1 Corinthians 10 – NIV & HCB

New International Version

1 Corinthians 10:1-33

Warnings From Israel’s History

1For I do not want you to be ignorant of the fact, brothers and sisters, that our ancestors were all under the cloud and that they all passed through the sea. 2They were all baptized into Moses in the cloud and in the sea. 3They all ate the same spiritual food 4and drank the same spiritual drink; for they drank from the spiritual rock that accompanied them, and that rock was Christ. 5Nevertheless, God was not pleased with most of them; their bodies were scattered in the wilderness.

6Now these things occurred as examples to keep us from setting our hearts on evil things as they did. 7Do not be idolaters, as some of them were; as it is written: “The people sat down to eat and drink and got up to indulge in revelry.”10:7 Exodus 32:6 8We should not commit sexual immorality, as some of them did—and in one day twenty-three thousand of them died. 9We should not test Christ,10:9 Some manuscripts test the Lord as some of them did—and were killed by snakes. 10And do not grumble, as some of them did—and were killed by the destroying angel.

11These things happened to them as examples and were written down as warnings for us, on whom the culmination of the ages has come. 12So, if you think you are standing firm, be careful that you don’t fall! 13No temptation10:13 The Greek for temptation and tempted can also mean testing and tested. has overtaken you except what is common to mankind. And God is faithful; he will not let you be tempted10:13 The Greek for temptation and tempted can also mean testing and tested. beyond what you can bear. But when you are tempted,10:13 The Greek for temptation and tempted can also mean testing and tested. he will also provide a way out so that you can endure it.

Idol Feasts and the Lord’s Supper

14Therefore, my dear friends, flee from idolatry. 15I speak to sensible people; judge for yourselves what I say. 16Is not the cup of thanksgiving for which we give thanks a participation in the blood of Christ? And is not the bread that we break a participation in the body of Christ? 17Because there is one loaf, we, who are many, are one body, for we all share the one loaf.

18Consider the people of Israel: Do not those who eat the sacrifices participate in the altar? 19Do I mean then that food sacrificed to an idol is anything, or that an idol is anything? 20No, but the sacrifices of pagans are offered to demons, not to God, and I do not want you to be participants with demons. 21You cannot drink the cup of the Lord and the cup of demons too; you cannot have a part in both the Lord’s table and the table of demons. 22Are we trying to arouse the Lord’s jealousy? Are we stronger than he?

The Believer’s Freedom

23“I have the right to do anything,” you say—but not everything is beneficial. “I have the right to do anything”—but not everything is constructive. 24No one should seek their own good, but the good of others.

25Eat anything sold in the meat market without raising questions of conscience, 26for, “The earth is the Lord’s, and everything in it.”10:26 Psalm 24:1

27If an unbeliever invites you to a meal and you want to go, eat whatever is put before you without raising questions of conscience. 28But if someone says to you, “This has been offered in sacrifice,” then do not eat it, both for the sake of the one who told you and for the sake of conscience. 29I am referring to the other person’s conscience, not yours. For why is my freedom being judged by another’s conscience? 30If I take part in the meal with thankfulness, why am I denounced because of something I thank God for?

31So whether you eat or drink or whatever you do, do it all for the glory of God. 32Do not cause anyone to stumble, whether Jews, Greeks or the church of God— 33even as I try to please everyone in every way. For I am not seeking my own good but the good of many, so that they may be saved.

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 10:1-33

Gargaɗi daga tarihin Isra’ila

1Ba na so ku kasance da rashin sani, ’yan’uwa, cewa dukan kakannin-kakanninmu sun yi tafiya a ƙarƙashin girgije, dukansu kuma suka bi ta tsakiyar teku. 2An yi wa dukansu baftisma ga bin Musa a cikin girgije da kuma cikin teku. 3Dukansu sun ci abincin ruhaniya guda 4suka kuma sha ruwan ruhaniyan nan guda; gama sun sha daga dutsen ruhaniya nan, wanda ya yi tafiya tare da su, wannan dutsen kuwa Kiristi ne. 5Duk da haka, Allah bai ji daɗin yawancinsu ba; gawawwakinsu kuwa suka bazu ko’ina a cikin hamada.

