Mattiyu 27 – HCB & JCB

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 27:1-66

Yahuda ya rataye kansa

(Markus 15.1; Luka 23.1,2; Yohanna 18.28-32)

1Da wayewar gari, sai dukan manyan firistoci da dattawan mutane suka yanke shawara su kashe Yesu. 2Suka daure shi, suka tafi da shi, suka ba da shi ga gwamna Bilatus.

(Ayyukan Manzanni 1.18,19)

3Sa’ad da Yahuda, wanda ya bashe Yesu, ya ga an yanke wa Yesu hukuncin kisa, sai ya yi “da na sani.” Ya je mayar wa manyan firistoci da dattawan kuɗin azurfa talatin ɗin. 4Ya ce, “Na yi zunubi da na ci amanar marar laifi.”

Suka ce masa, “Ina ruwanmu da wannan? Wannan dai ruwanka ne.”

5Sai Yahuda ya zubar da kuɗin a cikin haikalin ya tafi. Sa’an nan ya je ya rataye kansa.

6Manyan firistoci suka ɗauki kuɗin, suka ce, “Doka ta hana a sa kuɗin a cikin ma’aji, da yake kuɗin jini ne.” 7Saboda haka, sai suka yanke shawara su yi amfani da kuɗin suka sayi filin mai yin tukwane, saboda binne baƙi. 8Shi ya sa ake kiran filin, Filin Jini har yă zuwa yau. 9Sai abin da aka faɗa ta bakin annabi Irmiya ya cika cewa, “Suka ɗauki azurfa talatin, kuɗin da mutanen Isra’ila suka sa a kansa, 10suka kuma yi amfani da su, suka sayi filin mai yin tukwane, kamar yadda Ubangiji ya umarce ni.”27.10 Dubi Zak 11.12,13; Irm 19.1-13; Irm 32.6-9.

Yesu a gaban Bilatus

(Markus 15.2-5; Luka 23.3-5; Yohanna 18.33-38)

11Ana cikin haka, Yesu kuwa yana tsaye a gaban gwamna, sai gwamnan ya tambaye shi, “Kai ne Sarkin Yahudawa?”

Yesu ya ce, “I, haka ne, kamar yadda ka faɗa.”

12Da manyan firistoci da dattawa suka zarge shi, bai ba da amsa ba. 13Sai Bilatus ya tambaye shi ya ce, “Ba ka jin shaidar da suke kawowa a kanka?” 14Amma Yesu bai ce uffam game da ko ɗaya daga cikin zargin da suka yi masa ba. Har gwamna ya yi mamaki ƙwarai.

(Markus 15.6-15; Luka 23.13-26; Yohanna 18.39–19.16)

15A wannan irin Biki, gwamna yana da wata al’ada, ta sakin ɗan kurkuku guda wanda taron suka zaɓa. 16To, a wannan lokaci kuwa suna da wani shahararren ɗan kurkuku da ake kira Barabbas. 17Saboda haka da taron suka taru, sai Bilatus ya tambaye su ya ce, “Wane ne a cikinsu kuke so in sakar muku. Barabbas ko Yesu wanda ake kira Kiristi?” 18Don ya san saboda sonkai ne suka ba da Yesu a gare shi.

19Yayinda Bilatus yake zaune a kan kujerar shari’a, sai matarsa ta aika masa da wannan saƙo cewa, “Kada ka sa hannunka a kan marar laifin nan, domin na sha wahala ƙwarai, a cikin mafarki yau game da shi.”

20Amma manyan firistoci da dattawa suka shawo kan taron, su ce, a ba su Barabbas, amma a kashe Yesu.

21Gwamna ya yi tambaya ya ce, “Wane ne cikin biyun nan, kuke so in sakar muku?”

Suka ce, “Barabbas.”

22Bilatus ya yi tambaya, “To, me zan yi da Yesu wanda ake kira Kiristi?”

Duka suka ce, “A gicciye shi!”

23Bilatus ya ce, “Don me? Wane laifi ya yi?”

