1ביקשתם ממני להגיב לרעיון: מוטב לאיש להימנע מיחסים עם אשתו. 2אך משום הזנות והתאווה הרובצות בסביבה, כדאי לאיש ולאישה לקיים יחסים ביחד. 3על הבעל לתת לאשתו את כל הזכויות המגיעות לה כאישה נשואה, ועל האישה לתת אותן זכויות לבעלה. 4כי לאישה נשואה אין כבר זכות בלעדית על גופה – גם לבעלה יש זכות על גופה, ואף לבעל כבר אין זכות בלעדית על גופו, כי גופו שייך גם לאשתו. 5לכן אל תמנעו את עצמכם זה מזו, אלא אם שניכם החלטתם להימנע מקיום יחסי־מין למשך זמן מוגבל, כדי שתוכלו להקדיש את עצמכם לתפילה. במקרה כזה, מיד עם תום הזמן המוגבל עליכם לשוב ולקיים יחסים כמו מקודם, כדי שהשטן לא יוכל לפתות אתכם על־ידי תשוקתכם שלא באה על סיפוקה. 6אני אומר זאת בדרך של רשות, ולא בדרך של פקודה. 7מצדי, הלוואי שכולם יכולתם לחיות ללא נשואים, כמוני. אולם אנו שונים מאוד איש מרעהו. לאחד נותן אלוהים אישה במתנה, ולשני הוא נותן במתנה את היכולת להישאר רווק(ה) ומאושר(ת).
8אני פונה אל הרווקים ואל האלמנות: אם אתם יכולים, מוטב שלא תינשאו, כמוני. 9אבל אם אינכם יכולים לשלוט ביצריכם – הינשאו! כי מוטב להינשא מאשר לסבול מתשוקה מינית שאינה באה על סיפוקה.
10על הנשואים אני מצווה בשם ישוע המשיח ובפקודתו: אסור לאישה לעזוב את בעלה. 11אם היא מעדיפה להיפרד מבעלה אסור לה להינשא לאחר, אבל מותר לה לחזור לבעלה הראשון. גם לבעל אסור לגרש את אשתו.
12ברצוני להוסיף כמה הצעות משלי. אין אלה מצוות ישירות מהאדון, אך הן נראות צודקות בעיני: אם מאמין משיחי כבר נשוי לאישה שאינה מאמינה, וברצונה להמשיך לחיות איתו, אסור לו לעזוב את אשתו או לגרשה. 13אם מאמינה משיחית נשואה לבעל שאינו מאמין, וברצונו להמשיך לחיות איתה, אסור לה לעזוב אותו. 14כי האישה המאמינה מביאה קדושה לנישואין, והבעל המאמין מביא איתו קדושה לנישואין. אחרת, ילדיכם לא היו קדושים, אך כעת הם קדושים.
15אולם אם הבעל או האישה שאינם מאמינים רוצים להיפרד – מותר לכם להיפרד מהם. במקרה כזה, בן הזוג המאמין אינו צריך לדרוש מהשני להישאר, כי אלוהים רוצה שילדיו יחיו בשלום. 16אחרי הכול, מנין לכן לדעת אם בעליכן יבואו לידי אמונה או לא? ואותו הדבר אמור לגבי הבעלים המאמינים ונשותיהם.
17החשוב הוא שכל אחד ישמח בחלקו ויהיה מרוצה במצב שאלוהים בחר עבורו – נשוי או לא נשוי. זוהי מצוותי לכל הקהילות.
18מי שנימול לפני בואו לאמונה לא צריך להתחרט על כך; מי שלא נימול לפני בואו לאמונה, לא צריך לעשות עכשיו ברית־מילה. 19כי המילה אינה חשובה. החשוב הוא לשמור את מצוות האלוהים.
