Mattiyu 16 – HCB & CCBT

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 16:1-28

Neman alama

(Markus 8.11-13; Luka 12.54-56)

1Farisiyawa da Sadukiyawa suka zo don su gwada Yesu ta wurin neman yă nuna musu wata alama daga sama.

2Ya amsa ya ce,16.2 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko ba su da raguwar aya 2 da kuma dukan aya 3 “Sa’ad da yamma ta yi, kukan ce, ‘Yanayi zai yi kyau, gama sararin sama ya yi ja,’ 3da safe kuma, ku ce, ‘Yau kam za a yi hadari, gama sararin sama ya yi ja, ya kuma ɓata fuska.’ Kun san yadda za ku fassara yanayin sararin sama, amma ba kwa iya fassarar alamun lokuta. 4Wannan mugu da mazinacin zamani yana neman wani abin banmamaki, amma ba wata alamar da za a nuna wa wannan zamani sai dai ta Yunana.” Sai Yesu ya bar su ya tafi abinsa.

Yistin Farisiyawa da Sadukiyawa

(Markus 8.14-21)

5Da suka ƙetare tafkin, almajiran sun manta su riƙe burodi. 6Yesu ya ce musu, “Ku yi hankali, ku yi taka zallan da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.”

7Sai suka fara tattaunawa da junansu suna cewa, “Ko don ba mu kawo burodi ba ne.”

8Sane da abin da suke zance, sai Yesu ya ce, “Ku masu ƙarancin bangaskiya, don me kuke magana da junanku a kan ba ku zo da burodi ba? 9Har yanzu ba ku gane ba ne? Ba ku tuna da gurasa biyar ɗin nan na mutum dubu biyar ba? Kwando nawa kuka tattara cike? 10Ko kuma burodi bakwai nan na mutum dubu huɗu, cikakku manyan kwanduna nawa kuka ɗauka? 11Yaya kuka kāsa gane cewa ba zancen burodi nake yi ba? Sai dai ku yi hankali da yistin Farisiyawa da Sadukiyawa.” 12Sa’an nan suka gane ba cewa yake musu su yi hankali da yistin da ake amfani da shi a burodi ba ne, sai dai su yi hankali da koyarwar Farisiyawa da Sadukiyawa ne.

Shaidar Bitrus a kan Kiristi

(Markus 8.27-30; Luka 9.18-21)

13Sa’ad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, “Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?”

14Suka amsa, “Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Iliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa.”

15Ya tambaye su, “Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?”

16Siman Bitrus ya amsa ya ce, “Kai ne Kiristi,16.16 Ko kuwa a Almasihu; haka ma a aya 20 Ɗan Allah mai rai.”

17Yesu ya amsa ya ce, “Mai albarka ne kai Siman ɗan Yunana, gama ba mutum ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin sama. 18Ina kuwa gaya maka, kai ne Bitrus,16.18 Bitrus yana nufin dutse. a kan wannan dutse zan gina ikkilisiyata, kuma ƙofofin Hades16.18 Ko kuwa a lahira ba za su rinjaye ta ba. 19Zan ba ka mabuɗan mulkin sama; kome ka daure a duniya zai zama a daure a sama, kome kuma ka kunce a duniya zai zama a kunce a sama.” 20Sa’an nan ya gargaɗe almajiransa cewa kada su faɗa wa kowa shi ne Kiristi.

Yesu ya yi zancen mutuwarsa

(Markus 8.31–9.1; Luka 9.22-27)

21Tun daga wannan lokaci Yesu ya fara bayyana wa almajiransa cewa dole yă tafi Urushalima yă sha wahaloli da yawa a hannun dattawa, manyan firistoci da kuma malaman dokoki, dole a kashe shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.

22Bitrus ya ja shi gefe ya fara tsawata masa yana cewa, “Sam, Ubangiji! Wannan ba zai taɓa faruwa da kai ba!”

23Yesu ya juya ya ce wa Bitrus, “Rabu da ni, Shaiɗan! Kai abin sa tuntuɓe ne a gare ni; ba ka tunanin al’amuran Allah, sai dai al’amuran mutane.”

24Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa, yă bi ni. 25Gama duk mai son ceton ransa zai rasa shi, amma duk wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi. 26Me mutum zai amfana in ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa? Ko kuwa me mutum zai bayar a bakin ransa? 27Gama Ɗan Mutum zai zo cikin ɗaukakar Ubansa, tare da mala’ikunsa, sa’an nan zai ba wa kowane mutum lada gwargwadon abin da ya yi.

28“Gaskiya nake gaya muku, akwai waɗansu da suke tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin mulkinsa.”

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

馬太福音 16:1-28

求神蹟

1有幾個法利賽人和撒都該人來試探耶穌,要求祂顯個天上的神蹟給他們看。

2耶穌回答說:「傍晚的時候,你們看見天邊出現紅霞,就說明天一定是晴天; 3早晨的時候,你們看見天色又紅又暗,就說今天必有風雨。你們懂得分辨天色,卻不能分辨時代的徵兆。 4一個邪惡淫亂的世代想看神蹟,可是除了約拿的神蹟以外,再沒有神蹟給他們看。」於是耶穌離開他們走了。

防備法利賽人和撒都該人的酵

5門徒渡到湖對岸,忘記帶餅了。 6耶穌對他們說:「你們要小心提防法利賽人和撒都該人的酵。」

7門徒彼此議論說:「這是因為我們沒有帶餅吧。」

8耶穌知道他們的心思,就說:「你們的信心太小了!為什麼議論沒有帶餅的事呢? 9你們還不明白嗎?你們不記得那五個餅讓五千人吃飽,又裝滿多少籃子嗎? 10也不記得那七個餅給四千人吃飽,又裝滿多少筐子嗎? 11我說你們要提防法利賽人和撒都該人的酵,指的不是餅,你們怎麼不明白呢?」

12門徒這才恍然大悟,知道耶穌不是叫他們當心什麼麵酵,而是要提防法利賽人和撒都該人的教導。

彼得宣告耶穌是基督

13到了凱撒利亞·腓立比境內,耶穌問門徒:「人們說人子是誰?」

14門徒回答說:「有人說是施洗者約翰,有人說是以利亞,也有人說是耶利米,或其他某位先知。」

15耶穌問:「那麼,你們說我是誰?」

16西門·彼得回答說:「你是基督,是永活上帝的兒子!」

17耶穌對他說:「約拿的兒子西門啊,你是有福的!因為這件事不是屬血肉的人告訴你的,而是我天上的父啟示你的。 18我告訴你,你是彼得16·18 彼得」希臘文是「磐石」的意思。,我要在這磐石上建立我的教會,陰間的勢力16·18 勢力」希臘文是「門」。不能勝過它。 19我要把天國的鑰匙交給你。凡你在地上捆綁的,在天上也要捆綁;凡你在地上釋放的,在天上也要釋放。」

20當下,耶穌叮囑門徒不可告訴別人祂就是基督。

耶穌預言自己的受害和復活

21從此以後,耶穌開始清楚地指示門徒,祂必須去耶路撒冷,受長老、祭司長和律法教師許多的迫害,並且被處死,但第三天必從死裡復活。 22彼得把耶穌拉到一邊,勸阻祂說:「主啊,千萬不可!這件事絕不會發生在你身上!」

23耶穌立刻轉過身來責備彼得說:「撒旦,退到我後面去!你是我的絆腳石,因為你不考慮上帝的意思,只考慮人的意思。」

24於是耶穌對門徒說:「如果有人要跟從我,就應當捨己,背起他的十字架跟從我。 25因為想救自己生命的,必失去生命;但為了我而失去生命的,必得到生命。 26人若賺得全世界,卻喪失自己的生命,又有什麼益處呢?人還能拿什麼換回自己的生命呢?

27「因為人子要在祂父的榮耀裡與眾天使一起降臨,那時,祂將按照各人的行為報應各人。 28我實在告訴你們,有些站在這裡的人會在有生之年看見人子降臨在祂的國度裡。」