Mattiyu 13 – HCB & KLB

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 13:1-58

Misalin mai shuka

(Markus 4.1-9; Luka 8.4-8)

1A ranan nan sai Yesu ya fita daga gida ya je ya zauna a bakin tafkin. 2Taron mutane mai yawan gaske suka taru kewaye da shi har ya kai sai da ya shiga jirgin ruwa ya zauna, yayinda dukan mutane suka tsaya a gaci. 3Sa’an nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa, “Wani manomi ya fita don yă shuka irinsa. 4Da yana yafa irin, waɗansu suka fāffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su. 5Waɗansu suka fāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi. 6Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai. 7Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su. 8Har yanzu, waɗansu irin suka fāffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka. 9Duk mai kunnen ji, yă ji.”

(Markus 4.10-12; Luka 8.9,10)

10Almajiran suka zo wurinsa suka tambaye shi, “Me ya sa kake wa mutane magana da misalai?”

11Ya amsa ya ce, “Sanin asirin mulkin sama kam, ku aka ba wa, amma su ba a ba su ba. 12Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, zai kuwa samu a yalwace. Duk wanda kuma ba shi da shi, ko ɗan abin da yake da shi ma, za a karɓe. 13Abin da ya sa nake musu magana da misalai ke nan.

“Ko da yake suna kallo, ba sa gani;

ko da yake suna saurara, ba sa ji ko su gane.

14A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa,

“ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba;

za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.

15Gama zuciyar mutanen nan ta taurare;

da ƙyar suke ji da kunnuwansu,

sun kuma rufe idanunsu.

Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu,

su kuma ji da kunnuwansu,

su gane a zuciyarsu,

su kuwa juya, in kuma warkar da su.’13.15 Ish 6.9,10

16Amma idanunku masu albarka ne domin suna gani, haka ma kunnuwanku domin suna ji. 17Gama gaskiya nake gaya muku, annabawa da mutane masu adalci da yawa sun yi marmarin ganin abin da kuke gani amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji amma ba su ji ba.

(Markus 4.13-20; Luka 8.11-15)

18“To, ku saurari ma’anar misali na mai shukan nan. 19Duk sa’ad da wani ya ji saƙo game da mulkin bai kuwa fahimce shi ba, mugun nan yakan zo yă ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya. 20Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yă karɓe ta da murna. 21Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yă ja da baya. 22Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarrabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yă sa maganar ta kāsa amfani. 23Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yă kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”

Misalin ciyayi

24Yesu ya ba su wani misali. “Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa. 25Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa. 26Sa’ad da alkamar ta tashi ta yi kawuna, sai ciyayin ma suka bayyana.

27“Bayin mai gonar suka zo wurinsa suka ce, ‘Ranka yă daɗe, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, ina ciyayin nan suka fito?’

28“Sai ya ce, ‘Abokin gāba ne ya yi wannan.’

“Bayin suka tambaye shi suka ce, ‘Kana so mu je mu tuttumɓuke su?’

29“Ya amsa ya ce, ‘A’a, don kada garin tuttumɓuke ciyayi, ku cire har da alkamar. 30Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi, da fari ku tara ciyayin ku kuma daure su dami-dami don a ƙone; sa’an nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ ”

Misalai na ƙwayar mustad da na yisti

(Markus 4.30-32; Luka 13.18-21)

31Ya ba su wani misali ya ce, “Mulkin sama yana kama da ƙwayar mustad, wadda mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa. 32Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta cikin ƙwayoyinku, duk da haka sa’ad da ta yi girma, takan zama mafi girma cikin tsire-tsiren lambu ta kuma zama itace, har tsuntsayen sararin sama su zo su yi sheƙa a rassansa.”

33Har yanzu ya ba su wani misali ya ce, “Mulkin sama yana kama da yisti wanda mace ta ɗauka ta kwaɓa garin alkama mai yawa, har sai da yistin ya gauraye yistin duka.”

(Markus 4.33,34)

34Yesu ya faɗa wa taron dukan waɗannan abubuwa cikin misalai; bai faɗa musu kome ba, sai tare da yin amfani da misalai. 35Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta wurin annabi cewa,

“Zan buɗe bakina da misalai,

zan faɗi abubuwan da suke ɓoye tun halittar duniya.”13.35 Zab 78.2

An bayyana misali na ciyayi

36Sa’an nan ya bar taron ya shiga gida. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa suka ce, “Bayyana mana misalin ciyayin nan a gona.”

37Ya amsa ya ce, “Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum. 38Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ’ya’yan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ’ya’yan mugun nan, 39abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne mala’iku.

40“Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani. 41Ɗan Mutum zai aiki mala’ikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta. 42Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora. 43Sa’an nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

Misalai na ɓoyayyiyar dukiya da na lu’ulu’u

44“Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yă sāke ɓoye ta, sa’an nan cikin farin cikinsa yă je yă sayar da duk abin da yake da shi yă sayi gonar.

45“Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman lu’ulu’ai masu kyau. 46Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.