20בדרך כלל על כל אחד להישאר באותו מעמד שבו היה כשבא לידי האמונה. 21האם אתה עבד? אל תתלונן. אך אם יש לך הזדמנות לצאת לחופשי – אל תחמיץ אותה! 22אם אתה עבד והאדון קורא לך, אל תשכח שהמשיח שיחרר אותך מהשעבוד לחטא; אם האדון קורא לך ואתה בן־חורין, אל תשכח שהמשיח שיחרר אותך משעבוד לחטא; אם האדון קורא לך ואתה בן־חורין, אל תשכח שמעתה הינך עבד המשיח. 23אתם שייכים למשיח, כי הוא קנה אתכם במחיר יקר, ומשום כך אל תשתעבדו לבני־אדם. 24כן, אחים יקרים, לא משנה באיזה מצב הייתם או באיזו משרה עבדתם, כאשר האדון קורא לכם; הישארו במקומכם, כי עכשיו האדון אתכם לחזקכם ולעזור לכם.
25בתשובה לשאלתכם השנייה, האם מותר לבתולות להינשא? אין לי הוראה מיוחדת מהאדון. אך מאחר שהעניק לי מתבונתו והוא סומך עלי, אשמח לחוות את דעתי. 26בשל הבעיות והצרות הבאות עלינו אני חושב כי מוטב לא להינשא. 27מובן שהנשואים אינם צריכים להתגרש מסיבה זו, אך מי שטרם נישא – שלא ימהר עכשיו. 28אם הגברים רוצים בכל זאת להינשא עכשיו, מותר להם; ואם הבחורות רוצות להינשא עתה – אין זה חטא! העניין הוא שהנשואים גורמים לבעיות נוספות, ואישית, הייתי רוצה למנוע מכם כעת בעיות אלה.
29עלינו לזכור תמיד שזמננו עלי אדמות קצר מאוד. לכן על הגברים הנשואים להיות חופשיים למען האדון, כאילו שאינם נשואים כלל. 30אסור שאושר, נכסים או צער ימנעו בעד איש מלשרת את האדון. 31על העוסקים בענייני העולם להיזהר שלא לשקוע בו עמוק מדי, כי צורת הדברים בעולם משתנה במהירות.
32ברצוני שתהיו חופשיים מדאגה בכל מעשיכם. הרווק יכול לבלות את חייו בעבודת האדון ובמאמץ למצוא־חן בעיניו, 33בעוד שגבר נשוי דואג תחילה למלא את חובתו לאשתו, ואין הוא יכול להקדיש את עצמו לאדון כראוי; תשומת לבו מחולקת. 34גם לאישה הנשואה יש את אותן הבעיות. הרווקה משתדלת למצוא־חן בעיני האדון בכל מעשיה, ושומרת על טוהר גופה ורוחה; ואילו האישה הנשואה טרודה בבעיות משק הבית, ועליה לשרת את בעלה ולהשתדל למצוא־חן בעיניו.
35איני מנסה למנוע בעדכם מלהינשא; אני מנסה לעזור לכם. הייתי רוצה שתבחרו בדרך הטובה והיעילה ביותר לשרת את האדון.
36אם מישהו אינו יכול להתגבר על תשוקתו והוא מרגיש צורך להינשא, מותר לו – אין זה חטא. 37אך מי שיש לו כוח לא להינשא ומחליט שאין לו צורך בנשואים, החליט החלטה נבונה מאוד. 38מסקנה: טוב להינשא, אך טוב יותר לא להינשא.
39האישה קשורה לבעלה כל עוד הוא חי; אם בעלה נפטר היא רשאית להינשא שנית – אבל רק למאמין משיחי! 40אך לדעתי היא תהיה מאושרת יותר אם לא תינשא בשנית, וחושבני שאין זו דעתי בלבד, אלא גם רצון רוח הקודש השוכן בי.
