Mattiyu 6 – HCB & PCB

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 6:1-34

Bayarwa ga mabukata

1“Ku yi hankali kada ku nuna ‘ayyukanku na adalci’ a gaban mutane, don su gani. In kuka yi haka, ba za ku sami lada daga wurin Ubanku da yake cikin sama ba.

2“Saboda haka sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yi shelarsa, yadda munafukai suke yi a majami’u da kuma kan tituna, don mutane su yabe su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 3Amma sa’ad da kake ba wa masu bukata taimako, kada ka yarda hannun hagunka yă ma san abin da hannun damarka yake yi, 4don bayarwarka ta zama a ɓoye. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

Addu’a

(Luka 11.2-4)

5“Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku zama kamar munafukai, gama sun cika son yin addu’a a tsaye a cikin majami’u da kuma a bakin titi, don mutane su gan su. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 6Amma sa’ad da kake addu’a, sai ka shiga ɗakinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu’a ga Ubanka wanda ba a gani. Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka. 7Sa’ad da kuma kuke addu’a, kada ku yi ta maimaita magana, kamar marasa sanin Allah, domin suna tsammani za a ji su saboda yawan maganarsu. 8Kada ku zama kamar su, gama Ubanku ya san abin da kuke bukata kafin ma ku roƙe shi.

9“To, ga yadda ya kamata ku yi addu’a.

“ ‘Ubanmu wanda yake cikin sama,

a tsarkake sunanka,

10mulkinka yă zo

a aikata nufinka a duniya

kamar yadda ake yi a sama.

11Ka ba mu yau abincin yininmu.

12Ka gafarta mana laifofinmu,

kamar yadda mu ma muke gafarta wa masu yin mana laifi.

13Kada ka bari a kai mu cikin jarraba,

amma ka cece mu daga mugun nan.6.13 Ko kuwa daga mugu; waɗansu rubuce-rubucen hannun da ba su jima ba ɗaya, gama mulki da iko da ɗaukaka naka ne har abada. Amin.

14Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku. 15Amma in ba kwa yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku ma ba zai gafarta muku zunubanku ba.

Azumi

16“Sa’ad da kuma kuna azumi, kada ku ɓata fuska, yadda munafukai suke yi. Sukan ɓata fuskokinsu domin su nuna wa mutane cewa suna azumi. Gaskiya nake gaya muku, sun riga sun sami ladarsu cikakke. 17Amma sa’ad da kana azumi, ka shafa wa kanka mai, ka wanke fuskarka, 18domin kada mutane su ga alama cewa kana azumi, sai dai Ubanka kaɗai wanda ba a gani; Ubanka kuwa mai ganin abin da ake yi a ɓoye, zai sāka maka.

Ajiya a sama

(Luka 12.33,34)

19“Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. 20Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata. 21Gama inda dukiyarka take, a nan ne fa zuciyarka za tă kasance.

(Luka 11.34-36)

22“Ido shi ne fitilar jiki. In idanunka suna da kyau, dukan jikinka zai cika da haske. 23Amma in idanunka suna da lahani, dukan jikinka ma zai cika da duhu. To, in hasken da yake a cikinka duhu ne, duhun ya wuce misali ke nan!

(Luka 16.13)

24“Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai yă ƙi ɗaya, yă ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yă yi aminci ga ɗaya, sa’an nan yă rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya.”

Kada ku damu

(Luka 12.22-31)

25“Saboda haka, ina gaya muku, kada ku damu game da rayuwarku, game da abin da za ku ci, ko abin da za ku sha; ko kuma game da jikinku, game da abin da za ku sa. Ashe, rai bai fi abinci ba, jiki kuma bai fi tufafi ba? 26Ku dubi tsuntsayen sararin sama mana; ba sa shuki ko girbi ko ajiya a rumbuna, duk da haka, Ubanku na sama yana ciyar da su. Ashe, ba ku fi su daraja nesa ba? 27Wane ne a cikinku ta wurin damuwa zai iya ƙara wa rayuwarsa ko sa’a ɗaya6.27 Ko kuwa a kamu guda ga tsayinsa?

