הבשורה על-פי יוחנן 10 – HHH & HCB

Habrit Hakhadasha/Haderekh

הבשורה על-פי יוחנן 10:1-42

1”אני אומר לכם באמת,“ המשיך ישוע, ”מי שמסרב להיכנס למכלאת הצאן דרך השער, ובוחר להיכנס בדרך הצדדית, הוא גנב או שודד. 2האדם שנכנס דרך השער הוא רועה הצאן. 3השומר יפתח לו את השער, עדר הצאן ישמע ויכיר את קולו, והרועה יוביל את הצאן החוצה כשהוא נוקב בשם כל כבשה. 4הרועה הולך בראש והעדר נוהר אחריו, כי הוא מזהה את הרועה ומכיר את קולו. 5הצאן לא תלכנה אחרי אדם זר, אלא תברחנה מפניו, כי קולו אינו מוכר להן.“

6אלה ששמעו משל זה מפי ישוע לא הבינו למה התכוון, 7ולכן ישוע הסביר להם: ”אמן אני אומר לכם: אני השער של מכלאת הצאן. 8כל אלה שבאו לפני היו גנבים ושודדים, אולם הצאן לא שמעו בקולם. 9כן, אנוכי השער. הנכנסים דרכי יוושעו וימצאו מרעה עשיר בבואם ובצאתם. 10הגנב בא לגנוב, להרוג ולהשמיד, ואילו אני באתי להעניק חיים בשפע.

11”אני הרועה הטוב, ורועה טוב מקריב את חייו למען צאנו. 12כאשר רועה שכיר יראה זאב מתקרב, הוא יברח ויעזוב את הצאן לאנחות, כי העדר אינו שייך לו, והזאב יחטוף ויפזר את הצאן. 13הרועה השכיר יברח, משום שאינו אלא שכיר ואין הוא דואג לצאן באמת.

14”אני הרועה הטוב; אני מכיר את צאני והן מכירות אותי, 15כשם שאבי מכיר אותי ואני מכיר את אבי; ואני מקריב את חיי למען הצאן. 16יש לי עדר נוסף שאינו מהמכלאה הזאת. עלי להנהיג גם אותו, והצאן שומעות בקולי; כך יהיה עדר אחד ורועה אחד.

17”אבי אוהב אותי משום שאני מקריב את חיי כדי שאקבל אותם חזרה. 18איש אינו יכול להרוג אותי ללא הסכמתי. אני מקריב את חיי מרצוני, מפני שיש לי זכות וכוח להקריב את חיי כשאני רוצה בכך, ואף זכות וכוח להשיבם לעצמי. אלוהים הוא המעניק לי זכות זאת.“

19דבריו אלה שוב גרמו למחלוקת בין מנהיגי היהודים. 20חלקם אמר: ”או שהוא יצא מדעתו, או שנכנס בו שד! מדוע אתם מקשיבים לו?“

21אחרים אמרו: ”הוא אינו נשמע כמי שנכנס בו שד. האם שד יכול לפקוח עיני עיוורים?“

22בחג החנוכה, בחורף, 23התהלך ישוע בבית־המקדש באגף הנקרא ”אולם שלמה“. 24היהודים הקיפוהו מכל עבר ושאלו: ”עד מתי בכוונתך לסקרן אותנו? אם אתה הוא המשיח, מדוע אינך אומר זאת בפירוש?“

25”כבר אמרתי לכם, אבל לא האמנתם לי“, השיב ישוע. ”המעשים שאני עושה בשם אבי מאשרים זאת. 26אולם אינכם מאמינים לי, כי אינכם שייכים לצאני. 27אני מכיר את צאני, צאני מכירות את קולי והן הולכות אחרי. 28אני מעניק להן חיי נצח והן לא תאבדנה. איש לא יחטוף אותן ממני, 29כי אבי נתן לי אותן, והוא חזק וגיבור מכולם. משום כך לא יוכל איש לחטוף אותן ממני. 30אבי ואני אחד אנחנו!“

31שוב החלו מנהיגי היהודים להשליך עליו אבנים.

32”הראיתי לכם הרבה מעשים טובים בשם אבי, איזה מהם גרם לכך שתשליכו עלי אבנים?“ שאל ישוע.

33”איננו משליכים עליך אבנים בגלל המעשים הטובים שעשית, אלא בגלל שאתה מגדף את האלוהים; למרות שאתה אדם, אתה עושה את עצמך לאלוהים!“

34”אך הכתובים שלכם אומרים: ’אלוהים אתם‘,10‏.34 י 34 תהלים פב 6 והכוונה היא לבני־האדם“, השיב ישוע. 35”אם האנשים שאליהם מדברים הכתובים מכונים ’אלוהים‘, והכתוב הוא דבר אמת, 36מדוע קוראים אתם ’מגדף‘ למי שקדשו האב ונשלח לעולם הזה על־ידו, ושטוען כי הוא בן האלוהים? 37אם איני עושה מעשים כפי שעושה אבי, אל תאמינו לי. 38אולם אם אני אכן עושה את מעשי אבי, האמינו לפחות למעשים גם אם אינכם מאמינים לי, ואז תשוכנעו שאבי שוכן בי ואני בו.“

39הם שוב רצו לתפוס את ישוע, אולם הוא התחמק מידיהם. 40ישוע חזר לעבר הירדן, למקום שבו הטביל יוחנן לראשונה. הוא נשאר שם זמן־מה, 41ואנשים רבים הלכו אחריו.

”יוחנן לא חולל נסים,“ אמרו זה לזה, ”אולם כל מה שאמר על האיש הזה היה אמת.“ 42אנשים רבים במקום ההוא האמינו כי ישוע באמת המשיח.