Misalin taru

47“Har yanzu, mulkin sama yana kama da abin kamun kifin da aka jefa cikin tafki yă kamo kifi iri-iri. 48Da abin kamun kifi ya cika, masuntan suka jawo shi gaci. Sai suka zauna suka tattara kifi masu kyau a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau. 49Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Mala’iku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci 50su kuma jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

51Yesu ya tambaye su ya ce, “Kun gane dukan waɗannan abubuwa?”

Suka amsa, “I.”

52Sa’an nan ya ce musu, “Saboda haka duk malamin dokokin da ya horu game da koyarwar mulkin sama, yana kama da maigida wanda yakan fitar daga ɗakin ajiyarsa sababbin dukiya da kuma tsofaffi.”

Rashin ganin darajar annabi

(Markus 6.1-6; Luka 4.16-30)

53Sa’ad da Yesu ya gama ba da waɗannan misalai, sai ya ci gaba daga can. 54Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majami’arsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka? 55Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba? 56Duk ’yan’uwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?” 57Sai suka ji haushinsa.

Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”

58Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.

Korean Living Bible

마태복음 13:1-58

하늘 나라의 비유

1그 날 예수님은 집에서 나와 바닷가에 가서 앉으셨다.

2너무 많은 군중이 모여들므로 예수님은 배에 올라 앉으시고 그들은 물가에 서 있었다.

3그때 예수님은 여러 가지 비유를 들어 그들에게 많은 것을 말씀하셨다. “한 농부가 들에 나가

4씨를 뿌렸다. 그런데 어떤 씨는 길가에 떨어져서 새들이 와서 먹어 버렸고

5어떤 씨는 흙이 많지 않은 돌밭에 떨어져 흙이 깊지 않으므로 곧 싹이 나왔으나

6해가 돋자 뿌리를 박지 못한 싹은 타서 말라 버렸다.

7또 어떤 씨는 가시덤불에 떨어졌는데 가시나무가 자라 그 기운을 막았다.

8그러나 어떤 씨는 좋은 땅에 떨어져 100배, 60배, 30배의 열매를 맺었다.

9귀 있는 사람은 잘 들어라.”

10제자들이 예수님께 와서 “저 사람들에게는 왜 비유로 말씀하십니까?” 하고 묻자

11예수님은 이렇게 대답하셨다. “너희에게는 하늘 나라의 비밀을 아는 것이 허락되었으나 저 사람들에게는 허락되지 않았다.

12있는 사람에게는 더 주어 넘치게 하고 없는 사람은 가진 것까지도 빼앗길 것이다.

13저들은 보아도 알지 못하고 들어도 깨닫지 못하므로 나는 저들에게 비유로 말한다.

14그래서 다음과 같은 이사야의 예언은 저들에게 꼭 들어맞는 말이다. 13:14 사6:9, 10, 10‘너희는 계속 들어도 깨닫지 못하고 계속 보아도 알지 못한다.

15이 백성은 마음이 둔해졌고 귀는 먹었으며 눈까지 멀었다. 그렇지 않으면 그들이 눈으로 보고 귀로 듣고 마음으로 깨달아 돌아와서 나에게 고침을 받을지도 모른다.’

16“그러나 너희는 눈으로 보고 귀로 들을 수 있으니 행복하다.

17내가 분명히 말한다. 많은 예언자들과 의로운 사람들이 너희가 보는 것을 보고 싶어했으나 보지 못하였고 너희가 듣는 것을 듣고 싶어했으나 듣지 못하였다.

18“너희는 씨 뿌리는 사람에 대한 비유의 뜻을 들어 보아라.

19누구든지 하늘 나라의 말씀을 듣고도 깨닫지 못하면 13:19 원문에는 ‘악한 자’사탄이 와서 그 마음에 뿌려진 것을 빼앗아 가 버린다. 이런 사람은 길가에 떨어진 씨와 같은 사람이다.

20그리고 돌밭에 떨어진 씨는 말씀을 들을 때 기뻐하며 즉시 받아들이지만

2113:21 또는 ‘그 속에 뿌리가 없어’그것을 마음속 깊이 간직하지 못하고 잠시 견디다가 그 말씀 때문에 고통이나 핍박이 오면 곧 넘어지는 사람이다.

22또 가시덤불 속에 떨어진 씨는 말씀은 듣지만 이 세상 걱정과 재물에 대한 유혹 때문에 말씀대로 생활하지 못하는 사람을 말한다.

23그러나 좋은 땅에 뿌려진 씨는 말씀을 듣고 깨닫는 사람을 가리킨다. 그런 사람은 100배, 60배, 또는 30배의 열매를 맺는다.”

24예수님은 또 다른 비유를 들어 그들에게 말씀하셨다. “하늘 나라는 자기 밭에 좋은 씨앗을 뿌린 사람에 비할 수 있다.

25사람들이 다 잠들었을 때 원수가 와서 밀밭에 13:25 또는 ‘가라지’독보리를 덧뿌리고 갔다.

26밀이 싹터서 자랄 때 독보리도 함께 자라는 것을 보고

27종들이 주인에게 와서 ‘주인님, 밭에 좋은 씨앗을 뿌리지 않았습니까? 그런데 독보리가 어디서 생겨났습니까?’ 하고 물었다.

