הבשורה על-פי מתי 7 – HHH & HCB

Habrit Hakhadasha/Haderekh

הבשורה על-פי מתי 7:1-29

1”אל תשפטו אחרים, ולא ישפטו אתכם. 2כי יתייחסו אליכם לפי איך שאתם מתייחסים לאחרים. ישפטו אתכם במידה שאתם שופטים אחרים. 3כיצד יכול אתה לראות שביב־עץ קטן בעין חברך, ולא להבחין בקרש הגדול שבעינך?

4”איך אתה יכול לומר לחברך: ’תן לי לסלק את השביב מעינך‘ בזמן שבעינך יש קרש כזה גדול? הרי כלל לא תוכל לראות את השביב! 5צבוע שכמותך! סלק תחילה את הקרש מעינך, ורק לאחר מכן תוכל לסלק את שביב העץ מעין חברך!

6”אל תתנו דברים קדושים לאנשים מושחתים, אל תתנו פנינים לחזירים. הם ירמסו את הפנינים, ולאחר מכן יפנו לתקוף אתכם.

7”אם תבקשו – תקבלו; אם תחפשו – תמצאו; ואם תדפקו תיפתח לפניכם הדלת. 8כי כל המבקש מקבל, כל המחפש מוצא, ולפני כל דופק נפתחת הדלת. 9אם ילד מבקש מאביו פרוסת לחם, האם האב ייתן לו אבן במקום לחם? 10אם הילד מבקש דג, האם אתם חושבים שיקבל נחש? 11ואם אנשים רעים וחוטאים כמוכם נותנים לילדיכם מתנות טובות, האם לא ייתן אביכם שבשמים מתנות הרבה יותר טובות למבקשים ממנו?

12”עשו לאחרים את מה שהייתם רוצים שיעשו לכם – זאת תמצית התורה ודברי הנביאים.

13”הלכו דרך הפתח הצר, כי השביל המוביל לאבדון הוא רחב, ושער הכניסה רחב גם הוא. 14אולם שער החיים הוא קטן, השביל צר, ורק מעטים מוצאים אותו.

15”היזהרו לכם מהמורים המפיצים תורות שקר. הם מתחפשים לכבשים תמימים, בעוד שלמעשה הם זאבים רעים הרוצים לטרוף אתכם. 16תוכלו לזהות אותם על־פי התנהגותם, כשם שאפשר לזהות עץ על־פי פירותיו. הלא יודעים אתם להבחין בין גפן ענבים לבין ברקנים, בין תאנים לבין קוצים! 17עץ משובח נותן פרי משובח, ועץ רקוב נותן פרי רקוב. 18עץ טוב לא ייתן פרי רקוב, ועץ רקוב לא ייתן פרי טוב. 19משום כך יש לכרות ולשרוף כל עץ שאינו נותן פרי טוב. 20אכן, גם עצים וגם בני־אדם אפשר לזהות על־פי פירותיהם.

21”לא כל מי שמדבר כאיש דתי ואדוק הוא באמת מאמין. הם יכולים לקרוא לי: ’אדוני, אדוני‘, אבל אין זה מספיק כדי להכניסם לשמים. החשוב הוא אם הם שומעים לקול אבי שבשמים. 22ביום־הדין יאמרו לי אנשים רבים: ’אדון, אדון, הלא בשמך ניבאנו, ובשמך גירשנו שדים וחוללנו נסים רבים‘. 23אולם אני אענה: ’מעולם לא הכרתי אתכם. הסתלקו מכאן, פושעים שכמותכם!‘

24”כל מי שמקשיב לדברי ומקיים אותם, דומה לאדם חכם הבונה את ביתו על סלע איתן. 25שכן גם אם ירד גשם שוטף ותתחולל סערה, לא ייפול הבית ולא יתמוטט, כי נבנה על הסלע. 26לעומתו, מי שמקשיב לדברי ואינו מקיים אותו דומה לאדם טיפש הבונה את ביתו על החול. 27שהרי בבוא שיטפון וסערה יתמוטט הבית וייהרס כליל.“

28ההמונים נדהמו מאוד כששמעו את הדרשות של ישוע, 29כי הוא דיבר אליהם בסמכות רבה ולא כמו הסופרים.

