Mattiyu 21 – HCB & CCBT

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 21:1-46

Shigar mai nasara

(Markus 11.1-11; Luka 19.28-38; Yohanna 12.12-19)

1Da suka yi kusa da Urushalima suka kuma kai Betfaji da yake kan Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajirai biyu, 2yana ce musu, “Ku je ƙauyen da yake gabanku, nan take za ku ga wata jaka a daure tare da ɗanta kusa da ita, a can. Ku kunce su ku kawo mini. 3In wani ya yi muku wata magana, ku ce masa Ubangiji yana bukatarsu, zai kuwa mai da su nan da nan.”

4Wannan ya faru ne don a cika abin da aka faɗa ta bakin annabin cewa,

5“Ku ce wa Diyar Sihiyona,

‘Duba, sarkinki yana zuwa gare ki,

mai tawali’u yana a kan jaki,

a kan aholaki, ɗan jaki.’ ”21.5 Zak 9.9

6Almajiran suka tafi suka yi kamar yadda Yesu ya umarce su. 7Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa mayafansu a kansu, Yesu kuma ya zauna a kansu. 8Wani babban taron mutane suka shimfiɗa mayafansu a kan hanya, yayinda waɗansu suka sassari rassan itatuwa suka shisshimfiɗa a kan hanya. 9Taron mutanen da suke gabansa da kuma waɗanda suke binsa a baya suka yi ihu suna cewa,

“Hosanna21.9 Wani faɗi na Ibraniyanci mai ma’anar “Ceto!” Wanda ya kasance wani salon yabo; haka kuma a aya 15 ga Ɗan Dawuda!”

“Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!”21.9 Zab 118.26

“Hosanna a cikin sama!”

10Sa’ad da Yesu ya shiga Urushalima, dukan birnin ya ruɗe, ana ta tambaya, “Wane ne wannan?”

11Taron mutane suka amsa, “Wannan shi ne Yesu, annabin nan daga Nazaret a Galili.”

Yesu a haikali

(Markus 11.15-19; Luka 19.45-48; Yohanna 2.13-22)

12Yesu ya shiga filin haikali, ya kuma kori duk masu saya da sayarwa a can. Ya tutture tebur masu canjin kuɗi da kuma kujerun masu sayar da tattabarai. 13Ya ce musu, “A rubuce yake, ‘Za a ce da gidana, gidan addu’a,’21.13 Ish 56.7 amma kuna mai da shi ‘kogon ’yan fashi.’ ”21.13 Irm 7.11

14Makafi da guragu suka zo wurinsa a haikali, ya kuwa warkar da su. 15Amma da manyan firistoci da malaman dokoki suka ga abubuwan banmamakin da ya yi, yara kuma suna ihu a filin haikali suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda,” sai fushi ya kama su.

16Suka tambaye shi suka ce, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?”

Yesu ya amsa ya ce, “I, ba ku taɓa karanta ba cewa,

“ ‘Daga leɓunan yara da jarirai

kai, Ubangiji, ka shirya wa kanka yabo’?”21.16 Zab 8.2

17Sai ya bar su, ya fita daga birnin ya tafi Betani, inda ya kwana.

Itacen ɓaure ya yanƙwane

(Markus 11.12-14,20-24)

18Kashegari da sassafe, yayinda yake kan hanyarsa ta komawa cikin birni, sai ya ji yunwa. 19Ganin itacen ɓaure kusa da hanya, sai ya je wajensa amma bai sami kome a kansa ba sai ganye. Sai ya ce masa, “Kada ka ƙara yin ’ya’ya!” Nan da nan itacen ya yanƙwane.

20Sa’ad da almajiran suka ga haka, sai suka yi mamaki suna tambaya, “Yaya itacen ɓauren ya yanƙwane nan da nan haka?”

21Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, ‘Je ka, ka jefa kanka cikin teku,’ sai yă faru. 22In kun gaskata, za ku karɓi duk abin da kuka roƙa a cikin addu’a.”

An tuhumi ikon Yesu

23Sai Yesu ya shiga filin haikali, yayinda yake koyarwa, sai manyan firistoci da dattawan mutane suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Da wane iko kake yin waɗannan abubuwa? Kuma wa ya ba ka wannan iko?”

24Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku tambaya guda. In kuka ba ni amsa, ni ma zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa. 25Baftismar Yohanna, daga ina ta fito? Daga sama ce, ko daga mutane?”

Sai suka tattauna a junansu suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama,’ zai ce, ‘To, me ya sa ba mu gaskata shi ba?’ 26In kuma muka ce, ‘Daga mutane,’ muna tsoron mutane, gama duk sun ɗauka Yohanna annabi ne.”

