Luka 23 – Hausa Contemporary Bible HCB

Hausa Contemporary Bible

Luka 23:1-56

(Mattiyu 27.1,2,11-14; Markus 15.1-5; Yohanna 18.28-38)

1Sai dukan majalisa suka tashi, suka kai shi gaban Bilatus. 2Suka fara zarginsa suna cewa, “Mun sami wannan mutum yana rikitar da al’ummarmu. Yana hana a biya haraji ga Kaisar. Yana kuma cewa, shi Kiristi ne, sarki kuma.”

3Sai Bilatus ya tambayi Yesu ya ce, “Kai ne sarkin Yahudawa?”

Yesu ya amsa ya ce, “I, haka yake, kamar yadda ka faɗa.”

4Sai Bilatus ya sanar wa manyan firistoci da taron ya ce, “Ni fa, ban sami wani ainihin abin zargi game wannan mutum nan ba.”

5Amma suka nace, suna cewa, “Yana tā da hankulan mutane, ko’ina a Yahudiya da koyarwarsa. Ya fara daga Galili, ga shi har ya kai nan.”

6Da Bilatus ya ji haka, sai ya yi tambaya, “Ko shi mutumin Galili ne?” 7Da ya ji cewa, Yesu yana ƙarƙashin mulkin Hiridus ne, sai ya aika da shi zuwa wurin Hiridus, don a lokacin Hiridus yana Urushalima.

8Da Hiridus ya ga Yesu, sai ya yi murna ƙwarai, don tun dā ma yana marmari ya gan shi a kan abin da ya ji game da shi. Ya yi fata ya ga Yesu, yă kuma yi waɗansu ayyukan banmamaki. 9Ya yi masa tambayoyi masu yawa, amma Yesu bai ba shi ko amsa ba. 10Manyan firistoci da malaman dokoki suna tsaye a wurin, suna kawo zargi masu ƙarfi a kansa. 11Sai Hiridus da sojojinsa suka wulaƙanta shi, suka yi masa ba’a. Sa’an nan, suka sa masa babban riga, suka mai da shi wurin Bilatus. 12A ranar, Hiridus da Bilatus suka zama abokan juna, don tun dā ma, su abokan gāba ne.

(Mattiyu 27.15-26; Markus 15.6-15; Yohanna 18.39–19.16)

13Bilatus ya tara manyan firistoci, da masu mulki, da mutane, 14ya ce musu, “Kun kawo mini wannan mutum, a matsayin wanda yana zuga mutane su yi tawaye. Na bincike shi a gabanku, ban ga a kan me kuka kawo kararsa ba. 15Haka ma Hiridus, shi ya sa ya dawo da shi nan wurinmu. Kamar yadda ku ma kun gani, ba abin da mutumin nan ya yi, da ya isa mutuwa. 16Saboda haka, zan yi masa bulala, in sāke shi.”23.16 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da 17 A lokacin idi kuwa lalle ne ya sakar musu ɗaurarre guda.

18Suka yi ihu gaba ɗaya suka ce, “A yi gaba da wannan mutum! A sake mana Barabbas!” 19(Barabbas yana kurkuku saboda laifin tā da hankali a birnin, da kuma don kisankai.)

20Sai Bilatus ya sāke yin musu magana don yana so ya saki Yesu. 21Amma sai suka ci gaba da ihu, suna cewa, “A gicciye shi! A gicciye shi!”

22Ya sāke ce musu, sau na uku, “Don me? Wane laifi wannan mutum ya yi? Ni dai ban same shi da wani dalilin da ya isa a kashe shi ba. Saboda haka, zan sa a hore shi, sa’an nan in sāke shi.”

23Amma suna ihu, suna nacewa, suna cewa, dole a gicciye shi, har ihunsu ya rinjaye shi. 24Sai Bilatus ya biya bukatarsu da ya ji roƙonsu. 25Ya saki mutumin da aka jefa a kurkuku saboda tā da hankali, da kisankai, shi wanda suka roƙa. Sa’an nan ya ba da Yesu ga nufinsu.

Gicciyewa

(Mattiyu 27.31-44; Markus 15.21-32; Yohanna 19.17-27)

26Sa’ad da suna tafiya da Yesu, sai wani da ake kira Siman, mutumin Sairin, yana zuwa daga ƙauye. Suka kama shi, suka aza masa gicciyen, suka tilasta shi ya ɗauki gicciyen, ya bi Yesu a baya. 27Mutane da yawa sosai suka bi shi, a cikinsu ma da mata waɗanda suka yi makoki da kuka dominsa. 28Yesu ya juya, ya ce musu, “’Yan matan Urushalima, kada ku yi kuka saboda ni, amma ku yi kuka saboda kanku, da kuma saboda ’ya’yanku. 29Gama lokaci yana zuwa da za ku ce, ‘Masu albarka ne bakararru, wato, mata marasa haihuwa, da mahaihuwar da ba su taɓa haihuwa ba, da kuma mama da ba su taɓa shayar da nono ba!’ 30Sa’an nan

“ ‘za su ce wa duwatsu,

“Ku fāɗi a kanmu!”

Za su ce wa tuddai kuma,

“Ku rufe mu!” ’23.30 Hos 10.8

31Gama in mutane suna yin waɗannan abubuwa a lokacin da itace na ɗanye, me zai faru in ya bushe?”

32Tare da shi akwai mutum biyu masu laifi, da aka tafi da su don a gicciye. 33Da suka isa wurin da ake kira “Ƙoƙon Kai,” nan suka gicciye shi, tare da masu laifin nan, ɗaya a hannun damansa, ɗayan kuma a hagunsa. 34Yesu ya ce, “Ya Uba ka yi musu gafara, don ba su san abin da suke yi ba.” Suka rarraba tufafinsa ta wurin jefa ƙuri’a.

35Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”

36Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami. 37Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”

38Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce,

Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.

39Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”

40Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi? 41Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”

42Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.”

43Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”

Mutuwar Yesu

(Mattiyu 27.45-56; Markus 15.33-41; Yohanna 19.28-30)

44Yanzu kuwa wajen sa’a ta shida ne, kuma duhu ya rufe ko’ina a ƙasar, har zuwa sa’a ta tara, 45domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu. 46Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.

47Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.” 48Da dukan mutanen da suka taru, domin shaidar waɗannan abubuwa, suka ga abin da ya faru, sai suka buga ƙirjinsu suka tafi. 49Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna kallon abubuwan nan.

Binne Yesu

(Mattiyu 27.57-61; Markus 15.42-47; Yohanna 19.38-42)

50Akwai wani mutum mai suna Yusuf, ɗan Majalisa, wanda shi nagari ne, mai adalci, 51shi dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba. Shi daga Arimateya ne wani garin Yahudiya. Yana kuma jiran zuwa mulkin Allah. 52Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu. 53Sai ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi a cikin zanen lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe a cikin dutse, wadda ba a taɓa sa kowa ba. 54An yi haka ne a Ranar Shirye-shirye, ranar Asabbaci kuma yana dab da farawa.

55Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin. 56Sa’an nan, suka koma gida, suka shirya kayan ƙanshi da turare. Amma suka huta a ranar Asabbaci don kiyaye doka.