Mattiyu 17 – HCB & CCB

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 17:1-27

Sākewar kamanni

(Markus 9.2-13; Luka 9.28-36)

1Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗan’uwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. 2A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya. 3Nan take sai ga Musa da Iliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

4Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku, ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Iliya.”

5Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

6Sa’ad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice. 7Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.

9Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an tā da Ɗan Mutum daga matattu.”

10Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Iliya ya fara zuwa?”

11Yesu ya amsa ya ce, “Tabbatacce, Iliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa. 12Amma ina faɗa muku, Iliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.” 13Sa’an nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne.

Warkarwar yaro mai aljani

(Markus 9.14-29; Luka 9.37-43)

14Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. 15Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. 16Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”

17Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.” 18Yesu ya tsawata wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.

19Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”

20Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”17.20 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da kai. 21 Amma irin wannan ba ya fita, sai da addu’a da azumi

(Markus 9.30-32; Luka 9.43-45)

22Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane. 23Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki.

Harajin haikali

24Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne17.24 da Girik darik biyu?”

25Ya amsa ya ce “I, yana biya.”

Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji, daga wurin ’ya’yansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”

26Bitrus ya amsa ya ce, “Daga wurin waɗansu.”

Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ’ya’yan ke nan. 27Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

马太福音 17:1-27

登山变象

1六天后,耶稣带着彼得雅各雅各的兄弟约翰暗暗地登上一座高山。 2耶稣在他们面前改变了形象,面貌如太阳一样发光,衣服洁白如光。 3忽然,摩西以利亚一起出现,跟耶稣谈话。 4彼得对耶稣说:“主啊,我们在这里好极了。如果你愿意,我就在这里搭三座帐篷,一座给你,一座给摩西,一座给以利亚。”

5他正在说话的时候,一朵灿烂的云彩笼罩他们。云中传出声音:“这是我的爱子,我甚喜悦祂,你们要听从祂。”

6门徒听见这声音,便俯伏在地,非常惧怕。 7耶稣就过来摸他们,说:“起来吧,别害怕。” 8他们抬起头来,看见只剩下耶稣一个人。

9下山时,耶稣叮嘱他们:“人子还没有从死里复活以前,不要把刚才看见的告诉别人。”

10门徒问耶稣:“律法教师为什么说以利亚必须先来?”

11耶稣回答说:“以利亚的确要来,他将复兴一切。 12但我告诉你们,以利亚已经来了,人们却不认识他,甚至还任意对待他。人子同样也会在他们手下受苦。” 13门徒这才明白耶稣所说的是指施洗者约翰

治好被鬼附身的孩子

14他们回到山下众人聚集的地方。有一个人过来跪在耶稣跟前,说: 15“主啊!救救我的儿子吧!他患了癫痫症,痛苦极了,曾经几次跌进火中,掉进水里。 16我带他去见你的门徒,但他们却不能治好他。”

17耶稣说:“唉!这世代又不信又败坏的人啊,我要跟你们在一起待多久?我要容忍你们多久呢?把他带来吧。” 18耶稣斥责附在孩子身上的鬼,鬼就离开了那孩子,从此他就好了。

19事后,门徒私下问耶稣:“我们为什么赶不走那鬼呢?”

20耶稣说:“你们的信心太小了。我实在告诉你们,你们若有像芥菜种那样大的信心,就算叫这座山从这里移到那里,它也会移开,你们将没有办不到的事。 21至于这一类的鬼,你们必须祷告和禁食才能把它赶走。”

耶稣第二次预言受害和复活

22他们聚集在加利利的时候,耶稣对他们说:“人子将要被出卖,交在人手里。 23他们将杀害祂,第三天祂将复活。”门徒听了,十分忧愁。

从鱼口得税钱

24他们来到迦百农,有几个收圣殿税的来问彼得:“你们的老师不纳圣殿税吗?”

25彼得说“纳!”他进了屋,还没开口,耶稣便问他:“西门,你有何看法?世上的君王向谁征收赋税?向自己的儿子呢,还是向外人呢?”

26彼得答道:“向外人。”

耶稣说:“所以儿子不用纳税。 27但为了避免得罪这些人,你就去湖边钓鱼,把钓上来的第一条鱼的嘴打开,里面有一个钱币,拿它去缴你我的税好了。”