Amma suka ƙara tā da ihu, suna cewa, “A gicciye shi!”

24Da Bilatus ya ga cewa ba ya kaiwa ko’ina, sai ma hargitsi ne yake so yă tashi, sai ya ɗibi ruwa, ya wanke hannuwansa a gaban taron ya ce, “Ni kam, ba ruwana da alhakin jinin mutumin nan. Wannan ruwanku ne!”

25Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!”

26Sai ya sakar musu Barabbas. Amma ya sa aka yi wa Yesu bulala, sa’an nan ya ba da shi a gicciye.

Sojoji sun yi wa Yesu ba’a

(Markus 15.16-21; Yohanna 19.2,3)

27Sai sojojin gwamna suka ɗauki Yesu suka kai shi Fadar mai mulki, sa’an nan suka tara dukan kamfanin sojoji kewaye da shi. 28Suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar riga. 29Suka kuma tuƙa wani rawanin ƙaya, suka sa masa a kā. Suka sa sanda a hannun damansa. Suka durƙusa a gabansa, suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ranka yă daɗe sarkin Yahudawa!” 30Suka tattofa masa miyau, suka karɓe sandan, suka yi ta ƙwala masa shi a kai. 31Bayan sun yi masa ba’a, sai suka tuɓe masa rigar, suka sa masa nasa tufafin. Sai suka tafi da shi, domin su gicciye shi.

Gicciyewa

(Markus 15.16-21; Yohanna 19.2,3)

32Suna fitowa ke nan, sai suka sadu da wani mutumin Sairin, mai suna Siman. Sai suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen. 33Sai suka iso wani wurin da ake kira Golgota (wanda yake nufin Wurin Ƙoƙon Kai). 34A can, suka ba shi ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha. Amma da ya ɗanɗana, sai ya ƙi sha. 35Bayan da suka gicciye shi, sai suka raba tufafinsa a tsakaninsu ta wurin jefa ƙuri’a. 36Sa’an nan suka zauna suna tsaronsa. 37Bisa da kansa kuwa, an kafa rubutun zargin da aka yi masa, da ya ce,

Wannan shi ne Yesu Sarkin Yahudawa.

38An gicciye ’yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a damansa, ɗaya kuma a hagunsa. 39Masu wucewa, suka zazzage shi, suna kaɗa kai, 40suna cewa, “Kai da za ka rushe haikali, ka kuma gina shi cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, ka sauka daga gicciyen!”

41Haka ma, manyan firistoci da malaman dokoki da kuma dattawa, suka yi ta yin masa ba’a, suna cewa, 42“Ya ceci waɗansu, amma ya kāsa ceton kansa! In shi ne Sarkin Isra’ila! To, yă sauko daga kan gicciyen nan, mu kuwa mu gaskata shi. 43Ya dogara ga Allah. Bari Allah yă cece shi yanzu, in yana sonsa, domin ya ce, ‘Ni Ɗan Allah ne.’ ” 44Haka ma, ’yan fashin da aka gicciye tare da shi, suka zazzage shi.

Mutuwar Yesu

(Markus 15.33-41; Luka 23.44-49; Yohanna 19.28-30)

45Daga sa’a ta shida, har zuwa sa’a ta tara, duhu ya rufe ƙasa duka. 46Wajen sa’a ta tara, Yesu ya ɗaga murya da ƙarfi ya ce, “Eloi, Eloi,27.46 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Eloi, Eloi lama sabaktani?” (Wato, “Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni?”).27.46 Zab 22.1

47Sa’ad da waɗanda suke tsattsaye a wurin suka ji haka, sai suka ce, “Yana kiran Iliya.”

48Nan da nan, ɗaya daga cikinsu ya ruga, ya sami soso, ya jiƙa shi da ruwan tsami, ya sa a sanda, ya miƙa wa Yesu, yă sha. 49Sauran kuwa suka ce, “Ƙyale shi mu ga, ko Iliya zai zo yă cece shi.”