Aure
1To, game da zancen da kuka rubuto. Yana da kyau mutum yă zauna ba aure.7.1 Ko kuwa “Ya fi kyau kada mutum yă yi jima’i da mace.” 2Amma da yake fasikanci ya yi yawa, ya kamata kowane mutum yă kasance da matarsa, kowace mace kuma da mijinta. 3Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta. 4Jikin matar ba nata ne kaɗai ba, amma na mijinta ne ma. Haka ma jikin mijin, ba na shi ne kaɗai ba, amma na matarsa ne ma. 5Kada ku ƙi kwana da juna sai ko kun yarda a junanku kuma na ɗan lokaci, don ku himmantu ga addu’a. Sa’an nan ku sāke haɗuwa don kada Shaiɗan yă jarrabce ku saboda rashin ƙamewarku. 6Wannan fa shawara ce nake ba ku, ba umarni ba. 7Da ma a ce dukan maza kamar ni suke mana. Sai dai kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa; wani yana da wannan baiwa, wani kuwa wancan.
8To, ga marasa aure da gwauraye kuwa ina cewa yana da kyau su zauna haka ba aure, yadda nake. 9Sai dai in ba za su iya ƙame kansu ba, to, su yi aure, don yă fi kyau a yi aure, da sha’awa ta sha kan mutum.
10Ga waɗanda suke da aure kuwa ina ba da wannan umarni (ba ni ba, amma Ubangiji) cewa kada mace ta rabu da mijinta. 11In kuwa ta rabu da shi, sai ta kasance ba aure, ko kuma ta sāke shiryawa da mijinta. Kada miji kuma yă saki matarsa.
12Ga sauran kuwa (ni ne fa na ce ba Ubangiji ba), in wani ɗan’uwa yana da mata wadda ba mai bi ba ce, kuma tana so ta zauna tare da shi, kada yă sake ta. 13In kuma mace tana da miji wanda ba mai bi ba ne, kuma yana so yă zauna tare da ita, kada tă kashe auren. 14Don miji marar ba da gaskiya an tsarkake shi ta wurin matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma an tsarkake ta ta wurin mijinta. In ba haka ba ’ya’yanku ba za su zama da tsarki ba, amma kamar yadda yake, su masu tsarki ne.
15Amma in marar bi ɗin ya raba auren, a ƙyale shi. A irin wannan hali, babu tilas a kan wani, ko wata mai bi. Allah ya kira mu ga zaman lafiya ne. 16Ke mace, kin sani ne, ko ke ce za ki ceci mijinki? Kai miji, ka sani ne, ko kai ne za ka ceci matarka?
17Duk da haka, sai kowa yă kasance a rayuwar da Ubangiji ya sa shi da kuma wanda Allah ya kira shi. Umarnin da na kafa a dukan ikkilisiyoyi ke nan. 18In an riga an yi wa mutum kaciya sa’ad da aka kira shi, to, kada yă zama marar kaciya. In an kira mutum sa’ad da yake marar kaciya, to, kada a yi masa kaciya. 19Kaciya ba wani abu ba ne, rashin kaciya kuma ba wani abu ba ne. Kiyaye umarnin Allah shi ne muhimmin abu. 20Ya kamata kowa yă kasance a matsayin da yake ciki sa’ad da Allah ya kira shi.
21Kai bawa ne sa’ad da aka kira ka? Kada wannan yă dame ka, sai dai in kana iya samun ’yanci, sai ka yi amfani da wannan dama. 22Gama wanda yake bawa sa’ad da Ubangiji ya kira shi, ’yantacce ne na Ubangiji; haka ma, wanda yake ’yantacce sa’ad da aka kira shi, bawa ne na Kiristi. 23Da tsada fa aka saye ku, kada ku zama bayin mutane. 24’Yan’uwa, a duk matsayin da mutum yake sa’ad da aka kira shi, sai yă kasance haka a sabuwar dangantakarsa da Allah.