28“Me ya sa kuke damuwa a kan riguna? Ku dubi yadda furannin jeji suke girma mana. Ba sa aiki ko saƙa. 29Duk da haka ina gaya muku ko Solomon cikin dukan darajarsa bai sa kayan adon da ya kai na ko ɗaya a cikinsu ba. 30In haka Allah yake yi wa ciyawar jeji sutura, wadda yau tana nan, gobe kuwa a jefa a cikin wuta, ba zai ma fi yi muku sutura ba, ya ku masu ƙarancin bangaskiya? 31Don haka, kada ku damu, kuna cewa, ‘Me za mu ci?’ Ko, ‘Me za mu sha?’ Ko kuma, ‘Me za mu sa?’ 32Gama marasa sanin Allah suna fama neman dukan waɗannan abubuwa, Ubanku na sama kuwa ya san kuna bukatarsu. 33Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa. 34Saboda haka kada ku damu game da gobe, gama gobe zai damu da kansa. Damuwar yau ma ta isa wahala.

Persian Contemporary Bible

متی‌ٰ 6:1-34

پرهيز از تظاهر

1«مراقب باشيد كه اعمال نيک خود را در انظار مردم انجام ندهيد، تا شما را ببينند و تحسين كنند، زيرا در اين صورت نزد پدر آسمانی‌تان اجری نخواهيد داشت. 2هرگاه به فقيری كمک می‌كنی، مانند رياكاران كه در كنيسه و در بازار از خود تعريف می‌كنند تا مردم به آنها احترام بگذارند، دربارهٔ كار نيک خود داد سخن سر نده، چون به اين ترتيب، اجری را كه می‌بايست از خدا بگيری، از مردم گرفته‌ای. 3اما وقتی به كسی صدقه‌ای می‌دهی، نگذار حتی دست چپت از كاری كه دست راستت می‌كند، آگاه شود، 4تا نيكويی تو در نهان باشد. آنگاه پدر آسمانی كه امور نهان را می‌بيند، تو را اجر خواهد داد.

دعا و روزهٔ مسيحی

5«و اما دربارهٔ دعا. هرگاه دعا می‌كنی، مانند رياكاران نباش كه دوست دارند در عبادتگاه‌ها يا در گوشه و كنار خيابانها نماز بخوانند تا توجه مردم را به خود جلب كنند و خود را مؤمن نشان دهند. مطمئن باش اجری را كه بايد از خدا بگيرند، همين جا از مردم گرفته‌اند. 6اما تو هرگاه دعا می‌كنی، در تنهايی و در خلوت دل، پدر آسمانی را عبادت نما؛ و او كه كارهای نهان تو را می‌بيند، به تو پاداش خواهد داد.

7‏-8«وقتی دعا می‌كنيد، مانند كسانی كه خدای حقيقی را نمی‌شناسند، وِردهای بی‌معنی تكرار نكنيد. ايشان گمان می‌كنند كه با تكرار زياد، دعايشان مستجاب می‌شود. اما شما اين را به یاد داشته باشيد كه پدرتان، قبل از اينكه از او چيزی بخواهيد، كاملاً از نيازهای شما آگاه است.

9«پس شما اين گونه دعا كنيد:

«ای پدر ما كه در آسمانی،

نام مقدس تو گرامی باد.

10ملكوت تو برقرار گردد.

خواست تو آنچنان كه در آسمان مورد اجراست، بر زمين نيز اجرا شود.

11نان روزانهٔ ما را امروز نيز به ما ارزانی دار.

12خطاهای ما را بيامرز چنانكه ما نيز آنان را كه به ما بدی كرده‌اند، می‌بخشيم.

13ما را از وسوسه‌ها دور نگاه دار و از شيطان حفظ فرما؛

زيرا ملكوت و قدرت و جلال تا ابد از آن توست. آمين!