27Saboda haka suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.”

Sai ya ce, “Ni ma ba zan gaya muku ko da wane iko nake yin waɗannan abubuwa ba.”

Misalin ’ya’ya biyu maza

28“Me kuka gani? An yi wani mutum wanda yake da ’ya’ya biyu maza. Sai ya je wajen ɗan farin ya ce, ‘Ɗana, yau tafi gonar inabi ka yi aiki.’

29“Ya amsa ya ce, ‘Ba zan tafi ba,’ amma daga baya ya sāke tunani, ya tafi.

30“Sai mahaifin ya tafi waje na biyun ya faɗa masa iri magana guda. Sai ya amsa ya ce, ‘Zan tafi, ranka yă daɗe,’ amma bai tafi ba.

31“Wanne cikin yaran nan biyu ya yi abin da mahaifinsa yake so?”

Suka amsa, “Na farin.”

Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga mulkin Allah. 32Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”

Misalin ’yan haya

(Markus 12.1-12; Luka 20.9-19)

33“Ku saurari wani misali. An yi wani mai gona wanda ya yi gonar inabi. Ya kewaye ta da katanga, ya haƙa wurin matsin inabi a ciki, ya kuma gina hasumiyar gadi. Sa’an nan ya ba wa waɗansu manoma hayar gonar inabin, ya kuma yi tafiya. 34Da lokacin girbi ya yi kusa, sai ya aiki bayinsa wajen ’yan hayan, su karɓo masa ’ya’yan inabi.

35“Amma ’yan hayan suka kama bayinsa; suka dūke ɗaya, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi na ukun. 36Sai ya sāke aiken waɗansu bayi wurinsu, fiye da na dā yawa, amma ’yan hayan suka yi musu kamar yadda suka yi wa na farin. 37A ƙarshe, sai ya aiki ɗansa a wurinsu. Ya ce, ‘Za su girmama ɗana.’

38“Amma da ’yan hayan suka hangi ɗan, sai suka ce wa juna, ‘Wannan shi ne magājin. Ku zo, mu kashe shi, mu ci gādonsa.’ 39Saboda haka suka kama shi, suka jefar da shi bayan katangar gonar inabin, suka kashe shi.

40“To, idan mai gonar inabin ya zo, me zai yi da ’yan hayan nan?”

41Suka amsa suka ce, “Zai yi wa banzan mutanen nan mugun kisa, yă ba da hayar gonar inabin ga waɗansu ’yan haya, waɗanda za su ba shi rabonsa na amfanin gona a lokacin girbi.”

42Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karanta a cikin Nassi cewa,

“ ‘Dutsen da magina suka ƙi shi

ne ya zama dutsen kusurwar gini.

Ubangiji ne ya aikata wannan,

kuma abin mamaki ne a idanunmu’?21.42 Zab 118.22,23

43“Saboda haka, ina gaya muku cewa za a karɓe mulkin Allah daga gare ku, a ba wa mutanen da za su ba da amfani. 44Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Amma duk wanda dutsen nan ya fāɗi a kansa, za a murƙushe shi.”21.44 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā ba su da aya 44.

45Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan Yesu, sai suka gane cewa da su yake. 46Suka nemi hanyar kama shi, amma suka ji tsoron taron, don mutane sun ɗauka shi annabi ne.

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

馬太福音 21:1-46

光榮進聖城

1耶穌和門徒離耶路撒冷越來越近了,他們來到橄欖山旁的伯法其2耶穌派兩個門徒進村,並對他們說:「你們到前面的村莊去,就會看見一頭母驢拴在那裡,旁邊還有一頭驢駒。你們把牠們解開,牽到我這裡。 3要是有人問起,你們就說,『主要用牠們』,那人會立刻讓你們牽來。」 4這件事是要應驗先知的話:

5「要對錫安21·5 」希伯來文是「女子」,可能是對錫安的暱稱。說,『看啊,你的君王來了!祂謙卑地騎著驢,騎著一頭驢駒。』」

6兩個門徒照著耶穌的吩咐去了, 7把母驢和驢駒帶了回來。他們把自己的衣服蓋在驢背上,讓耶穌騎上去。 8許多人把衣服鋪在路上,也有些人砍下樹枝鋪在路上。 9眾人前呼後擁,歡呼著說:

「和散那21·9 和散那」原意是「拯救我們」,此處有「讚美」的意思。歸於大衛的後裔!

奉主名來的當受稱頌!

