התגלות 7 – HHH & HCB

Habrit Hakhadasha/Haderekh

התגלות 7:1-17

1לאחר מכן ראיתי ארבעה מלאכים עומדים בארבע פינות הארץ ועוצרים את משב ארבע רוחות הארץ, כדי שלא תישוב הרוח בים או ביבשה והכול יעמוד דומם. 2ראיתי מלאך אחר עולה מצד מזרח, שם זורחת השמש, ובידו חותם אלוהים חיים. הוא קרא אל ארבעת המלאכים שקיבלו סמכות וכוח לחבל בארץ, בים ובצומח: 3”חכו! אל תחבלו בארץ, בים ובצומח עד שנחתום את עבדי האלוהים על מצחם.“

4שמעתי שמספר החתומים היה 144,000 מכל שבטי ישראל:

512,000 משבט יהודה

12,000 משבט ראובן

12,000 משבט גד

612,000 משבט אשר

12,000 משבט נפתלי

12,000 משבט מנשה

712,000 משבט שמעון

12,000 משבט לוי

12,000 משבט יששכר

812,000 משבט זבולון

12,000 משבט יוסף

12,000 משבט בנימין.

9אחר כך ראיתי אנשים רבים, שלא ניתן למנותם, מכל הארצות, העמים, הגזעים, השבטים והשפות. הם עמדו לפני כיסא־המלכות ולפני השה, לבושים גלימות לבנות ובידיהם כפות תמרים. 10כל ההמון הזה קרא בקול אדיר: ”הישועה לאלוהינו היושב על כיסא־המלכות ולשה!“

11כל המלאכים – אשר עמדו עתה סביב כיסא־המלכות, סביב הזקנים וארבע החיות – נפלו על פניהם לפני הכיסא, השתחוו לאלוהים 12וקראו: ”אמן! כל הכבוד, הברכה, החכמה, התודה, ההדר, הכוח והעוז לאלוהינו לעולם ועד. אמן!“

13אחד מעשרים־וארבעה הזקנים שאל אותי: ”היודע אתה מיהם הלבושים לבן ומאין באו?“

14”אדוני,“ השבתי, ”אתה יודע.“

”אלה הם אנשים שעברו צרות, רדיפות וסבל רב“, הסביר לי הזקן. ”הם רחצו את גלימותיהם והלבינו אותן בדם השה. 15לכן הם נמצאים כאן לפני כיסא אלוהים; הם משרתים את אלוהים במקדשו יומם ולילה, והוא מגן עליהם, 16הם לא ירעבו ולא יצמאו יותר לעולם, ואף השמש והשרב לא יכו אותם. 17כי השה העומד לפני כיסא־המלכות ירעה אותם ויובילם למעיינות מים חיים, ואלוהים ימחה כל דמעה מעיניהם.“

Hausa Contemporary Bible

Ruʼuya ta Yohanna 7:1-17

An yi wa 144,000 hatimi

1Bayan wannan, na ga mala’iku huɗu, a tsaye a kusurwoyi huɗu na duniya, suna tsare iskoki huɗu na duniya, domin su hana wani iska hurawa a bisan ƙasa ko a bisan teku ko a bisa wani itace. 2Sai na ga wani mala’ika yana zuwa daga gabas, yana da hatimin Allah mai rai. Ya yi kira da babbar murya wa mala’ikun nan huɗu da aka ba su iko su cuci ƙasa da teku ya ce, 3“Kada ku cuci ƙasa ko teku ko kuma itatuwa sai bayan mun sa hatimi a goshin dukan bayin Allahnmu.” 4Sai na ji yawan waɗanda aka sa musu hatimi. Su 144,000 daga dukan kabilan Isra’ila.

5Daga kabilar Yahuda mutum 12,000 ne aka sa musu hatimin,

daga kabilar Ruben mutum 12,000,

daga kabilar Gad mutum 12,000,

6daga kabilar Asher mutum 12,000,

daga kabilar Naftali mutum 12,000,

daga kabilar Manasse mutum 12,000,

7daga kabilar Simeyon mutum 12,000,

daga kabilar Lawi mutum 12,000,

daga kabilar Issakar mutum 12,000,

8daga kabilar Zebulun mutum 12,000,

daga kabilar Yusuf mutum 12,000,

daga kabilar Benyamin mutum 12,000.

Babban taro sanye da fararen tufafi

9Bayan wannan sai na duba, can a gabana kuwa ga wani taro mai girma, wanda ba mai iya ƙirgawa, daga kowace al’umma, kabila, mutane da kuma harshe, suna tsaye a gaban kursiyin da kuma gaban Ɗan Ragon nan. Suna saye da fararen tufafi suna kuma riƙe da rassan dabino a hannuwansu. 10Suka tā da murya da ƙarfi suna cewa,

“Ceto na Allahnmu ne,

wanda yake zaune a bisan kursiyi,

da kuma na Ɗan Ragon.”

11Dukan mala’iku suna tsaye kewaye da kursiyin da kuma kewaye da dattawan tare da halittu huɗun nan masu rai. Suka fāɗi da fuskokinsu ƙasa a gaban kursiyin suka kuma yi wa Allah sujada, 12suna cewa,

“Amin!

Yabo da ɗaukaka,

da hikima da godiya da girma

da iko da ƙarfi

sun tabbata ga Allahnmu har abada abadin.

Amin!”

13Sai ɗaya daga cikin dattawan ya tambaye ni ya ce, “Waɗannan da suke saye da fararen tufafi su wane ne, daga ina kuma suka fito?”

14Na amsa na ce, “Ranka yă daɗe, kai ka sani.”

Sai ya ce, “Waɗannan su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala; sun wanke tufafinsu suka kuma mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan. 15Saboda haka,

“suna a gaban kursiyin Allah

suna masa hidima dare da rana a cikin haikalinsa;

kuma wannan mai zaune a kursiyin zai shimfiɗa tentinsa a bisansu.

16‘Ba za su sāke jin yunwa ba;

ba za su kuma sāke jin ƙishirwa ba.

Rana ba za tă buga su ba,’

ko kuma kowane irin zafin ƙuna.

17Gama Ɗan Ragon da yake a tsakiyar kursiyin zai zama makiyayinsu;

‘zai bi da su zuwa ga maɓulɓular ruwan rai.’

‘Allah kuwa zai share dukan hawaye daga idanunsu.’ ”