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 10:1-42

Makiyayi da garkensa

1“Gaskiya nake gaya muku, mutumin da bai shiga inda ake ajiye garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya hau ta katanga, ɓarawo ne, ɗan fashi kuma. 2Mutumin da ya shiga ta ƙofa makiyayin tumakinsa ne. 3Mai gadin yakan buɗe wa makiyayin ƙofa, tumakin kuma sukan saurari muryarsa. Yakan kira tumakinsa da suna, yă kuma fid da su waje. 4Sa’ad da ya fitar da dukan nasa waje, sai ya ja gabansu, tumakinsa kuma sukan bi shi domin sun san muryarsa. 5Amma ba za su taɓa bin baƙo ba; sai dai ma su guje masa don ba su san muryar baƙo ba.” 6Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su fahimci abin da yake faɗa musu ba.

7Saboda haka Yesu ya sāke cewa, “Gaskiya nake gaya muku, ni ne ƙofar tumakin. 8Duk waɗanda suka riga ni zuwa ɓarayi ne, ’yan fashi kuma, amma tumakin ba su saurare su ba. 9Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo. 10Ɓarawo yakan zo don yă yi sata ne kawai da kisa da kuma ɓarna. Ni kuwa na zo ne don su sami rai, su kuma same shi a yalwace.

11“Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau yakan ba da ransa domin tumakin. 12Wanda aka ɗauko haya ba shi ne makiyayi mai tumakin ba. Saboda haka sa’ad da ya ga kyarkeci yana zuwa, sai yă sheƙa da gudu yă bar tumakin. Sai kyarkecin yă kai wa garken hari, yă kuma watsar da su. 13Mutumin yakan gudu don shi ɗan haya ne kawai, bai kuwa damu da tumakin ba.

14“Ni ne makiyayi mai kyau; na san tumakina, tumakina kuma sun san ni, 15kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uba, ina kuwa ba da raina domin tumakin. 16Ina da waɗansu tumaki da ba na wannan garken ba ne. Dole ne in kawo su su ma. Za su saurari muryata, za su kasance garke guda ɗaya, makiyayi guda kuma. 17Abin da ya sa Ubana yake ƙaunata ke nan, domin ina ba da raina, in ɗauko shi kuma. 18Ba mai karɓe mini rai, ina dai ba da shi. Ina da iko in ba da shi, ina da iko in ɗauko shi kuma. Wannan umarni kuwa daga wurin Ubana na karɓo shi.”

19Saboda waɗannan kalmomi fa, sai ɓaraka ta sāke shiga cikin Yahudawa. 20Da yawa daga cikinsu suka ce, “Yana da aljani, yana kuma hauka. Don me za ku saurare shi?”

21Amma waɗansu suka ce, “Kai, waɗannan kalmomi ba na mai aljani ba ne. Anya, aljani yana iya buɗe idanun makaho?”

Rashin bangaskiyar Yahudawa

22Bikin Miƙawa10.22 Wato, Hanukka a Urushalima ya kewayo, lokacin sanyin hunturu ne kuwa. 23Sai ga Yesu a filin haikali yana zagawa a Shirayin Solomon, 24sai Yahudawa suka taru kewaye da shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In kai ne Kiristin, ka faɗa mana a fili mana.”

25Yesu ya amsa ya ce, “Na faɗa muku, amma ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi cikin sunan Ubana su suke nuna ko wane ne ni. 26Amma ba ku gaskata ba domin ku ba tumakina ba ne. 27Tumakina sukan saurari muryata; na sansu, suna kuma bi na. 28Ina ba su rai madawwami, ba za su taɓa hallaka ba; ba kuma mai ƙwace su daga hannuna. 29Ubana, wanda ya ba ni su, ya fi duka girma, ba mai ƙwace su daga hannun Ubana. 30Da ni da Uba ɗaya ne.”

31Sai Yahudawa suka sāke ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, 32amma Yesu ya ce musu, “Na nuna muku ayyukan alheri masu yawa da Uba ya aiko ni in yi, a kan wanne kuke so ku jajjefe ni?”

33Yahudawa suka amsa suka ce, “Ai, ba don wani daga cikin waɗannan ayyukan alheri ne muke so mu jajjefe ka ba, amma don saɓon da kake yi, kai da kake mutum kawai, kana mai da kanka Allah.”

34Yesu ya amsa musu ya ce, “Ba a rubuce yake a cikin Dokarku ba cewa, ‘Na ce ku alloli ne’10.34 Zab 82.6? 35Mun dai san Nassi ba ya ƙarya, In har ya kira su waɗanda maganar Allah ta zo musu, ‘alloli,’ 36to, game da wanda Uba ya keɓe a matsayin nasa ne ya kuma aiko shi duniya. Don me kuke ce saɓo nake, domin na ce, ‘Ni Ɗan Allah ne?’ 37In ba ayyukan da Ubana yake yi ne nake yi ba, to, kada ku gaskata ni. 38Amma in su nake yi, ko ba ku gaskata ni ba, to, ku gaskata ayyukan, don ku sani, ku kuma gane, Uban yana cikina, ni kuma ina cikin Uban.” 39Sai suka sāke yin ƙoƙari su kama shi, amma ya kuɓuce musu.

40Sa’an nan Yesu ya sāke koma ƙetaren Urdun inda dā Yohanna yake baftisma. A can ya zauna 41mutane da yawa suka zo wurinsa. Suka ce, “Ko da yake Yohanna bai yi wani abin banmamaki ba, duk abubuwan da Yohanna ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.” 42A nan kuwa mutane da yawa suka gaskata da Yesu.