50Da Yesu ya sāke ɗaga murya da ƙarfi, sai ya saki ruhunsa.

51A daidai wannan lokaci, sai labulen haikali ya tsage gida biyu, daga sama har ƙasa. Ƙasa ta jijjiga, duwatsu kuma suka farfashe. 52Kaburbura suka bubbuɗe, jikunan tsarkaka da yawa kuwa cikin waɗanda da suka mutu, suka tashi. 53Suka firfito daga kaburbura, sa’an nan bayan tashin Yesu daga matattu, suka shiga birni mai tsarki, suka bayyana ga mutane da yawa.

54Da jarumin nan tare da waɗanda suke tsaron Yesu, suka ga girgizar ƙasa, da kuma abin da ya faru, sai tsoro ya kama su, suka kuma ce, “Gaskiya, wannan Ɗan Allah ne!”

55Akwai mata da yawa a can, suna kallo daga nesa. Sun bi Yesu tun daga Galili, suna masa hidima. 56A cikinsu, akwai Maryamu Magdalin, da Maryamu uwar Yaƙub da Yoses, da kuma uwar ’ya’yan Zebedi.

Bizinar Yesu

(Markus 15.42-47; Luka 23.50-56; Yohanna 19.38-42)

57Da yamma ta yi, sai ga wani mutum mai arziki daga Arimateya, sunansa Yusuf, wanda shi da kansa almajirin Yesu ne. 58Ya je wurin Bilatus, ya roƙe shi yă ba shi jikin Yesu. Sai Bilatus ya umarta a ba shi. 59Yusuf ya ɗauki jikin ya nannaɗe shi da zanen lilin mai tsabta. 60Sa’an nan ya sa shi a sabon kabarinsa, wanda ya haƙa a dutse. Bayan ya gungura wani babban dutse ya rufe bakin kabarin, sai ya tafi abinsa. 61Maryamu Magdalin da ɗayan Maryamun, suna zaune a wurin, ɗaura da kabarin.

Masu gadi a kabari

62Kashegari, wato, bayan Ranar Shirye-shirye, sai manyan firistoci da Farisiyawa, suka je wurin Bilatus. 63Suka ce, “Ranka yă daɗe, mun tuna, mai ruɗin nan tun yana da rai ya ce, ‘Bayan kwana uku, zan tashi daga matattu.’ 64Saboda haka, ka ba da umarni, a tsare kabarin sai rana ta uku ɗin. In ba haka ba, almajiransa za su iya zuwa su sace jikin, sa’an nan su faɗa wa mutane cewa, an tashe shi daga matattu. Ruɗin ƙarshen nan fa, sai yă fi na farkon muni.”

65Sai Bilatus ya ce, “Shi ke nan, ku ɗebi soja, ku je ku tsare kabarin iya ƙoƙarinku.” 66Sai suka je suka tsare kabarin ta wurin buga masa hatimi, suka kuma sa masu gadi.

Japanese Contemporary Bible

マタイの福音書 27:1-66

27

イエスの裁判と十字架の死

1さて、朝になりました。祭司長とユダヤ人の指導者たちはまた集まり、どうやってローマ政府にイエスの死刑を承認させようかと、あれこれ策を練りました。 2それから、縛ったまま、イエスをローマ総督ピラトに引き渡しました。

3ところで、裏切り者のユダはどうなったでしょう。イエスに死刑の判決が下されると聞いてはじめて、彼は自分のしたことがどんなに大それたことだったか気づき、深く後悔しました。それで祭司長やユダヤ人の指導者たちのところに銀貨三十枚を返しに行き、 4「私はとんでもない罪を犯してしまった。罪のない人の血を売ったりして」と言いました。しかし祭司長たちは、「今さらわれわれの知ったことか。かってにしろ」と言って、取り合おうとしませんでした。

5それでユダは、銀貨を神殿に投げ込み、出て行って首をくくって死んでしまいました。 6祭司長たちはその銀貨を拾い上げてつぶやきました。「まさか、これを神殿の金庫に入れるわけにもいくまい。人を殺すために使った金だから。」

