אגרת פולוס השליח אל האפסיים 3 – HHH & HCB

Habrit Hakhadasha/Haderekh

אגרת פולוס השליח אל האפסיים 3:1-21

1אני, פולוס, עבד ישוע המשיח, נמצא כאן בבית־הסוהר בגללכם. 2‏-3אתם ודאי יודעים שאלוהים הטיל עלי את המשימה המיוחדת להראות לכם, הגויים, את חסדו, כפי שכבר ציינתי בקצרה באחד ממכתבי. אלוהים עצמו גילה לי את תוכניתו הסודית האומרת שגם הגויים כלולים בחסדו זה.

4אני מספר לכם את כל זאת כדי שתבינו כיצד אני יודע את סוד המשיח. 5בדורות הראשונים הסתיר אלוהים מעמו את הסוד הזה, אך עתה גילהו לשליחיו ונביאיו באמצעות רוח הקודש.

6זהו הסוד: על־ידי הבשורה היהודים והגויים הם יורשים שווים של העושר המיועד לבני־האלוהים; הם חברים שווי־זכויות בקהילת האלוהים, ושותפים בהבטחותיו שניתנו על־ידי המשיח לכל המאמינים בו (במשיח). 7אלוהים העניק לי את הזכות הנפלאה לספר לכולם על אודות תוכניתו זאת, ונתן לי את הכישרון והיכולת לעשות זאת כהלכה. 8אכן, לי, הצעיר מכל המאמינים, העניק אלוהים את הזכות והחסד לבשר לגויים את הבשורה של עושר המשיח – עושר שהוא מעל ומעבר לכושר הבנתנו – 9ולהסביר לכל האנשים שאלוהים הוא גם מושיעם של הגויים, כפי שבורא־הכול תכנן מבראשית. 10מדוע? כדי שכל הכוחות, השרים והשליטים אשר בשמים יראו את חכמתו הנפלאה של אלוהים, וכל בני־משפחתו, יהודים וגויים, ייראו מאוחדים בקהילתו, 11בדרך שבה תמיד תכנן זאת על־ידי ישוע המשיח אדוננו.

12עתה אנו יכולים לבוא ישר אל נוכח האלוהים, ללא חשש ובטוחים שישמח לבואנו, בזכות אמונתנו בישוע המשיח.

13לפיכך אל תדאגו על סבלי למענכם אלא התעודדו והתגאו בכך! 14בחשבי על תוכנית נפלאה זאת אני כורע ברך לפני האלוהים, אבי אדוננו ישוע המשיח, 15אשר על שמו נקראו כל המשפחות בארץ ובשמים, 16ואני מתפלל שבאמצעות רוח הקודש הוא יעניק לכם כוח וגבורה פנימיים מתוך אוצרו הנהדר והאין־סופי. 17אני מתפלל שהמשיח באמת ישכון בלבבכם על־ידי אמונתכם ושתתחזקו באהבה, 18כדי שתוכלו לתפוש ולהבין, יחד עם שאר המאמינים, עד כמה עצומה, רבה, עמוקה וחובקת היא אהבת המשיח, 19וכדי שתתנסו בעצמכם באהבה נפלאה זאת, שהיא מעל ומעבר להבנתנו. וכך תימלאו כולכם באלוהים עצמו.

20אלוהים יכול להרבות את חסדו אלינו, ולפעול בנו מעל ומעבר למה שאנו מסוגלים לתאר או לבקש. 21כל הכבוד והתהילה לאלוהים בקרב המאמינים ובישוע המשיח, לדור ודור עד עולם.

Hausa Contemporary Bible

Afisawa 3:1-21

Kyakkyawan shirin Allah domin al’ummai

1Saboda haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Al’ummai.

2Na tabbata kun ji labarin hidimar alheri na musamman da Allah ya ba ni dominku. 3Wannan wasiƙa za tă faɗa muku kaɗan game da yadda Allah ya bayyana mini shirinsa na asiri. 4A yayinda kuke karanta wannan, za ku gane abin da na sani game da wannan shirin Kiristi. 5Ba a sanar da wannan asiri wa wani a sauran zamanai ba, amma a yanzu an bayyana shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzanninsa da annabawansa. 6Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Al’ummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Isra’ila, sun zama gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.

7Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina. 8Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali. 9An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru. 10Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar da hikima iri dabam-dabam na Allah ga masu mulki, da masu iko a samaniya. 11Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu. 12A cikinsa, kuma ta wurin bangaskiya a cikinsa ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagadi. 13Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

Addu’a saboda Afisawa

14Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba, 15wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna. 16Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa. 17Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna, 18don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take. 19Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.

20Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani. 21Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yă zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin.