Luke 9 – NIRV & HCB

New International Reader’s Version

Luke 9:1-62

Jesus Sends Out the Twelve Disciples

1Jesus called together the 12 disciples. He gave them power and authority to drive out all demons and to heal sicknesses. 2Then he sent them out to announce God’s kingdom and to heal those who were sick. 3He told them, “Don’t take anything for the journey. Do not take a walking stick or a bag. Do not take any bread, money or extra clothes. 4When you are invited into a house, stay there until you leave town. 5Some people may not welcome you. If they don’t, leave their town and shake the dust off your feet. This will be a witness against the people living there.” 6So the 12 disciples left. They went from village to village. They announced the good news and healed people everywhere.

7Now Herod, the ruler of Galilee, heard about everything that was going on. He was bewildered, because some were saying that John the Baptist had been raised from the dead. 8Others were saying that Elijah had appeared. Still others were saying that a prophet of long ago had come back to life. 9But Herod said, “I had John’s head cut off. So who is it that I hear such things about?” And he tried to see Jesus.

Jesus Feeds the Five Thousand

10The disciples returned. They told Jesus what they had done. Then he took them with him. They went off by themselves to a town called Bethsaida. 11But the crowds learned about it and followed Jesus. He welcomed them and spoke to them about God’s kingdom. He also healed those who needed to be healed.

12Late in the afternoon the 12 disciples came to him. They said, “Send the crowd away. They can go to the nearby villages and countryside. There they can find food and a place to stay. There is nothing here.”

13Jesus replied, “You give them something to eat.”

The disciples answered, “We have only five loaves of bread and two fish. We would have to go and buy food for all this crowd.” 14About 5,000 men were there.

But Jesus said to his disciples, “Have them sit down in groups of about 50 each.” 15The disciples did so, and everyone sat down. 16Jesus took the five loaves and the two fish. He looked up to heaven and gave thanks. He broke them into pieces. Then he gave them to the disciples to give to the people. 17All of them ate and were satisfied. The disciples picked up 12 baskets of leftover pieces.

Peter Says That Jesus Is the Messiah

18One day Jesus was praying alone. Only his disciples were with him. He asked them, “Who do the crowds say I am?”

19They replied, “Some say John the Baptist. Others say Elijah. Still others say that one of the prophets of long ago has come back to life.”

20“But what about you?” he asked. “Who do you say I am?”

Peter answered, “God’s Messiah.”

Jesus Speaks About His Coming Death

21Jesus strongly warned them not to tell this to anyone. 22He said, “The Son of Man must suffer many things. The elders will not accept him. The chief priests and the teachers of the law will not accept him either. He must be killed and on the third day rise from the dead.”

23Then he said to all of them, “Whoever wants to follow me must say no to themselves. They must pick up their cross every day and follow me. 24Whoever wants to save their life will lose it. But whoever loses their life for me will save it. 25What good is it if someone gains the whole world but loses or gives up their very self? 26Suppose someone is ashamed of me and my words. The Son of Man will come in his glory and in the glory of the Father and the holy angels. Then he will be ashamed of that person.

27“What I’m about to tell you is true. Some who are standing here will not die before they see God’s kingdom.”

Jesus’ Appearance Is Changed

28About eight days after Jesus said this, he went up on a mountain to pray. He took Peter, John and James with him. 29As he was praying, the appearance of his face changed. His clothes became as bright as a flash of lightning. 30Two men, Moses and Elijah, appeared in shining glory. Jesus and the two of them talked together. 31They talked about how he would be leaving them soon. This was going to happen in Jerusalem. 32Peter and his companions had been very sleepy. But then they became completely awake. They saw Jesus’ glory and the two men standing with him. 33As the men were leaving Jesus, Peter spoke up. “Master,” he said to him, “it is good for us to be here. Let us put up three shelters. One will be for you, one for Moses, and one for Elijah.” Peter didn’t really know what he was saying.

34While he was speaking, a cloud appeared and covered them. The disciples were afraid as they entered the cloud. 35A voice came from the cloud. It said, “This is my Son, and I have chosen him. Listen to him.” 36When the voice had spoken, they found that Jesus was alone. The disciples kept quiet about this. They didn’t tell anyone at that time what they had seen.

