Yahuda 1 – HCB & CCB

Hausa Contemporary Bible

Yahuda 1:1-25

1Yahuda, bawan Yesu Kiristi, ɗan’uwan Yaƙub,

Zuwa ga waɗanda aka kira, waɗanda Allah Uba yake ƙauna, waɗanda kuma Yesu Kiristi ya kiyaye.

2Jinƙai, salama da kuma ƙauna, su kasance tare da ku a yalwace.

Zunubi da hallakar marasa tsoron Allah

3Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak. 4Na faɗa haka ne domin waɗansu mutanen da aka rubuta hukuncinsu tun dā sun shiga cikinku a ɓoye. Su fa marasa tsoron Allah ne. Su ne waɗanda suka mai da alherin Allahnmu ya zama dalilin yin fasikanci, suna kuma mūsun Yesu Kiristi wanda shi ne Makaɗaici Mai Iko Duka da kuma Ubangijinmu.

5Ko da yake kun riga kun san duk wannan, ina so in tuna muku cewa Ubangiji ya ceci mutanensa daga Masar, duk da haka daga baya ya hallaka waɗanda ba su ba da gaskiya ba. 6Haka ma mala’ikun da ba su riƙe matsayinsu na iko ba, waɗanda suka bar ainihin mazauninsu, su ne ya tsare a duhu daure da dawwammamun sarƙoƙi don hukunci ta babbar Ranan nan. 7Haka ma Sodom da Gomorra da garuruwan da suke kewaye da su, waɗanda su ma suka ba da kansu ga fasikanci da muguwar sha’awar jiki, sun zama misalin waɗanda suke shan hukuncin madawwamiyar wuta.

8Haka yake da masu mafarke-mafarken nan, gama sun ƙazantar da jikunansu, suka ƙi bin masu mulki, suna ɓata sunan talikan sararin sama. 9Kai, ko Mika’ilu babban shugaban mala’iku ma, sa’ad da yake mūsu da Iblis game da gawar Musa, bai yi garajen ɗora masa laifi da baƙar magana ba, sai dai ya ce, “Ubangiji yă tsawata maka!” 10Duk da haka mutanen nan suna maganar banza a kan kome da ba su gane ba; kuma abubuwan da suka fahimta bisa ga jiki, kamar dabbobi marasa hankali, waɗannan abubuwa ne suke hallaka su.

11Kaitonsu! Gama sun kama hanyar Kayinu; sun ruga a guje garin neman riba cikin kuskure kamar Bala’am; aka kuma hallaka su cikin tawayen Kora.

12Waɗannan mutane sun zama kamar ƙazanta a taronku na soyayya, suna ta ciye-ciye a cikinku, ba kunya ba tsoro. Su masu kiwo ne da suke ciyar da kansu kawai. Su kamar hadari ne da babu ruwa da iska take kori. Su kamar itatuwa ne, marasa ’ya’ya da rani, waɗanda aka tumɓuke, ko kamar itatuwan da aka tumɓuke suka kuma mutu ƙurmus. 13Su kamar raƙuman ruwan teku ne masu hauka, suna taƙama da tumbatsan kumfar kunyarsu. Su kamar taurari ne masu yawo barkatai, waɗanda aka ajiye mugun duhu saboda su har abada.

14Enok ma, wanda yake na bakwai daga Adamu, ya yi annabci game da waɗannan mutane cewa, “Duba, Ubangiji yana zuwa da dubu dubban tsarkakansa 15don yă yi wa kowa shari’a, yă kuma hukunta duk marasa tsoron Allah game da dukan ayyukansu na rashin tsoron Allah da suka aikata ta hanyar rashin tsoron Allah, da kuma dukan baƙaƙen kalmomin da masu zunubi marasa tsoron Allah suka faɗa game da shi.” 16Waɗannan mutane dai, gunaguni gare su, kullum ganin laifin waɗansu suke yi. Muguwar sha’awa ce kaɗai tunaninsu. Sun cika da banzar magana ta yabon kansu. Suna ruɗin mutane da zaƙin baki don samun ribar kansu.

Kira don jimiri

17Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā. 18Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.” 19Waɗannan mutanen ne, suke kawo rabe-rabe, masu bin abin da jiki yake so, marasa Ruhu.

20Amma ku, abokaina ƙaunatattu, ku gina kanku cikin bangaskiyarku mafi tsarki, ku kuma yi addu’a cikin Ruhu Mai Tsarki. 21Ku zauna cikin ƙaunar Allah yayinda kuke jira jinƙan Ubangijinmu Yesu Kiristi don yă kawo ku ga rai madawwami.