和散那歸於至高之處的上帝!」

10耶穌進耶路撒冷時,全城轟動,說:「這是誰?」

11眾人說:「祂是先知耶穌,來自加利利拿撒勒。」

潔淨聖殿

12耶穌進入聖殿,趕走裡面做買賣的人,又推翻兌換錢幣之人的桌子和賣鴿子之人的凳子。

13耶穌斥責他們說:「聖經上說,『我的殿必稱為禱告的殿。』你們竟把它變成了賊窩。」

14殿中的瞎子和瘸子都來到耶穌面前,祂便醫好了他們。 15祭司長和律法教師看見祂所行的奇事,又聽見小孩子在聖殿裡高聲喊著:「和散那歸於大衛的後裔!」便十分惱怒。 16他們責問耶穌說:「你聽見這些人說的了嗎?」

耶穌說:「我聽見了。聖經上說,『你使孩童和嬰兒口中發出頌讚』,你們沒有讀過嗎?」 17然後,祂便離開他們,出城前往伯大尼,在那裡住宿。

咒詛無花果樹

18清早,耶穌在回城的途中餓了。 19祂看見路旁有一棵無花果樹,便走過去,卻發現除了葉子外什麼也沒有。

祂對那棵樹說:「你將再不會結果子!」那棵樹立刻枯萎了。

20門徒見了就驚奇地問:「這棵樹怎麼一下子枯萎了?」

21耶穌回答說:「我實在告訴你們,如果你們有信心、不懷疑,不但能使無花果樹枯乾,就算對這座山說,『從這裡挪開,投進大海裡!』也照樣可以實現。 22所以,你們禱告時無論求什麼,只要有信心,就必定得到。」

質問耶穌的權柄

23耶穌進了聖殿,正在教導人的時候,祭司長和民間的長老來質問祂:「你憑什麼權柄做這些事?誰授權給你了?」

24耶穌說:「我也要問你們一個問題,你們回答了,我就告訴你們我憑什麼權柄做這些事。 25約翰的洗禮是從哪裡來的?從天上來的,還是從人來的?」

他們便彼此議論說:「如果我們說『是從天上來的』,祂一定會問我們,『那你們為什麼不信他?』 26但如果我們說『是從人來的』,又怕觸怒百姓,因為他們相信約翰是個先知。」 27於是,他們回答耶穌說:「我們不知道。」

耶穌說:「我也不告訴你們我憑什麼權柄做這些事。」

兩個兒子的比喻

28耶穌又說:「你們怎樣看這件事?某人有兩個兒子。他對大兒子說,『孩子,你今天到葡萄園工作吧!』

29「大兒子回答說,『我不去!』但後來他改變了主意,就去了。

30「那父親又對小兒子說,『你今天到葡萄園工作吧!』小兒子回答說,『好的,父親。』他答應了,卻沒有去。

31「你們認為這兩個兒子,到底哪一個服從父親呢?」

他們回答道:「大兒子。」

耶穌說:「我實在告訴你們,稅吏和娼妓要比你們先進上帝的國。 32因為約翰來指示你們當行的正路,你們不信他,但稅吏和娼妓信了。你們親眼看見了這些事,竟然還是執迷不悟,不肯信他。

惡毒的佃戶

33「你們再聽一個比喻。有個園主栽種了一個葡萄園,在園子的四周建造圍牆,又在園中挖了一個榨酒池,建了一座瞭望臺,然後把葡萄園租給佃戶,就出遠門了。 34到了收穫的季節,園主派奴僕到佃戶那裡收果子。 35但那些佃戶卻抓住他的奴僕,打傷一個,殺死一個,又用石頭打死了一個。 36於是,園主又派更多的奴僕去,結果也遭到同樣的對待。 37最後,園主派了自己的兒子去,心想,『他們肯定會尊重我的兒子。』 38然而,那些佃戶看見園主的兒子來了,就商量說,『這是園主的繼承人。來吧!我們殺掉他,佔了他的產業!』 39於是,他們抓住他,把他推出園外殺了。 40那麼,當園主回來的時候,他會怎樣處置那些佃戶呢?」

41他們說:「他會毫不留情地除掉那些惡人,然後把葡萄園租給其他按時交果子的佃戶。」

42耶穌說:

「『工匠丟棄的石頭已成了房角石。

這是主的作為,在我們看來奇妙莫測。』

你們難道沒有讀過這段經文嗎? 43所以,我告訴你們,將把上帝的國從你們那裡奪去,賜給結果子的人。 44凡跌在這石頭上的人,一定粉身碎骨;這石頭落在誰身上,就會把誰砸爛。」

45祭司長和法利賽人聽了耶穌的比喻,明白是針對他們講的。 46他們試圖逮捕耶穌,但又害怕百姓,因為百姓都認為耶穌是先知。