Mattiyu 9 – HCB & NIV

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 9:1-38

Yesu ya warkar da shanyayye

(Markus 2.1-12; Luka 5.17-26)

1Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa. 2Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

3Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”

4Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku? 5Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’ 6Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.” 7Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida. 8Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.

Kiran Mattiyu

(Markus 2.13-17; Luka 5.27-32)

9Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

10Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa. 11Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”

12Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya. 13Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’9.13 Hos 6.6 Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”

An Tuhumi Yesu game da azumi

(Markus 2.18-22; Luka 5.33-39)

14Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”

15Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.

16“Ba mai yin faci da sabon ƙyalle a kan tsohuwar riga, gama facin zai kece rigar yă sa kecewar ma ta fi ta dā muni. 17Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yă zube salkunan kuma su lalace. A’a, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.”

Yarinya da ta mutu da kuma mace marar lafiya

(Markus 5.21-43; Luka 8.40-56)

18Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.” 19Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.

20A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa. 21Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.”

22Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take macen ta warke.

23Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya, 24sai ya ce, “Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne.” Amma suka yi masa dariya. 25Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi. 26Labarin wannan kuwa ya bazu ko’ina a yankin.

Yesu ya warkar da makafi da kuma kurame

27Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!”

28Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?”

Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.”

29Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”; 30sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.” 31Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi ko’ina a wannan yankin.

32Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana. 33Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.”

34Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”

Ma’aikata kaɗan ne

35Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya. 36Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi. 37Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne. 38Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”

New International Version

Matthew 9:1-38

Jesus Forgives and Heals a Paralyzed Man

1Jesus stepped into a boat, crossed over and came to his own town. 2Some men brought to him a paralyzed man, lying on a mat. When Jesus saw their faith, he said to the man, “Take heart, son; your sins are forgiven.”

3At this, some of the teachers of the law said to themselves, “This fellow is blaspheming!”

4Knowing their thoughts, Jesus said, “Why do you entertain evil thoughts in your hearts? 5Which is easier: to say, ‘Your sins are forgiven,’ or to say, ‘Get up and walk’? 6But I want you to know that the Son of Man has authority on earth to forgive sins.” So he said to the paralyzed man, “Get up, take your mat and go home.” 7Then the man got up and went home. 8When the crowd saw this, they were filled with awe; and they praised God, who had given such authority to man.

The Calling of Matthew

9As Jesus went on from there, he saw a man named Matthew sitting at the tax collector’s booth. “Follow me,” he told him, and Matthew got up and followed him.

10While Jesus was having dinner at Matthew’s house, many tax collectors and sinners came and ate with him and his disciples. 11When the Pharisees saw this, they asked his disciples, “Why does your teacher eat with tax collectors and sinners?”

12On hearing this, Jesus said, “It is not the healthy who need a doctor, but the sick. 13But go and learn what this means: ‘I desire mercy, not sacrifice.’9:13 Hosea 6:6 For I have not come to call the righteous, but sinners.”

Jesus Questioned About Fasting

14Then John’s disciples came and asked him, “How is it that we and the Pharisees fast often, but your disciples do not fast?”

15Jesus answered, “How can the guests of the bridegroom mourn while he is with them? The time will come when the bridegroom will be taken from them; then they will fast.

16“No one sews a patch of unshrunk cloth on an old garment, for the patch will pull away from the garment, making the tear worse. 17Neither do people pour new wine into old wineskins. If they do, the skins will burst; the wine will run out and the wineskins will be ruined. No, they pour new wine into new wineskins, and both are preserved.”

Jesus Raises a Dead Girl and Heals a Sick Woman

18While he was saying this, a synagogue leader came and knelt before him and said, “My daughter has just died. But come and put your hand on her, and she will live.” 19Jesus got up and went with him, and so did his disciples.

20Just then a woman who had been subject to bleeding for twelve years came up behind him and touched the edge of his cloak. 21She said to herself, “If I only touch his cloak, I will be healed.”

22Jesus turned and saw her. “Take heart, daughter,” he said, “your faith has healed you.” And the woman was healed at that moment.

23When Jesus entered the synagogue leader’s house and saw the noisy crowd and people playing pipes, 24he said, “Go away. The girl is not dead but asleep.” But they laughed at him. 25After the crowd had been put outside, he went in and took the girl by the hand, and she got up. 26News of this spread through all that region.

Jesus Heals the Blind and the Mute

27As Jesus went on from there, two blind men followed him, calling out, “Have mercy on us, Son of David!”

28When he had gone indoors, the blind men came to him, and he asked them, “Do you believe that I am able to do this?”

“Yes, Lord,” they replied.

29Then he touched their eyes and said, “According to your faith let it be done to you”; 30and their sight was restored. Jesus warned them sternly, “See that no one knows about this.” 31But they went out and spread the news about him all over that region.

32While they were going out, a man who was demon-possessed and could not talk was brought to Jesus. 33And when the demon was driven out, the man who had been mute spoke. The crowd was amazed and said, “Nothing like this has ever been seen in Israel.”

34But the Pharisees said, “It is by the prince of demons that he drives out demons.”

The Workers Are Few

35Jesus went through all the towns and villages, teaching in their synagogues, proclaiming the good news of the kingdom and healing every disease and sickness. 36When he saw the crowds, he had compassion on them, because they were harassed and helpless, like sheep without a shepherd. 37Then he said to his disciples, “The harvest is plentiful but the workers are few. 38Ask the Lord of the harvest, therefore, to send out workers into his harvest field.”