7彼らは相談し、その金で、陶器師が粘土を取っていた畑を買い上げ、そこをエルサレムで死んだ外国人の墓地とすることにしました。 8そこでこの墓地は、今でも「血の畑」と呼ばれています。 9-10こうして、「彼らは銀貨三十枚を取った。それは、イスラエルの人々がその人を見積もった値段だ。彼らは、主が私に命じられたように、それで陶器師の畑を買った」ゼカリヤ11・12―13というエレミヤの預言のとおりになったのです。

11さてイエスは、ローマ総督ピラトの前に立ちました。総督はイエスを尋問しました。「おまえはユダヤ人の王なのか。」イエスは「そのとおりです」と答えました。

12しかし、祭司長とユダヤ人の指導者たちからいろいろな訴えが出されている時は、口をつぐんで、何もお答えになりませんでした。 13それでピラトはイエスに、「おまえにあれほど不利な証言をしているのが、聞こえないのか」と尋ねました。

14それでもイエスは何もお答えになりません。これには総督も、驚きあきれてしまいました。

15ところで、毎年、過越の祭りの間に、ユダヤ人たちが希望する囚人の一人に、総督が恩赦を与える慣習がありました。 16当時、獄中にはバラバという名の知れた男が捕らえられていました。 17それでその朝、群衆が官邸に詰めかけた時、ピラトは尋ねました。「さあ、いったいどちらを釈放してほしいのか。バラバか、それともキリストと呼ばれるイエスか。」 18ピラトがこう言ったのは、イエスが捕らえられたのは、イエスの人気をねたむユダヤ人指導者たちの陰謀だと気づいたからです。

19裁判の最中に、ピラトのもとへ彼の妻が、「どうぞ、その正しい方に手をお出しになりませんように。ゆうべ、その人のことで恐ろしい夢を見ましたから」と言ってよこしました。

20ところが、祭司長とユダヤの役人たちは、バラバを釈放し、イエスの死刑を要求するように、群衆をたきつけました。 21それで、ピラトがもう一度、「二人のうち、どちらを釈放してほしいのか」と尋ねると、群衆は即座に、「バラバを!」と大声で叫んだのでした。

22「では、キリストと呼ばれるあのイエスは、どうするのだ。」「十字架につけろ!」

23「どうしてだ。あの男がいったいどんな悪事を働いたというのか。」ピラトがむきになって尋ねても、人々は、「十字架だ! 十字架につけろ!」と叫び続けるばかりでした。

24どうにも手のつけようがありません。暴動になるおそれさえ出てきました。あきらめたピラトは、水を入れた鉢を持って来させ、群衆の面前で手を洗い、「この正しい人の血について、私には何の責任もない。責任は全部おまえたちが負いなさい」と言いました。

25すると群衆は大声で、「かまわない。責任はおれたちや子どもたちの上にふりかかってもいい!」と叫びました。

26ピラトはやむなくバラバを釈放し、イエスをむち打ってから、十字架につけるためにローマ兵に引き渡しました。 27兵士たちはまず、イエスを兵営に連れて行き、全部隊を召集すると、 28イエスの着物をはぎとって赤いガウンを着せ、 29長いとげのいばらで作った冠を頭に載せ、右手には、王の笏に見立てた葦の棒を持たせました。それから、拝むまねをして、「これはこれは、ユダヤ人の王様。ばんざーい!」とはやし立てました。 30また、つばをかけたり、葦の棒をひったくって頭をたたいたりしました。

31こうしてさんざんからかったあげく、赤いガウンを脱がせ、もとの服を着せると、いよいよ十字架につけるために引いて行きました。 32刑場に行く途中、通りすがりの男にむりやりイエスの十字架を背負わせました。クレネから来合わせたシモンという男でした。 33ついに、ゴルゴタ、すなわち「どくろの丘」という名で知られる場所に着きました。 34兵士たちはそこで、薬用のぶどう酒を飲ませようとしましたが、イエスはちょっと口をつけただけで、飲もうとはされませんでした。