Jesus Heals a Boy Who Is Controlled by an Evil Spirit

37The next day Jesus and those who were with him came down from the mountain. A large crowd met Jesus. 38A man in the crowd called out. “Teacher,” he said, “I beg you to look at my son. He is my only child. 39A spirit takes hold of him, and he suddenly screams. It throws him into fits so that he foams at the mouth. It hardly ever leaves him. It is destroying him. 40I begged your disciples to drive it out. But they couldn’t do it.”

41“You unbelieving and evil people!” Jesus replied. “How long do I have to stay with you? How long do I have to put up with you?” Then he said to the man, “Bring your son here.”

42Even while the boy was coming, the demon threw him into a fit. The boy fell to the ground. But Jesus ordered the evil spirit to leave the boy. Then Jesus healed him and gave him back to his father. 43They were all amazed at God’s greatness.

Jesus Speaks a Second Time About His Coming Death

Everyone was wondering about all that Jesus did. Then Jesus said to his disciples, 44“Listen carefully to what I am about to tell you. The Son of Man is going to be handed over to men.” 45But they didn’t understand what this meant. That was because it was hidden from them. And they were afraid to ask Jesus about it.

Who Is the Most Important Person?

46The disciples began to argue about which one of them would be the most important person. 47Jesus knew what they were thinking. So he took a little child and had the child stand beside him. 48Then he spoke to them. “Anyone who welcomes this little child in my name welcomes me,” he said. “And anyone who welcomes me welcomes the one who sent me. The one considered least important among all of you is really the most important.”

49“Master,” said John, “we saw someone driving out demons in your name. We tried to stop him, because he is not one of us.”

50“Do not stop him,” Jesus said. “Anyone who is not against you is for you.”

The Samaritans Do Not Welcome Jesus

51The time grew near for Jesus to be taken up to heaven. So he made up his mind to go to Jerusalem. 52He sent messengers on ahead. They went into a Samaritan village to get things ready for him. 53But the people there did not welcome Jesus. That was because he was heading for Jerusalem. 54The disciples James and John saw this. They asked, “Lord, do you want us to call down fire from heaven to destroy them?” 55But Jesus turned and commanded them not to do it. 56Then Jesus and his disciples went on to another village.

The Cost of Following Jesus

57Once Jesus and those who were with him were walking along the road. A man said to Jesus, “I will follow you no matter where you go.”

58Jesus replied, “Foxes have dens. Birds have nests. But the Son of Man has no place to lay his head.”

59He said to another man, “Follow me.”

But the man replied, “Lord, first let me go and bury my father.”

60Jesus said to him, “Let dead people bury their own dead. You go and tell others about God’s kingdom.”

61Still another person said, “I will follow you, Lord. But first let me go back and say goodbye to my family.”

62Jesus replied, “Suppose someone starts to plow and then looks back. That person is not fit for service in God’s kingdom.”

Hausa Contemporary Bible

Luka 9:1-62

Yesu ya aiki sha biyun

(Mattiyu 10.5-15; Markus 6.7-13)

1Bayan da Yesu ya tara Sha Biyun wuri ɗaya, sai ya ba su iko da izini na fitar da dukan aljanu, da na warkar da cututtuka. 2Ya kuma aike su, su yi wa’azin mulkin Allah, su kuma warkar da marasa lafiya. 3Ya ce musu, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, wato, ba sanda, ba jaka, ba burodi, ba kuɗi, ba riga na biyu. 4Duk gidan da kuka sauka, ku zauna nan sai kun bar garin. 5In mutane ba su karɓe ku ba, sa’ad da kun bar garinsu, ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku don shaida a kansu.” 6Sai suka tashi suka shiga ƙauye zuwa ƙauye suna wa’azin bishara, suna warkar da marasa lafiya a ko’ina.

(Mattiyu 14.1-12; Markus 6.14-29)

7Yanzu fa, Hiridus mai sarauta ya ji labarin dukan abubuwan da suke faruwa. Sai ya rikice, don waɗansu mutane suna cewa, Yohanna Mai Baftisma ne ya tashi daga matattu, 8waɗansu kuma suna cewa, annabi Iliya ne ya sāke bayyana. Waɗansu kuma har wa yau, suna cewa, ɗaya daga cikin annabawa na dā ne, ya tashi. 9Amma Hiridus ya ce, “Yohanna dai na yanke kansa, amma wanne mutum ne nake jin labarin abubuwan nan a kansa?” Sai ya yi ƙoƙari ya ga Yesu.