28그러자 주인은 ‘원수가 이런 짓을 했구나’ 하고 대답하였다. 종들이 ‘그러면 우리가 가서 독보리를 뽑아 버릴까요?’ 하고 다시 묻자

29주인은 이렇게 말하였다. ‘아니다. 독보리를 뽑다가 밀까지 뽑을까 걱정된다.

30추수 때까지 둘 다 함께 자라도록 그냥 두어라. 추수 때에 내가 추수꾼들에게 먼저 독보리를 뽑아 단으로 묶어서 불태워 버리고 밀은 내 곳간에 모아들이게 하겠다.’ ”

31예수님은 또 다른 비유로 그들에게 말씀하셨다. “하늘 나라는 어떤 사람이 자기 밭에 갖다 심은 겨자씨 한 알과 같다.

32그것은 씨앗 중에 가장 작은 것이지만 모든 채소보다 더 크게 자라나 나무처럼 되어서 새들이 날아와 그 가지에 깃들인다.”

33예수님은 또 다른 비유를 말씀하셨다. “하늘 나라는 어떤 여자가 13:33 헬 ‘세 사톤’ (약 22리터)한 포대의 밀가루에 섞어 전부 부풀게 한 누룩과 같다.”

34예수님은 군중에게 이 모든 것을 비유로만 말씀하시고 비유가 아니면 아무것도 말씀하지 않으셨다.

35이것은 다음과 같은 예언자의 예언을 이루기 위해서였다. 13:35 시78:2“내가 비유를 들어 세상이 창조될 때부터 감추어진 것을 말하겠다.”

36그 후 예수님이 군중과 헤어져 집에 들어가 있을 때 제자들이 와서 “밭의 독보리 비유를 자세히 설명해 주십시오” 하였다.

37그래서 예수님은 그들에게 이렇게 대답하셨다. “좋은 씨를 뿌리는 농부는 13:37 원문에는 ‘인자’ (사람의 아들)나 그리스도이며

38밭은 세상이다. 그리고 좋은 씨앗은 하늘 나라에 속한 사람들이고 독보리는 악한 자에게 속한 사람들이다.

39독보리를 뿌린 원수는 마귀이며 추수 때는 세상 끝날이고 추수꾼은 천사들이다.

40그러므로 독보리를 뽑아 불에 태우듯 세상 끝날에도 그렇게 할 것이다.

41내가 천사들을 보내겠다. 그들은 죄 짓게 하는 모든 사람과 악을 행하는 사람들을 내 나라에서 모두 추려내어

42불구덩이에 던져 넣을 것이다. 그러면 그 사람들이 거기서 통곡하며 이를 갈 것이다.

43그때 의로운 사람들은 아버지의 나라에서 해같이 빛날 것이다. 귀 있는 사람은 잘 들어라.

44“하늘 나라는 밭에 숨겨진 보물과 같다. 사람이 그것을 발견하면 다시 감추어 두고 기뻐하며 돌아가 가진 것을 다 팔아서 그 밭을 샀다.

45“또 하늘 나라는 아름다운 진주를 구하는 장사꾼과 같다.

46그가 아주 값진 진주 하나를 발견하고 가서 가진 것을 모두 팔아 그 진주를 샀다.

47“또 하늘 나라는 바다에 던져 여러 종류의 물고기를 모으는 그물과 같다.

48그물에 고기가 가득 차면 물가로 끌어내어 앉아서 좋은 것은 골라 그릇에 담고 나쁜 것은 버린다.

49세상 끝날에도 이렇게 할 것이다. 천사들이 와서 의로운 사람들 가운데서 악한 사람들을 가려내어

50불구덩이에 던져 넣을 것이다. 그러면 그들이 거기서 통곡하며 이를 갈 것이다.”

51말씀을 마치시고 예수님이 그들에게 “이 모든 것을 이제 알겠느냐?” 하고 물으시자 제자들은 “예, 알겠습니다” 하고 대답하였다.

52그러자 예수님은 그들에게 “그러므로 하늘 나라의 가르침을 받은 율법학자는 마치 자기 곳간에서 새 것과 낡은 것을 꺼내는 집 주인과 같다” 라고 하셨다.

목수의 아들이 아니냐

53예수님은 이 비유들을 다 말씀하시고 나서 그 곳을 떠나

54고향으로 가서 회당에서 가르치셨다. 사람들이 듣고 놀라 “이 사람의 이런 지혜와 기적을 행하는 능력이 어디서 났느냐?

55이 사람은 목수의 아들이 아니냐? 그의 어머니는 마리아이고 야고보와 요셉과 시몬과 유다는 그의 동생들이다.

56그리고 그의 누이동생들도 모두 우리와 함께 있지 않느냐? 그렇다면 이 사람은 이 모든 것을 어디서 얻었느냐?” 하면서

57예수님을 배척하였다. 그러나 예수님은 그들에게 “예언자는 자기 고향과 집에서만 존경을 받지 못한다” 하시고

58그들이 믿지 않으므로 거기서는 기적을 많이 베풀지 않으셨다.