Yohanna 2 – Hausa Contemporary Bible HCB

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 2:1-25

Yesu ya mai da ruwa ya zama ruwan inabi

1A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta Galili. Mahaifiyar Yesu kuwa tana can, 2aka gayyaci Yesu da almajiransa su ma a auren. 3Da ruwan inabi ya ƙare, sai mahaifiyar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.”

4Yesu ya ce, “Mace, me ya sa kike haɗa ni a wannan? Lokacina bai yi ba tukuna.”

5Sai mahaifiyarsa ta ce wa bayin, “Ku yi duk abin da ya faɗa.”

6Nan kusa kuwa akwai tulunan ruwa shida na dutse a ajiye, irin da Yahudawa suke amfani da su don tsarkakewa bisa ga al’ada, kowace kan ci gallon kusan ashirin zuwa talatin.

7Sai Yesu ya ce wa bayin, “Ku ciccika tulunan da ruwa.” Suka kuwa ciccika su fal.

8Sa’an nan ya ce musu, “Yanzu ku ɗiba ku kai wa uban bikin.”

Suka yi haka. 9Uban bikin kuwa ya ɗanɗana ruwan da aka juya ya zama ruwan inabi. Bai san daga ina ya fito ba, ko da yake bayin da suka ɗiba ruwan sun sani. Sai ya kira angon waje ɗaya 10ya ce, “Kowa yakan kawo ruwan inabi mafi kyau da fari, sa’an nan marar kyan bayan baƙin sun sha da yawa; amma ka ajiye ruwan inabi mafi kyau sai yanzu.”

11Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.

Yesu ya tsabtacce haikali

12Bayan wannan sai ya tafi Kafarnahum tare da mahaifiyarsa da ’yan’uwansa da kuma almajiransa. A can suka zauna ’yan kwanaki.

(Mattiyu 21.12,13; Markus 11.15-17; Luka 19.45,46)

13Da lokacin Bikin Ƙetarewa na Yahudawa ya yi kusa, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima. 14A filin haikali ya sami mutane suna sayar da shanu, tumaki da tattabaru, waɗansu kuma zaune a tebur suna canjin kuɗi. 15Saboda haka ya tuƙa bulala ta igiyoyi, ya kori duka daga filin haikali, har da tumaki da shanu; ya watsar da kuɗin masu canjin, ya birkice teburansu. 16Ga masu sayar da tattabaru kuwa ya ce, “Ku kwashe waɗannan daga nan! Don me za ku mai da gidan Ubana kasuwa!” 17Sai almajiransa suka tuna cewa a rubuce yake, “Himma saboda gidanka zai cinye ni.”2.17 Zab 69.9

18Sai Yahudawa suka tambaye shi, “Wace abar banmamaki za ka nuna mana ka tabbatar mana ikonka na yin duk waɗannan?”

19Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe wannan haikali, zan kuwa sāke tā da shi cikin kwana uku.”

20Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba’in da shida ana ginin haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka tā da shi?” 21Amma haikalin da ya yi magana jikinsa ne. 22Bayan da ya tashi daga matattu, sai almajiransa suka tuna da abin da ya faɗa. Sa’an nan suka gaskata Nassi da kuma kalmomin da Yesu ya yi.

23To, yayinda yake a Urushalima a Bikin Ƙetarewa, mutane da yawa suka ga abubuwan banmamakin da yake aikata suka kuma gaskata da sunansa. 24Sai dai Yesu bai amince da su ba, don ya san dukan mutane. 25Ba ya bukatar shaidar mutum game da mutum, don yă san abin da yake cikin zuciyar mutum.