Yesu ya ciyar da dubu biyar

(Mattiyu 14.13-21; Markus 6.30-44; Yohanna 6.1-14)

10Da manzannin suka dawo, sai suka faɗa wa Yesu abin da suka yi. Sai ya ɗauke su, suka keɓe kansu su kaɗai, zuwa wani gari da ake kira Betsaida. 11Amma taron mutane suka ji labari, sai suka bi shi. Ya marabce su, kuma ya yi musu magana a kan mulkin Allah, ya kuma warkar da masu bukatar warkarwa.

12Da rana ta kusa fāɗuwa, sai Sha Biyun suka zo wurinsa, suka ce, “Ka sallami taron domin su shiga ƙauyuka na kewaye, su nemi abin da za su ci, da wurin kwana, don inda muke, ba kowa.”

13Yesu ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.”

Sai suka ce masa, “Muna da burodi biyar da kifi biyu kaɗai. Sai dai, in mun je mu sayi abinci domin dukan wannan taron.” 14Maza kaɗai sun kai kusan dubu biyar.

Amma ya ce wa almajiransa, “Ku sa su su zauna a ƙungiya hamsin-hamsin.” 15Haka almajiran suka yi, kowa kuwa ya zauna. 16Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen. 17Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.

Shaidar Bitrus a kan Yesu

(Mattiyu 16.13-19; Markus 8.27-29)

18Wata rana sa’ad da Yesu yana addu’a a ɓoye, almajiransa kuma suna tare da shi, sai ya tambaye, su ya ce, “Wa, taron mutane ke ce da ni?”

19Suka amsa, suka ce, “Waɗansu suna cewa, Yohanna Mai Baftisma, waɗansu kuma annabi Iliya, har wa yau waɗansu suna cewa, kai ɗaya daga cikin annabawan da ne, da ya tashi da rai.”

20“Amma ku fa, wa, kuke ce da ni?”

Bitrus ya amsa ya ce, “Kiristi na Allah.”

(Mattiyu 16.20-28; Markus 8.30–9.1)

21Yesu ya gargaɗe su da ƙarfi, kada su gaya wa kowa wannan magana. 22Ya sāke cewa, “Dole ne Ɗan mutum ya sha wahaloli da yawa, dattawa, da manyan firistoci, da malaman dokoki kuma su ƙi shi, kuma dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tā da shi da rai.”

23Sai ya ce wa dukansu, “In wani zai bi ni, dole yă mūsanta kansa, ya ɗauki gicciyensa kowace rana, ya bi ni. 24Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni zai same shi. 25Ina amfani, in mutum ya ribato duniya duka, amma ya rasa ransa, ko kuma ya yi hasarar ransa. 26Duk wanda yake jin kunyana da na kalmomina, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa sa’ad da zai zo a cikin ɗaukakarsa, da ɗaukakar Uban, da kuma ta tsarkaka mala’ikun.

27“Gaskiya nake gaya muku, waɗansu da suke tsattsaye a nan ba za su ga mutuwa ba, sai sun ga mulkin Allah.”

Sāke kamanni

(Mattiyu 17.1-8; Markus 9.2-8)

28Bayan kamar kwana takwas da yin wannan magana, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yohanna, da kuma Yaƙub, suka hau kan dutse tare don yin addu’a. 29Yana cikin addu’a, sai kamannin fuskarsa ta sāke, tufafinsa kuma suka zama da haske kamar hasken walƙiya. 30Sai ga mutum biyu, Musa da Iliya, suka bayyana cikin kyakkyawar daraja, suna magana da Yesu. 31Suka yi zance a kan tashinsa, wanda shi ya kusan ya kawo ga cikarsa a Urushalima. 32Barci kuwa ya kama Bitrus da abokan tafiyarsa sosai. Da idanunsu suka warware, sai suka ga ɗaukakarsa da kuma mutum biyun tsaye tare da shi. 33Da mutanen na barin Yesu, sai Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. Bari mu kafa bukkoki guda uku, wato, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.” (Bai ma san abin da yake faɗi ba.)

34Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije ya bayyana ya rufe su, sai suka ji tsoro, yayinda suke shiga cikin girgijen. 35Wata murya ta fito daga cikin girgijen, tana cewa, “Wannan Ɗana ne, zaɓaɓɓena, ku saurare shi.” 36Da muryar ta gama magana, sai suka tarar Yesu shi kaɗai ne. Almajiran kuwa suka riƙe wannan al’amari a zukatansu. A lokacin nan, ba su gaya wa kowa abin da suka gani ba.

Warkar da yaro mai mugun ruhu

(Mattiyu 17.14-18; Markus 9.14-27)

37Kashegari, sa’ad da Yesu tare da almajiran nan uku suka sauka daga kan dutsen, sai taro mai yawa ya haɗu da shi. 38Sai wani mutum daga cikin taron ya yi kira da ƙarfi ya ce, “Malam, ina roƙonka, ka dubi ɗan nan nawa, gama shi ne kaɗai nake da shi. 39Wani ruhu yakan kama shi, sai ya yi ihu farar ɗaya. Yakan sa shi farfaɗiya, har bakinsa ya yi kumfa. Da ƙyar yake barinsa, yana kuwa kan hallakar da shi. 40Na roƙi almajiranka su fitar da shi, amma ba su iya ba.”

41Yesu ya amsa ya ce, “Ya karkataccen zamani marar bangaskiya, har yaushe ne zan kasance tare da ku, ina kuma haƙuri da ku? Kawo yaronka nan.”

42Yaron yana kan zuwa ke nan, sai aljanin ya buga shi ƙasa, cikin farfaɗiya. Amma Yesu ya kwaɓe mugun ruhun, ya warkar da yaron, sai ya miƙa shi ga mahaifinsa. 43Duk suka yi mamakin girman Allah.

(Mattiyu 17.22,23; Markus 9.30-32)

Yayinda kowa yana cikin mamakin dukan abubuwan da Yesu ya yi, sai ya ce wa almajiransa, 44“Ku kasa kunne da kyau ga abin da zan faɗa muku. Za a bashe Ɗan Mutum ga hannun mutane.” 45Amma ba su fahimci abin da yake nufi da wannan magana ba. Ba su gane ba, don an ɓoye musu shi. Su kuwa sun ji tsoro su tambaye shi.

Wa zai zama mafi girma?

(Mattiyu 18.1-5; Markus 9.33-37)

46Wata gardama ta tashi a tsakanin almajiran, a kan ko wane ne a cikinsu zai zama mafi girma 47Da yake Yesu ya san tunaninsu, sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa ya tsaya kusa da shi. 48Sai ya ce musu, “Duk wanda ya karɓi wannan ƙaramin yaron a cikin sunana, ni ya karɓa, kuma duk wanda ya karɓe ni, ya karɓi wanda ya aiko ni ne. Gama mafi ƙanƙanta duka a cikinku, shi ne kuma mafi girma.”

(Markus 9.38-40)

49Sai Yohanna ya ce, “Ubangiji, mun ga wani mutum yana fitar da aljanu a cikin sunanka, muka yi ƙoƙarin hana shi, don shi ba ɗaya ba ne daga cikinmu.”

50Yesu ya ce, “Kada ku hana shi, gama duk wanda ba ya gāba da ku, naku ne.”

Hamayyar Samariyawa

51Da lokaci ya yi kusa da za a ɗauki Yesu zuwa sama, sai ya ɗaura niyyar tafiya Urushalima. 52Sai ya aiki ’yan saƙo, su yi gaba. Su kuwa, suka shiga cikin wani ƙauyen Samariyawa, don su shirya masa abubuwa. 53Amma mutanen ƙauyen ba su karɓe shi ba, don yana kan hanyar zuwa Urushalima ne. 54Da almajiransa, Yaƙub da Yohanna suka ga haka, sai suka yi tambaya suka ce, “Ubangiji, kana so mu kira wuta ta sauka daga sama ta hallaka su?” 55Amma Yesu ya juya, ya kwaɓe su. 56Sai shi da almajiransa suka tafi wani ƙauye.

Wahalar bin Yesu

(Mattiyu 8.19-22)

57Suna kan tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, “Zan bi ka, duk inda za ka.”

58Yesu ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”

59Ya kuma ce wa wani mutum, “Ka bi ni.”

Amma mutumin ya amsa ya ce, “Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna.”

60Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah.”

61Har wa yau, wani ya ce, “Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna.”

62Yesu ya amsa ya ce, “Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba.”