6To, waɗannan abubuwa misalai10.6 Ko kuwa ire-ire; haka ma a aya 11 ne a gare mu, kada mu yi marmarin mugayen abubuwa, kamar yadda suka yi. 7Kada ku zama masu bautar gumaka, yadda waɗansunsu suka zama; kamar yadda yake a rubuce cewa, “Mutanen suka zauna don su ci su kuma sha, suka kuma tashi suka shiga rawa ta rashin kunya.”10.7 Fit 32.6 8Kada fa mu yi fasikanci yadda waɗansunsu suka yi, har a rana guda mutane dubu ashirin da uku a cikinsu suka mutu. 9Kada mu gwada Kiristi yadda waɗansunsu suka yi, har macizai suka kakkashe su. 10Kada kuma ku yi gunaguni yadda waɗansunsu suka yi, har mala’ika mai hallakarwa ya hallaka su. 11Waɗannnan abubuwa sun same su ne, domin su zama abubuwan koyi, aka kuma rubuta su domin a gargaɗe mu, mu da ƙarshen zamani ya zo mana. 12Saboda haka in kana tsammani kana tsaye ne, to, ka yi hankali kada ka fāɗi! 13Ba jarrabar da ta taɓa samunku, wadda ba a saba yi wa mutum ba. Allah mai aminci ne; ba zai bari a jarrabce ku fiye da ƙarfinku ba. Amma in aka jarrabce ku, zai nuna muku mafita, domin ku iya cin nasara.

Bukukkuwan gumaka da cimar Ubangiji

14Saboda haka abokaina ƙaunatattu, ku guje wa bautar gumaka. 15Ina magana da ku a kan ku mutane ne fa masu azanci; ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa. 16Kwaf nan na godiya da muke yin godiya da shi, ashe ba tarayya ce a cikin jinin Kiristi ba? Wannan burodi kuma da muke karya mu ci, ashe, ba tarayya ne a cikin jikin Kiristi ba? 17Da yake burodin nan ɗaya ne, ashe kuwa, mu da muke da yawa jiki ɗaya ne, gama dukanmu muna ci daga burodi nan guda.

18Ku dubi mutanen Isra’ila mana. Ashe, waɗanda suke cin hadayu, ba ɗaya suke da juna cikin cin hadayun da aka miƙa a bagade ba? 19To, me kuke tsammani nake nufi a nan? Hadayar da aka miƙa wa gunki ce wani abu, ko kuma gunkin ne wani abu? 20A’a, ina nufin akan miƙa hadayun da masu bautar gumaka suka wa aljanu ne, ba Allah ba. Ba na so ku zama ɗaya da aljanu. 21Ba zai yiwu ku sha daga kwaf na Ubangiji ku kuma sha daga kwaf na aljanu ba, ba ya yiwuwa ku ci a teburin Ubangiji, ku kuma ci a teburin aljanu. 22Ashe, so muke mu tsokani Ubangiji ya yi kishi? Mun fi shi ƙarfi ne?

’Yancin mai bi

23“Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa. 24Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma. 25Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito, 26gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.”10.26 Zab 24.1

27In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito. 28Sai dai in wani ya ce muku, “Ai, wannan an miƙa ne wa gunki,” to, kada ku ci, saboda duban mutuncin wannan da ya gaya muku, don kuma lamiri yă kasance babu laifi 29ina nufin lamirin wancan mutum ne fa, ba naku ba. Don me lamirin wani zai shari’anta ’yancina? 30In na ci abinci da godiya, don me za a zarge ni a kan abin da na ci da godiya ga Allah?

31Saboda haka, duk abin da kuke yi, ko ci ko sha, ku yi shi duka saboda ɗaukakar Allah. 32Kada ku sa wani yă yi tuntuɓe, ko mutumin Yahuda ne, ko mutumin Al’ummai ko kuma ikkilisiyar Allah 33kamar dai yadda nake ƙoƙarin faranta wa kowa rai, ta kowace hanya. Gama ba don kaina kaɗai nake yi ba, sai dai don amfanin mutane da yawa, don su sami ceto.