belong to the body,” it would not for that reason stop being part of the body. 17If the whole body were an eye, where would the sense of hearing be? If the whole body were an ear, where would the sense of smell be? 18But in fact God has placed the parts in the body, every one of them, just as he wanted them to be. 19If they were all one part, where would the body be? 20As it is, there are many parts, but one body.

21The eye cannot say to the hand, “I don’t need you!” And the head cannot say to the feet, “I don’t need you!” 22On the contrary, those parts of the body that seem to be weaker are indispensable, 23and the parts that we think are less honorable we treat with special honor. And the parts that are unpresentable are treated with special modesty, 24while our presentable parts need no special treatment. But God has put the body together, giving greater honor to the parts that lacked it, 25so that there should be no division in the body, but that its parts should have equal concern for each other. 26If one part suffers, every part suffers with it; if one part is honored, every part rejoices with it.

27Now you are the body of Christ, and each one of you is a part of it. 28And God has placed in the church first of all apostles, second prophets, third teachers, then miracles, then gifts of healing, of helping, of guidance, and of different kinds of tongues. 29Are all apostles? Are all prophets? Are all teachers? Do all work miracles? 30Do all have gifts of healing? Do all speak in tongues12:30 Or other languages? Do all interpret? 31Now eagerly desire the greater gifts.

Love Is Indispensable

And yet I will show you the most excellent way.

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 12:1-31

Baye-bayen ruhaniya

1To, game da baye-baye na ruhaniya, ’yan’uwa, ba na so ku kasance da rashin sani. 2Kun san cewa sa’ad da kuke masu bautar gumaka, ya zama, an shawo kanku, aka kuma ɓad da ku ga bin gumaka marasa magana. 3Saboda haka, ina gaya muku cewa ba wani mai magana da ikon Ruhun Allah da zai ce, “Yesu la’ananne ne,” haka kuma ba wanda zai ce, “Yesu Ubangiji ne,” sai wanda Ruhu Mai Tsarki yake bi da shi.

4Akwai baye-baye iri dabam-dabam, amma Ruhu ɗaya ne. 5Akwai hidimomi iri-iri, amma Ubangiji ɗaya ne. 6Akwai aiki iri-iri, amma duk Allah ɗaya ne yake aikata su a cikin dukan mutane.

7An ba wa kowane mutum bayyanuwar Ruhu don amfanin kowa. 8Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. 9Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. 10Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna. 11Duk waɗannan aiki ne na wannan Ruhu guda, yana kuma ba da su ga kowane mutum, yadda yake so.

12Jiki guda ne, ko da yake an yi shi da gaɓoɓi da yawa; gaɓoɓin kuma ko da yake da yawa suke, jiki ɗaya ne. Haka yake da Kiristi. 13Dukanmu an yi mana baftisma ta wurin Ruhu guda zuwa ga jiki guda, ko Yahudawa ko Hellenawa, bawa ko ’yantacce, an kuma ba wa dukanmu wannan Ruhu guda mu sha. 14To, ba a yi jiki da gaɓa ɗaya kawai ba, amma da gaɓoɓi da yawa.

15Da ƙafa za tă ce, “Saboda ni ba hannu ba ce, ni ba gaɓar jiki ba ce.” Wannan ba zai hana ta zama gaɓar jikin ba. 16Da kunne zai ce, “Saboda ni ba ido ba ne, ni ba gaɓar jiki ba ne.” Wannan ba zai hana shi zama gaɓar jikin ba. 17Da a ce dukan jiki ido ne, da me za a ji? Da kuma a ce dukan jiki kunne ne, da me za a sansana? 18Tabbatacce, Allah ya shirya gaɓoɓin jiki, kowannensu, kamar yadda yake so su zama. 19Da a ce dukan jiki gaɓa ɗaya ne, da ina sauran jikin? 20Yadda yake dai, akwai gaɓoɓi da yawa, amma jiki ɗaya.

21Ba dama ido ya ce wa hannu, “Ba na bukatarka ba!” Kai kuma ba zai ce wa ƙafafu, “Ba na bukatarku ba!” 22A maimakon haka, gaɓoɓin jiki da ake gani kamar ba su da ƙarfi, su ne masu muhimmanci. 23Kuma gaɓoɓin da muke tsammani ba su da martaba sosai, su ne mukan fi ba su girma. Sa’an nan gaɓoɓi marasa kyan gani, mun fi mai da hankali a kansu, 24gaɓoɓi masu kyan gani kuwa, ba su bukatar yawan girmamawa. Allah ya harhaɗa jikunanmu yadda gaɓoɓin da ake gani kamar ba su da muhimmanci suna da amfani, 25don kada rarrabuwa ta kasance a jiki, sai dai gaɓoɓin jiki su kula da juna. 26In wata gaɓa tana a damuwa, duk sai su damu tare. In kuma an ɗaukaka wata gaɓa, sai duk su yi farin ciki tare.

27To, ku jikin Kiristi ne, kowannenku kuwa gaɓarsa ne. 28A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri. 29Shin, duka ne manzanni? Duka ne annabawa? Duka ne malamai? Duka ne suke da baiwar yin ayyukan banmamaki? 30Duka ne suke da baiwar warkarwa? Duka ne suke magana da harsuna? Duka ne suke iya fassara? 31Sai dai ku yi marmarin neman baye-baye mafi girma.

Yanzu kuwa zan nuna muku mafificiyar hanya.