25To, game da budurwai. Ba ni da wani umarni daga Ubangiji, sai dai na yanke hukunci a matsayi wanda yake amintacce ta wurin jinƙan Ubangiji. 26Saboda ƙuncin rayuwar da ake ciki, ina gani ya fi kyau ku kasance yadda kuke. 27In kuna da aure, kada ku nemi kashe auren. In ba ku da aure, kada ku nemi yin aure. 28Amma idan ka riga ka yi aure, to, ba laifi, ba zunubi ba ne, kuma idan yarinya7.28 yarinya. Da Girik an rubuta “budurwa” ne nan ta yi aure, ba tă yi laifi ba. Sai dai waɗanda suka yi aure za su fuskanci damuwoyi masu yawa a cikin rayuwa, ni kuwa ina so in fisshe su daga wannan.
29’Yan’uwa, abin da nake nufi shi ne, lokaci ya rage kaɗan. Daga yanzu, waɗanda suke da mata ya kamata su yi rayuwa kamar ba su da su; 30waɗanda suke kuka kuma kamar ba kuka suke yi ba, waɗanda suke farin ciki kuwa kamar ba farin ciki suke yi ba. Waɗanda suka sayi abu su yi kamar ba nasu ba ne; 31masu amfani da kayan duniya kuwa, kada su duƙufa a cikinsu. Gama duniyan nan a yadda take mai shuɗewa ce.
32Zan so ku ’yantu daga damuwa. Mutum marar aure ya damu ne da al’amuran Ubangiji, yadda zai gamshi Ubangiji. 33Amma mutumin da yake da aure yakan damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda zai gamshi matarsa 34hankalinsa a rabe yake. Mace marar aure ko kuwa budurwa ta damu ne da al’amuran Ubangiji. Nufinta shi ne ta ba da kanta ga Ubangiji cikin jiki da ruhu. Amma mace da take da aure ta damu ne da al’amuran wannan duniya, yadda za tă gamshi mijinta. 35Na faɗa haka don amfaninku ne, ba don in ƙuntata muku ba. Sai dai don ku yi rayuwa a hanyar da ta dace da nufin ku himmantu ga bautar Ubangiji ba da raba hankali ba.
36In mutum ya ga cewa ba ya nuna halin da ya kamata ga budurwar da ya yi alkawarin aure da ita, in kuma shekarunta suna wucewa, shi kuma ya ga ya kamata yă yi aure, to, sai yă yi. Ba zunubi ba ne. Ya kamata su yi aure. 37Amma mutumin da ya riga ya yanke shawara a ransa, wanda kuma ba lalle ba ne amma yana iya shan kan nufinsa, kuma ya riga ya zartar a zuciyarsa ba zai auri budurwar ba, wannan mutum ma ya yi abin da ya dace. 38Don haka, wanda ya auri budurwar ya yi daidai, amma wanda bai aure ta ba ya ma fi.7.36-38 Ko kuwa 36 In wani yana tsammani cewa ba ya yin wa ’yarsa abin da ya dace, in kuma shekarunta suna ƙaruwa, ya kuwa ji ya kamata tă yi aure, sai yă yi yadda ya ga ya dace. Bai yi zunubi ba. Ya kamata yă bar ta tă yi aure. 37 Amma mutumin da ya warware batun a zuciyarsa, wanda ba ya ƙarƙashin tilas amma yana iya sarrafa nufinsa, wanda kuma ya yanke shawara yă bar budurwarsa ba aure, wannan mutum ma ya yi abin da yake daidai. 38 Saboda haka, wanda ya ba da budurwarsa a aure ya yi daidai, amma wanda bai ba da ita ga aure ba ya ma yi abin da ya fi.
39Mace tana haɗe da mijinta muddin yana da rai. Amma in mijinta ya mutu, tana da ’yanci ta auri wanda take so. Amma fa, sai mai bin Ubangiji. 40A nawa ra’ayi, za tă fi jin daɗi in ta zauna haka, a ganina kuwa ina ba ku shawara ce daga Ruhun Allah da na ce haka.