1זוהי הפעם השלישית שאבוא אליכם. הכתובים אומרים שעל־פי שניים או שלושה עדים יקום כל דבר. 2כבר הזהרתי אתכם פעם אחת בביקורי הקודם, ועתה בהעדרי אני חוזר על האזהרה: בשובי אליכם הפעם לא אחוס על אלה שחטאו מקודם ועל כל הראויים לעונש.
3אוכיח לכם מעל כל ספק שהמשיח אכן מדבר באמצעותי. המשיח שבו אתם מאמינים אינו חלש לפניכם, אלא חזק בתוככם! 4המשיח אמנם נצלב בחולשה, אך עתה הוא חי בגבורת אלוהים. כך גם אנחנו חלשים, כשם שהמשיח היה חלש, אך אנו נחיה עמו למענכם בגבורת אלוהים.
5בחנו את עצמכם וראו אם אתם עומדים במבחן: האם אתם באמת מאמינים במשיח? האם אתם מרגישים בקרבכם את נוכחותו וגבורתו? או האם אמונתכם במשיח אינה אלא העמדת פנים? 6אני מקווה שאתם מסכימים אתי שעברתי מבחן זה בהצלחה.
7אני מתפלל לאלוהים שלא תעשו רע – לא כדי להוכיח את הצלחתנו, אלא כדי שתעשו את הטוב גם אם כלפי חוץ ייראה שנכשלנו. 8תפקידנו לעודד את הטוב בכל עת, ולא לקוות לרע.13.8 יג 8 או: כי איננו יכולים לעשות דבר נגד האמת אלא רק בעד האמת.
9אנו תמיד מוכנים להיות חלשים, אם פרוש הדבר שאתם חזקים. משאלתנו ותפילתנו היא שתתבגרו באמונתכם.
10אני כותב לכם עתה מכתב זה בתקווה שלא אצטרך לנזוף בכם או להעניש אתכם בבואי, כי ברצוני להשתמש בסמכות שנתן לי האדון לחזק אתכם ולא להענישכם.
11אני מסיים מכתבי במילים הבאות: שמחו, התבגרו באמונתכם, שימו לב לדברים שאמרתי, חיו באהבה ובשלום. מי ייתן שאלוהי האהבה והשלום יהיה עמכם.
12-13ברכו איש את רעהו לשלום בנשיקה קדושה. כל המאמינים המשיחיים מוסרים לכם דרישת שלום.
14מי ייתן שחסד אדוננו ישוע המשיח, אהבת האלוהים וחברת רוח־הקודש יהיו עם כולכם.
Gargaɗin ƙarshe
1Wannan za tă zama ziyarata ta uku a wurinku ke nan. “Dole a tabbatar da kowace magana ta bakin shaidu biyu ko uku.”13.1 M Sh 19.15 2Na riga na yi muku gargaɗi sa’ad da nake tare da ku a zuwana na biyu. Yanzu da ba na nan tare da ku, ina maimaita irin gargaɗin nan domin in na zo ba wanda zai kuɓuce wa horon nan, 3da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku. 4Ko da yake tabbatacce an gicciye shi cikin rashin ƙarfi, duk da haka, yana rayuwa bisa ga ikon Allah. Haka mu ma marasa ƙarfi ne a cikinsa, amma ta wurin ikon Allah za mu rayu tare da shi don mu yi muku hidima.
5Ku gwada kanku ku gani ko kuna cikin bangaskiya; ku auna kanku. Ashe, ba ku san cewa Kiristi Yesu yana cikinku ba? Sai ko in kun fāɗi gwajin. 6Ina fata za ku gane cewa ba mu fāɗi gwajin ba. 7Muna addu’a ga Allah kada ku aikata wani laifi. Ba don mutane su gani cewa mun ci gwajin ba ne, a’a, sai dai don ku yi abin da yake daidai, ko da yake zai zama kamar mun fāɗi gwajin ne. 8Kai, ba dama mu saɓa wa gaskiya, sai dai mu bi bayan gaskiyar. 9Murna muke sa’ad da ba mu da ƙarfi, ku kuwa kuna da ƙarfi. Addu’armu ita ce, ku zama cikakku. 10Shi ya sa nake rubuta waɗannan abubuwa, sa’ad da ba na nan tare da ku, domin sa’ad da na zo, kada yă zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
Gaisuwa ta ƙarshe
11A ƙarshe ’yan’uwa, sai wata rana. Ku yi ƙoƙari ku zama cikakku. Ku saurari roƙona, ku zama da tunani ɗaya, ku yi zaman salama. Allah na ƙauna da salama kuwa zai kasance tare da ku.
12Ku gaggai da juna da sumba mai tsarki.
13Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
14Alherin Ubangiji Yesu Kiristi, da ƙaunar Allah, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki su kasance tare da ku duka.