Mattiyu 8 – HCB & SNC

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 8:1-34

Mutum mai kuturta

(Markus 1.40-45; Luka 5.12-16)

1Da ya sauko daga dutsen, sai taron mutane mai yawan gaske suka bi shi. 2Wani mutum mai kuturta ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Ubangiji, in kana so, kana iya tsabtacce ni.”

3Yesu ya miƙa hannunsa ya taɓa mutumin. Ya ce, “Ina so, ka tsabtacce!” Nan da nan aka warkar8.3 Girik aka tsabtacce da shi daga kuturtarsa. 4Sai Yesu ya ce masa, “Ka lura kada ka gaya wa kowa. Sai dai ka tafi, ka nuna kanka ga firist ka kuma yi bayarwar da Musa ya umarta, a matsayin shaida gare su.”

Bangaskiyar jarumi

(Luka 7.1-10; Yohanna 4.43-54)

5Da Yesu ya shiga Kafarnahum, sai wani jarumi ya zo wurinsa, yana neman taimako. 6Ya ce, “Ubangiji, bawana yana kwance a gida shanyayye, yana kuma shan azaba ƙwarai.”

7Yesu ya ce masa, “Zan je in warkar da shi.”

8Jarumin ya amsa, “Ubangiji, ban cancanci in sa ka zo gidana ba, ka dai yi magana kawai, bawana zai warke. 9Gama ni kaina mutum ne a ƙarƙashin iko, da kuma sojoji a ƙarƙashina. Nakan ce wa wannan, ‘Je ka,’ sai yă tafi; wancan kuma, ‘Zo nan,’ sai yă zo. Nakan ce wa bawana, ‘Yi wannan,’ sai kuwa yă yi.”

10Da Yesu ya ji wannan, sai ya yi mamaki ya kuma ce wa waɗanda suke binsa, “Gaskiya nake gaya muku, ban taɓa samun wani a Isra’ila da bangaskiya mai girma haka ba. 11Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama. 12Amma za a jefar da ’ya’yan mulki waje, zuwa cikin baƙin duhu, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

13Sa’an nan Yesu ya ce wa jarumin, “Je ka! Za a yi bisa ga bangaskiyarka.” A daidai wannan lokaci bawansa kuwa ya warke.

Yesu ya warkar da mutane da yawa

(Markus 1.29-34; Luka 4.38-41)

14Da Yesu ya zo cikin gidan Bitrus, sai ya ga surukar Bitrus tana kwance a gado tana da zazzaɓi. 15Ya taɓa hannunta sai zazzaɓin ya sake ta, ta kuwa tashi ta fara yin masa hidima.

16Da yamma ta yi, aka kawo masa masu aljanu da yawa, ya kuwa fitar da ruhohin ta wurin magana, ya kuma warkar da dukan marasa lafiya. 17Wannan ya faru ne domin a cika abin da aka faɗa ta bakin annabi Ishaya cewa,

“Ya ɗebi rashin lafiyarmu,

ya kuma ɗauki cututtukanmu.”8.17 Ish 53.4

Wahalar bin Yesu

(Luka 9.57-62)

18Da Yesu ya ga taron mutane kewaye da shi, sai ya ba da umarni a ƙetare zuwa ɗayan hayin tafkin. 19Sai wani malamin dokoki ya zo wurinsa ya ce, “Malam, zan bi ka duk inda za ka.”

20Sai Yesu ya amsa ya ce, “Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa.”

21Sai wani almajiri ya ce masa, “Ubangiji, da farko bari in je in binne mahaifina.”

22Amma Yesu ya ce masa, “Ka bi ni, ka bar matattu su binne matattunsu.”

Yesu ya kwantar da hadari

(Markus 4.35-41; Luka 8.22-25)

23Sai ya shiga jirgin ruwa, almajiransa kuwa suka bi shi. 24Ba zato ba tsammani, sai wani babban hadari ya taso a tafkin, har raƙuman ruwan suka sha kan jirgin. Amma Yesu yana barci. 25Almajiran suka je suka tashe shi, suna cewa, “Ubangiji, ka cece mu! Za mu nutse!”

26Ya amsa ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, me ya sa kuke tsoro haka?” Sa’an nan ya tashi ya tsawata wa iskar da kuma raƙuman ruwan, sai wuri ya yi tsit gaba ɗaya.

27Mutanen suka yi mamaki suka ce, “Wane irin mutum ne wannan? Har iska da raƙuman ruwa suna masa biyayya!”

Warkar da mutum biyu masu aljanu

(Markus 5.1-20; Luka 8.26-39)

28Da ya isa ɗayan gefen a yankin Gadarenawa8.28 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Gergesenawa; waɗansu kuma Gerasenawa ne a nan (ko kuwa Gerasenawa), sai ga mutum biyu masu aljanu suna fitowa daga kaburbura suka tarye shi. Su abin tsoro ne ƙwarai, har ba mai iya bin wannan hanya. 29Suka yi ihu suka ce, “Me ya haɗa ka da mu, Ɗan Allah?” Ka zo ne nan don ka ji mana kafin lokaci yă yi?

30Nesa kaɗan da su kuwa akwai babban garken aladu da yake kiwo. 31Aljanun suka roƙi Yesu suka ce, “In ka fitar da mu, tura mu cikin garken aladun nan.”

