1 Yohanna 1 – HCB & CCBT

Hausa Contemporary Bible

1 Yohanna 1:1-10

Kalman da ya zama mutum

1Wannan da ya kasance tun farko, wanda muka ji, wanda muka gani da idanunmu, wanda muka duba, hannuwanmu kuma suka taɓa, wannan ne muke shela game da Kalman rai. 2Wannan Rai ya bayyana, muka kuwa gan shi, muka kuma shaida shi, muna kuwa yin muku shelar wannan rai madawwami, wanda dā yake tare da Uba, ya kuma bayyana a gare mu. 3Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi. 4Muna rubuta wannan domin farin cikinmu yă zama cikakke.

Tafiya cikin haske

5Wannan shi ne saƙon da muka ji daga wurinsa, muna kuma sanar da ku cewa Allah haske ne; a cikinsa kuwa babu duhu ko kaɗan. 6In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya. 7Amma in muna tafiya cikin haske, yadda yake cikin haske, muna da zumunci da juna ke nan, kuma jinin Yesu, Ɗansa, yana tsarkake mu daga dukan1.7 Ko kuwa kowane zunubi.

8In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. 9In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, yă kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci. 10In muka ce ba mu yi zunubi ba, mun mai da shi maƙaryaci ke nan, maganarsa kuwa ba ta da wuri a cikinmu.

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

約翰一書 1:1-10

生命之道

1論到從太初就已經存在的生命之道,我們曾經耳聞目睹,親眼看過,親手摸過。 2這生命曾顯現過,我們看見了,現在做見證,向你們傳揚這原本與父同在、曾向我們顯現的永恆生命。 3我們把所見所聞傳給你們,使你們可以與我們相交。誠然,我們是與父和祂兒子耶穌基督相交。 4我們將這些話寫給你們,是要讓大家都充滿喜樂。

要活在光中

5我們從耶穌那裡聽見、現在傳給你們的信息就是:上帝是光,在祂裡面毫無黑暗。 6如果我們說與祂相交,卻仍過著黑暗的生活,就是撒謊,沒有遵行真理。 7如果我們生活在光明之中,像上帝在光明中一樣,就能夠彼此相交,上帝兒子耶穌的血能洗淨我們一切的罪。

8如果我們說自己沒有罪,便是自欺,真理就不在我們心中。 9如果我們承認自己的罪,上帝是信實公義的,必赦免我們的罪,洗淨我們一切的不義。 10我們如果說自己沒有犯過罪,就是把上帝看作說謊的,祂的道也不在我們心中。