Ibraniyawa 1 – HCB & CCBT

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 1:1-14

1A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri, 2amma a waɗannan kwanaki a ƙarshe ya yi magana da mu ta wurin Ɗansa, wanda ya naɗa magājin dukan abubuwa, wanda kuma ta wurinsa ya halicci duniya. 3Ɗan shi ne hasken ɗaukakar Allah, shi ne kuma ainihin kamanninsa, yana riƙe da dukan abubuwa ta wurin kalmarsa mai iko. Bayan ya yi tsarkakewa don zunubai, sai ya zauna a hannun daman Maɗaukaki a sama. 4Ta haka yake da fifiko a kan mala’iku kamar yadda sunan da ya gāda ya fi nasu fifiko.

Ɗan ya fi Mala’iku

5Gama ga wane daga cikin mala’ikun Allah ya taɓa cewa,

“Kai Ɗana ne;

yau na zama Uba a gare ka”1.5 Zab 2.7?

Ko kuwa,

“Zan zama Ubansa,

shi kuma zai zama Ɗana”1.5 2Sam 7.14; 1Tar 17.13?

6Haka kuma, sa’ad da Allah ya kawo ɗan farinsa a duniya ya ce,

“Bari dukan mala’ikun Allah su yi masa sujada.”

7Da yake magana game da mala’iku kuwa ya ce,

“Ya mai da mala’ikunsa iska,

bayinsa kuma harsunan wuta.”1.7 Zab 104.4

8Amma game da Ɗan ya ce,

“Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin,

adalci kuma zai zama sandan mulkinka.

9Ka ƙaunaci abin da yake daidai, ka kuma ƙi mugunta;

saboda haka Allah, Allahnka, ya ɗora ka a bisan abokan zamanka,

ta wurin shafan da ya yi maka da man farin ciki.”1.9 Zab 45.6,7

10Ya kuma ce,

“Tun da farko, ya Ubangiji, ka kafa tushen duniya,

sammai kuma aikin hannuwanka ne.

11Su za su hallaka, amma kai kana nan;

dukansu za su tsufa kamar riga.

12Za ka naɗe su kamar mayafi,

kamar riga za su sauya.

Amma kai ba za ka canja ba,

shekarunka kuma ba za su taɓa ƙarewa ba.”1.12 Zab 102.25-27

13Ga wane daga cikin mala’iku Allah ya taɓa cewa,

“Zauna a hannun damana,

sai na sa abokan gābanka

su zama matashin sawunka”1.13 Zab 110.1?

14Ashe, dukan mala’iku ba ruhohi masu hidima ba ne da aka aika don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

希伯來書 1:1-14

劃時代的啟示

1在古代,上帝曾藉著先知以各種方式多次向我們的祖先說話; 2在這世界的末期,祂又藉著自己的兒子親自向我們說話。上帝早已立祂承受萬物,並藉著祂創造了宇宙萬物。 3祂正是上帝榮耀的光輝,是上帝本體的真像。祂用自己充滿能力的話語維繫萬物。祂洗淨了世人的罪之後,便坐在天上至高上帝的右邊。 4祂既承受了比天使更高的名分,就遠超越天使。

5上帝從未對任何一個天使說:

「你是我的兒子,我今日成為你父親。」

或說:

「我要作你的父親,你要作我的兒子。」

6上帝差遣祂的長子到世上來時,說:

「上帝的天使都要敬拜祂。」

7上帝提到天使的時候,也只是說:

「上帝使祂的天使成為風,使祂的僕役成為火焰。」

8但論到祂的兒子,祂卻說:

「上帝啊,你的寶座永遠長存,

你以公義的杖執掌王權。

9你喜愛公義,憎惡邪惡。

所以上帝,你的上帝,

用喜樂之油膏你,使你超過同伴。」

10此外又說:

「主啊,太初你奠立大地的根基,

親手創造諸天。

11天地都要消亡,但你永遠長存。

天地都會像衣服漸漸破舊,

12你要像捲外衣一樣把天地捲起來。

天地將如衣服一樣被更換,

但你永遠不變,

你的年日永無窮盡。」

13上帝從未對任何一個天使說:

「你坐在我的右邊,

等我使你的仇敵成為你的腳凳。」

14天使豈不都是服役的靈嗎?他們奉差遣,豈不是去為那些將要承受救恩的人服務嗎?