32Ya ce musu, “Ku tafi!” Sai suka fita suka shiga cikin aladun, dukan garken kuwa ya gangara a guje daga kan tudun zuwa cikin tafkin aladun kuma suka mutu a cikin ruwa. 33Masu kiwon aladun suka ruga, suka je cikin gari suka ba da labarin dukan wannan, haɗe da abin da ya faru da mutanen nan masu aljanu. 34Sai dukan garin suka fito don su taryi Yesu. Da suka kuwa gan shi, sai suka roƙe shi yă bar musu yanki.

Slovo na cestu

Matouš 8:1-34

Ježíš uzdravuje malomocného

1Velké zástupy se hrnuly za Ježíšem, když sestupoval s hory. 2Tu se k němu přiblížil malomocný, klekl před ním a řekl: „Pane, budeš-li chtít, můžeš mne uzdravit!“

3Ježíš zvedl ruku, dotkl se toho muže a řekl: „Ano, chci. Ať tvá nemoc zmizí!“ A hned byl ten malomocný zdráv. 4Ježíš mu pak řekl: „Nikomu nic neříkej, ale jdi, ukaž se knězi a vezmi s sebou obětní dar, který ustanovil Mojžíš pro uzdravené od malomocenství. To bude veřejné svědectví o tvém uzdravení.“

Římský setník projevuje svou víru

5Když Ježíš přicházel do Kafarnaum, přistoupil k němu římský setník s prosbou: 6„Pane, můj služebník leží doma ochrnutý a má velké bolesti.“

7Ježíš mu odpověděl: „Přijdu za ním a uzdravím ho.“ 8Setník mu však na to řekl: „Pane, nezasloužím si, aby ses namáhal ke mně domů. Vždyť stačí tvé slovo, a bude uzdraven. 9Já vím, jak to je: sám poslouchám i poroučím. Když vojákovi rozkážu, tak jde, když ho zavolám, přijde. A když uložím svému služebníkovi práci, tak ji vykoná. Takovou moc máš ty i nad nemocemi.“

10Když to Ježíš uslyšel, podivil se a řekl těm, kteří šli s ním: „Řeknu vám, že s tak velikou vírou jsem se nesetkal v celém Izraeli. 11Je to opravdu tak, že mnozí lidé z celého světa budou přijati do Boží věčné říše, 12zatímco mnozí Izraelci, pro které byla připravena, budou z ní vyloučeni; zbyde jim beznaděj, bolest a pláč.“

13Potom se Ježíš obrátil opět k setníkovi: „Jdi domů. Čemu jsi uvěřil, ať se stane.“ V tu chvíli se služebník uzdravil.

Ježíš uzdravuje Petrovu tchyni a mnoho dalších

14Pak Ježíš navštívil Petra a našel jeho tchyni schvácenou horečkou. 15Dotkl se její ruky, teplota klesla a jí se ulevilo natolik, že vstala a obsloužila hosta.

16Večer k němu přivedli mnoho posedlých, on je pouhým slovem zbavil zlého a všechny nemocné uzdravil. 17Tím se naplnilo, co předpověděl prorok Izajáš: „On na sebe vzal naše slabosti a nesl naše nemoci.“

Ježíš učí o ceně následování

18Když Ježíš viděl, jak se kolem něj kupí množství lidí, chtěl se na loďce přeplavit na druhou stranu jezera; 19zadržel ho však ještě jeden učitel zákona: „Mistře, chci být stále s tebou.“

20Ježíš mu odpověděl: „Každá liška má svou noru, pták hnízdo, ale já často nemám kde spát.“

21Jeden z jeho žáků mu zase řekl: „Pane, než půjdu s tebou, dovol mi ještě pohřbít mého otce.“ 22Ale Ježíš mu odpověděl: „Ty pojď se mnou! Poslední službu mrtvému může poskytnout za tebe i ten, kdo se ještě duchovně neprobudil.“

Ježíš utišuje bouři

23Pak vyplul spolu se svými učedníky. 24Nad jezerem se strhla prudká bouře, takže člunu hrozilo potopení ve vlnách. Ježíš však klidně spal. 25Probudili ho: „Pane, zachraň nás. Jde o život!“ 26Ale on jim řekl: „Proč se bojíte? Kde je vaše víra?“ Vstal, okřikl vítr i vlny, a nastal klid. 27Kteří to viděli, byli naplněni údivem a říkali si: „Kdo to vlastně je, že ho poslouchají vítr i moře?“

Ježíš vyhání démony do stáda vepřů

28Když přistáli na druhém břehu jezera poblíž Gadary, narazili na dva muže posedlé démony. Ti žili ve skalních hrobech a byli tak nebezpeční, že se nikdo neodvážil tudy chodit. 29Na Ježíše začali křičet: „Co je ti do nás, Boží Synu? Ještě na nás nemáš právo!“ 30Opodál se páslo velké stádo vepřů. 31„Když nám bereš moc nad lidmi, nech nám ji aspoň nad těmi vepři,“ prosili démoni.

32On jim řekl: „Zmizte!“ Démoni opustili muže a zmocnili se zvířat. V tom okamžiku se celé stádo splašilo a hnalo se dolů k jezeru, kde se utopilo. 33Pasáci vepřů utekli do města a všude roznesli, co se stalo. 34Celé město se šlo na Ježíše podívat, ale žádali ho, aby z jejich kraje odešel.