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 7:1-29

Ɗora wa waɗansu laifi

(Luka 6.37,38,41,42)

1“Kada ku ba wa kowa laifi, don kada a ba ku laifi ku ma. 2Gama da irin shari’ar da kuka yi wa waɗansu, da ita za a shari’anta ku. Mudun da kuka yi awo da shi, da shi za a yi muku.

3“Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido? 4Yaya za ka ce wa ɗan’uwanka, ‘Bari in cire maka ɗan tsinken nan daga idonka,’ alhali kuwa a kowane lokaci akwai gungume a naka ido? 5Kai munafuki, fara cire gungumen da yake idonka, a sa’an nan ne za ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake a idon ɗan’uwanka.

6“Kada ku ba karnuka abin da yake mai tsarki; kada kuma ku jefa wa aladu lu’ulu’anku. In kuka yi haka za su tattake su, sa’an nan su juyo su jijji muku ciwo.

Roƙa, nema, ƙwanƙwasa

(Luka 11.9-13)

7“Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. 8Gama duk wanda ya roƙa, akan ba shi; wanda ya nema kuwa, yakan samu, wanda kuma ya ƙwanƙwasa, za a buɗe masa ƙofa.

9“Wane ne a cikinku in ɗansa ya roƙe shi burodi, sai yă ba shi dutse? 10Ko kuwa in ya roƙe shi kifi, sai yă ba shi maciji? 11In ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba da kyautai masu kyau ga ’ya’yanku, balle Ubanku na sama, ba zai fi ku iya ba da abubuwa masu kyau, ga su waɗanda suka roƙe shi ba! 12Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.

Matsattsiya da faɗaɗɗiyar ƙofa

(Luka 13.24)

13“Ku shiga ta matsattsiyar ƙofa. Gama ƙofar zuwa hallaka faɗaɗɗiya ce mai sauƙin bi kuma, masu shiga ta cikinta kuwa suna da yawa. 14Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce matsattsiya kuma, masu samunta kuwa kaɗan ne.

Itace da ’ya’yansa

(Luka 6.43-45)

15“Ku yi hankali da annabawan ƙarya. Sukan zo muku da kamannin tumaki, amma daga ciki mugayen kyarketai ne. 16Ta wurin aikinsu za ku gane su. Mutane suna iya tsinkan inabi a jikin ƙaya, ko kuwa ɓaure a jikin sarƙaƙƙiya? 17Haka ma kowane itace mai kyau yakan ba da ’ya’ya masu kyau, kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 18Itace mai kyau ba ya ba da munanan ’ya’ya, haka kuma mummunan itace ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. 19Duk itacen da ba ya ba da ’ya’ya masu kyau sai a sare shi a jefa cikin wuta. 20Ta haka, ta wurin aikinsu za ku gane su.”

(Luka 13.26,27)

21“Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama. 22Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’ 23Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’

Magini mai hikima da marar hikima

(Luka 6.47-49)

24“Saboda haka duk wanda yake jin kalmomin nan nawa yake kuma aikata su, yana kama da mutum mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse. 25Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuma ta hura ta bugi gidan; duk da haka bai fāɗi ba, gama yana da harsashinsa a kan dutse. 26Amma duk wanda yake jin kalmomin nan nawa bai kuwa aikata su ba, yana kama da wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi. 27Ruwan sama ya sauko, rafuffuka suka cika, iska kuwa ta hura ta bugi gidan, sai ya fāɗi da mummunar ragargajewa kuwa.”

28Sa’ad da Yesu ya gama faɗin waɗannan abubuwa, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa, 29domin ya koyar kamar wani wanda yake da iko, ba kamar malamansu na dokoki ba.