1ሽማግሌው፤
በእውነት ለምወድዳት፣ እኔ ብቻ ሳልሆን እውነትን የሚያውቁ ሁሉ ለሚወድዷት ለተመረጠችው እመቤትና ለልጆቿ፤ 2በውስጣችን ከሚኖርና ከእኛ ጋር ለዘላለም ከሚሆን እውነት የተነሣ፤
3ከእግዚአብሔር አብና የአብ ልጅ ከሆነው ከኢየሱስ ክርስቶስ ጸጋ፣ ምሕረትና ሰላም በእውነትና በፍቅር ከእኛ ጋር ይሆናል።
4ከልጆችሽ አንዳንዶቹ ከአብ በተሰጠን ትእዛዝ መሠረት በእውነት ጸንተው እየሄዱ በማግኘቴ እጅግ ደስ ብሎኛል። 5አሁንም እመቤት ሆይ፤ ከመጀመሪያ የነበረችውን እንጂ አዲስ ትእዛዝ አልጽፍልሽም፤ ይኸውም እርስ በርሳችን እንዋደድ ዘንድ ነው። 6ይህም ፍቅር፣ በትእዛዞቹ መሠረት እንመላለስ ዘንድ ነው። ትእዛዙም ከመጀመሪያ እንደ ሰማችሁት በፍቅር እንድትኖሩ ነው።
7ኢየሱስ ክርስቶስ በሥጋ እንደ መጣ የማያምኑ ብዙ አሳቾች ወደ ዓለም ወጥተዋል። እንዲህ ያለ ማንኛውም ሰው አታላይና የክርስቶስ ተቃዋሚ ነው። 8እናንተም የደከማችሁበትን ዋጋ እንዳታጡ፣ ነገር ግን ሙሉ ሽልማት እንድትቀበሉ ለራሳችሁ ተጠንቀቁ። 9በክርስቶስ ትምህርት የማይኖርና ከትምህርቱ የሚወጣ ሁሉ አምላክ የለውም፤ በክርስቶስ ትምህርት የሚኖር ግን አብም ወልድም አለው። 10ማንም ወደ እናንተ ቢመጣ፣ ይህንም ትምህርት ባያመጣ በቤታችሁ አትቀበሉት፤ ሰላምም አትበሉት፤ 11የሚቀበለው ሰው፣ የክፉ ሥራው ተባባሪ ይሆናልና።
12የምጽፍላችሁ ብዙ ነገር ነበረኝ፤ ይሁን እንጂ በወረቀትና በቀለም እንዲሆን አልፈልግም፤ ዳሩ ግን ደስታችን ፍጹም ይሆን ዘንድ ወደ እናንተ መጥቼ ፊት ለፊት ላነጋግራችሁ ተስፋ አደርጋለሁ።
13የተመረጠችው የእኅትሽ ልጆች ሰላምታ ያቀርቡልሻል።
1Dattijon nan,
Zuwa ga uwargida zaɓaɓɓiya da kuma ’ya’yanta, waɗanda nake ƙauna ƙwarai da gaske kuma ba ni kaɗai ba, amma har da dukan waɗanda suka san gaskiya. 2Muna ƙaunarku saboda gaskiyan nan, wadda take cikinmu za tă kuma kasance tare da mu har abada.
3Alheri, jinƙai da kuma salama daga Allah Uba da kuma Yesu Kiristi, Ɗan Uba, su kasance tare da mu cikin gaskiya da ƙauna.
4Na yi farin ciki ƙwarai, da na sami waɗansu ’ya’yanki suna tafiya cikin gaskiya, kamar yadda Uba ya umarce mu. 5Yanzu kuma, uwargida ƙaunatacciya, ba sabon umarni nake rubuta miki ba sai dai wanda muke da shi tun farko. Ina roƙo cewa mu ƙaunaci juna. 6Ƙauna, ita ce mu yi biyayya ga umarnansa. Kamar yadda kuka ji tun da fari, umarninsa shi ne ku yi zaman ƙauna.
7Masu ruɗi da yawa, waɗanda ba su yarda da zuwan Yesu Kiristi cikin jiki ba, sun riga sun fito a duniya. Duk irin mutumin nan mai ruɗi ne kuma magabcin Kiristi. 8Ku lura don kada ku yi hasarar aikin da kuka yi, sai dai ku sami cikakken lada. 9Duk mutumin da bai tsaya a kan koyarwar Kiristi ba, amma ya yi ƙari a kanta, mutumin nan ba shi da Allah. Amma wanda ya tsaya a kan koyarwar Kiristi, yana da Uban da kuma Ɗan. 10Duk wanda ya zo wurinku bai kuma kawo koyarwan nan ba, kada ku karɓe shi a gidanku ko ku marabce shi. 11Duk wanda ya karɓe shi yana tarayya da mugun aikinsa ke nan.
12Ina da abubuwa da dama da zan rubuta muku, sai dai ba na so in yi amfani da takarda da inki in rubuta. A maimako, ina fata in ziyarce ku in kuma yi magana da ku fuska da fuska, domin farin cikinmu yă zama cikakke.
13’Ya’yan ’yar’uwarki wadda Allah ya keɓe, suna gaishe ku.