14‏-15«پدر آسمانی، شما را به شرطی خواهد بخشيد كه شما نيز آنانی را كه به شما بدی كرده‌اند، ببخشيد.

16«و اما دربارهٔ روزه. وقتی روزه می‌گيريد، مانند رياكاران خود را افسرده و ناتوان نشان ندهيد. ايشان با اين كار می‌خواهند به مردم بفهمانند كه روزه گرفته‌اند. مطمئن باشيد كه ايشان تمام اجر خود را به همين صورت از مردم می‌گيرند. 17اما تو وقتی روزه می‌گيری، سر و صورت خود را تميز و مرتب كن، 18تا كسی متوجه نشود روزه گرفته‌ای. آنگاه پدر آسمانی تو كه از همه چيز آگاه است، تو را اجر خواهد داد.

ثروت و خوراک و پوشاک

19«ثروت خود را بر روی اين زمين نيندوزيد زيرا ممكن است بيد يا زنگ به آن آسيب رساند و يا دزد آن را بربايد. 20ثروتتان را در آسمان بيندوزيد، در جايی كه از بيد و زنگ و دزد خبری نيست. 21اگر ثروت شما در آسمان باشد، فكر و دلتان نيز در آنجا خواهد بود.

22«چشم، چراغ وجود انسان است. اگر چشم تو پاک باشد، تمام وجودت نيز پاک و روشن خواهد بود. 23ولی اگر چشمت با شهوت و طمع تيره شده باشد، تمام وجودت هم در تاريكی عميقی فرو خواهد رفت. چه تاريكی وحشتناكی!

24«نمی‌توانی به دو ارباب خدمت كنی. بايد فقط يكی از آنها را دوست داشته باشی و فقط به يكی وفادار بمانی. همچنين نمی‌توانی هم بندهٔ خدا باشی و هم بندهٔ پول.

25«پس نصيحت من اين است كه برای خوراک و پوشاک غصه نخوريد. برای همين زندگی و بدنی كه داريد شاد باشيد. آيا ارزش زندگی و بدن، بيشتر از خوراک و پوشاک نيست؟ 26به پرندگان نگاه كنيد. غصه ندارند كه چه بخورند. نه می‌كارند، نه درو می‌كنند، و نه در انبارها ذخيره می‌كنند، ولی پدر آسمانی شما خوراک آنها را فراهم می‌سازد. آيا شما برای خدا خيلی بيشتر از اين پرندگان ارزش نداريد؟ 27آيا غصه خوردن می‌تواند يک لحظه عمرتان را طولانی‌تر كند؟

28«چرا برای لباس و پوشاک غصه می‌خوريد؟ به گلهای سوسن كه در صحرا هستند، نگاه كنيد. آنها برای لباس غصه نمی‌خورند. 29با اين حال به شما می‌گويم كه سليمان هم با تمام شكوه و ثروت خود، هرگز لباسی به زيبايی اين گلهای صحرايی نپوشيد. 30پس اگر خدا در فكر گلهايی است كه امروز هستند و فردا از بين می‌روند، چقدر بيشتر در فكر شماست، ای كم‌ايمانان.

31‏-32«پس غصهٔ خوراک و پوشاک را نخوريد. چون بی‌ايمانان دربارهٔ اين چيزها دائماً فكر می‌كنند و سخن می‌گويند. شما با ايشان فرق داريد. پدر آسمانی شما كاملاً می‌داند شما به چه نياز داريد. 33اگر شما قبل از هر چيز، به ملكوت و عدالت خدا دل ببنديد، او همهٔ اين نيازهای شما را برآورده خواهد ساخت.

34«پس غصهٔ فردا را نخوريد، چون خدا در فكر فردای شما نيز می‌باشد. مشكلات هر روز برای همان روز كافی است؛ لازم نيست مشكلات روز بعد را نيز به آن بيفزاييد.»