22Ku ji tausayin waɗanda suke shakka; 23ku cece waɗansu ta wurin fizge su daga wuta. Ga waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro, har ma ku yi ƙyamar tufafin da suka ɓata da ayyukansu na jiki.

Yabo

24To, yabo yă tabbata a gare shi, shi wanda yake da iko yă tsare ku daga fāɗuwa, yă kuma miƙa ku marasa laifi a gaban ɗaukakarsa da matuƙar farin ciki. 25Gare shi kuma, shi da yake kaɗai Allah Mai Cetonmu, ta wurin Yesu Kiristi Ubangijinmu, bari ɗaukaka, daraja, iko da mulki, su tabbata a gare shi, tun farkon zamanai, yanzu, da har abada abadin! Amin.

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

犹大书 1:1-25

1我是耶稣基督的奴仆、雅各的兄弟犹大,现在写信给蒙父上帝呼召、眷爱、被耶稣基督看顾的人。

2愿上帝丰丰富富地赐给你们怜悯、平安和慈爱!

捍卫真道

3亲爱的弟兄姊妹,我一直迫切地想写信跟你们谈谈我们所共享的救恩,但现在我觉得有必要写信劝勉你们竭力护卫一次就完整地交给圣徒的真道。 4因为有些不敬虔的人偷偷地混进你们中间,以上帝的恩典作借口,放纵情欲,否认独一的主宰——我们的主耶稣基督。圣经上早已记载,这样的人必受到审判。

前车之鉴

5以下的事情,你们虽然都知道,但我还要再提醒你们:从前上帝1:5 上帝”有些抄本作“主”。把祂的子民从埃及救出来,后来把其中不信的人灭绝了。 6至于不守本分、擅离岗位的天使,上帝也用锁链将他们永远囚禁在幽暗里,等候最后审判的大日子到来。 7此外,所多玛蛾摩拉及其附近城镇的人同样因为荒淫无度、沉溺于变态的情欲而遭到永火的刑罚。这些事都成为我们的警戒。

假教师的恶行

8同样,这些做梦的人玷污自己的身体,不服权柄,亵渎有尊荣的。 9当天使长米迦勒摩西的尸体跟魔鬼争辩的时候,尚且不敢用毁谤的话谴责它,只说:“愿主责罚你!” 10这些人却毁谤自己不明白的事,像没有理性的野兽一样凭本能行事,结果自取灭亡。 11他们大祸临头了!他们步了该隐的后尘,为谋利而重蹈巴兰的谬误,又像可拉一样因叛逆而灭亡。 12这些人在你们的爱宴中是败类1:12 败类”希腊文是“暗礁”或“污点”的意思。。他们肆无忌惮地吃喝,是只顾喂养自己的牧人;是没有雨的云,随风飘荡;是深秋不结果子的树,被连根拔起,彻底枯死。 13他们是海中的狂涛,翻动着自己可耻的泡沫,是流荡的星星,有幽幽黑暗永远留给他们。

14亚当的第七代子孙以诺曾经针对这些人说预言:“看啊!主率领祂千万的圣者一同降临, 15要审判所有的人,按不虔不敬的罪人所行的恶事和他们亵渎上帝的话定他们的罪。” 16这些人满腹牢骚,怨天尤人,放纵自己的邪情私欲。他们口出狂言,为了谋利而阿谀奉承他人。

牢记警告

17亲爱的弟兄姊妹,要谨记主耶稣基督的使徒从前给你们的警告。 18他们曾对你们说:“末世的时候,必定有不敬虔、好讥笑的人放纵自己的邪情私欲。” 19这些人制造分裂,血气用事,心中没有圣灵。

20亲爱的弟兄姊妹,你们要在至圣的真道上造就自己,在圣灵的引导下祷告, 21常在上帝的爱中,等候我们主耶稣基督施怜悯赐给你们永生。

22那些心存疑惑的人,你们要怜悯他们; 23有些人,你们要将他们从火中抢救出来;还有些人,你们要怀着畏惧的心怜悯他们,甚至要厌恶被他们的邪情私欲玷污的衣服。

祝颂

24愿荣耀归给我们的救主——独一的上帝!祂能保守你们不失足犯罪,使你们无瑕无疵、欢欢喜喜地站在祂的荣耀面前。 25愿荣耀、威严、能力和权柄借着我们的主耶稣基督都归给祂,从万世以前直到现今,一直到永永远远。阿们!