35イエスを十字架につけ終わると、兵士たちはさいころを投げてイエスの着物を分け合いました。 36それがすむと、今度はその場に座って見張りをしました。 37またイエスの頭上には、「この者はユダヤ人の王イエスである」と書いた罪状書きを打ちつけました。

38その朝、強盗が二人、それぞれイエスの右と左で十字架につけられました。 39刑場のそばを通りかかった人々は、大げさな身ぶりをしながら、口ぎたなくイエスをののしりました。 40「やい。神殿を打ちこわして、三日のうちに建て直せるんだってな! おまえが神の子だって? それなら、十字架から降りてみろ。」

41祭司長やユダヤ人の指導者たちも、イエスをあざけりました。 42「他人は救えるが自分は救えないというわけか。イスラエルの王が聞いてあきれる。さあ、十字架から降りて来い! そうしたら信じてやろうじゃないか。 43おまえは神に頼っているのだろう。神のお気に入りなら、せいぜい助けていただくがいい。自分を神の子だと言っていたのだから。」

44強盗までがいっしょになって、悪口をあびせました。

45さて時間がたち、正午にもなったころ、急にあたりが暗くなり、一面の闇におおわれました。それが三時間も続きました。

46三時ごろ、イエスは大声で、「エリ、エリ、レマ、サバクタニ」と叫ばれました。それは、「わが神、わが神。どうしてわたしをお見捨てになったのですか」という意味です。

47近くでその声を聞いた人の中には、「あれはエリヤを呼んでいるのだ」と思う者もいました。 48一人の男がさっと駆け寄り、海綿に酸っぱいぶどう酒を含ませると、それを葦の棒につけて差し出しました。 49ところが、ほかの者たちは、「放っておけよ。エリヤが救いに来るかどうか、見ようじゃないか」と言いました。

50その時、イエスはもう一度大声で叫んで、息を引き取りました。 51すると、神殿の至聖所を仕切っていた幕が、上から下まで真っ二つに裂けたのです。大地は揺れ動き、岩はくずれました。 52さらに墓が開いて、生前神に従っていた多くの人たちが生き返りました。 53彼らはイエスが復活されたあと、墓を出てエルサレムに入り、多くの人の前に姿を現したのです。

54十字架のそばにいた隊長や兵士たちは、このすさまじい地震やいろいろの出来事を見て震え上がり、「この人はほんとうに神の子だった!」と叫びました。

55イエスの世話をするためにガリラヤからついて来たたくさんの女たちも、遠くからこの様子を見ていました。 56マグダラのマリヤ、ヤコブとヨセフの母マリヤ、ゼベダイの息子ヤコブとヨハネの母などです。

イエスの埋葬

57夕方になりました。イエスの弟子で、アリマタヤ出身のヨセフという金持ちが来て、 58ピラトに、イエスの遺体を引き取りたいと願い出ました。ピラトは願いを聞き入れ、遺体を渡すように命じました。 59ヨセフは遺体を取り降ろすと、きれいな亜麻布でくるみ、 60岩をくり抜いた、自分の新しい墓に納めました。そして、大きな石を転がして入口をふさぎ、帰って行きました。 61この有様を、マグダラのマリヤともう一人のマリヤが、近くに座って見ていました。 62-63翌日の安息日に、祭司長やパリサイ人たちがピラトに願い出ました。「総督閣下。あの大うそつきは、確か、『わたしは三日後に復活する』と言っていました。 64それをいいことに、弟子たちが死体を盗み出し、イエスは復活したと言いふらしては、まずいことになりかねません。それこそ、このところの騒ぎではすまず、大混乱になるかもしれません。ですからどうぞ、墓を三日目まで見張るように命令を出してください。」

65ピラトは答えました。「よろしい。では厳重に見張らせるがよい。」

66そこで彼らは、石に封印をし、警備の者をおいて、だれも忍び込めないようにしました。