1 Bitrus 1 – HCB & OL

Hausa Contemporary Bible

1 Bitrus 1:1-25

1Bitrus, manzon Yesu Kiristi,

Zuwa ga zaɓaɓɓu na Allah, baƙi a duniya, da suke a warwatse ko’ina a Fontus, Galatiya, Kaffadokiya, Asiya da kuma Bitiniya, 2waɗanda aka zaɓa bisa ga rigyasanin Allah Uba, ta wurin aikin tsarkakewar Ruhu, don biyayya ga Yesu Kiristi, su kuma sami yayyafan jininsa.

Alheri da salama su zama naku a yalwace.

Yabo ga Allah domin bege mai rai

3Yabo ya tabbata ga Allah Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi! Cikin jinƙansa mai girma ya ba mu sabuwar haihuwa cikin bege mai rai ta wurin tashin Yesu Kiristi daga matattu, 4da kuma cikin gādon da ba zai taɓa lalacewa, ɓacewa ko koɗewa ba, ajiyayye a sama dominku, 5ku waɗanda ta wurin bangaskiya ake kiyayewa ta wurin ikon Allah har yă zuwa ceton da yake a shirye da za a bayyana a ƙarshen lokaci. 6A kan wannan kuke cike da farin ciki ƙwarai, ko da yake yanzu na ɗan lokaci kuna fuskantar baƙin ciki daga gwaje-gwaje iri-iri. 7Wannan kuwa domin a tabbatar da sahihancin bangaskiyarku ne, wadda ta fi zinariya daraja nesa, ita zinariya kuwa, ko da yake mai ƙarewa ce, akan gwada ta da wuta, domin bangaskiyan nan taku ta jawo muku yabo da girma da ɗaukaka a bayyanar Yesu Kiristi. 8Ko da yake ba ku taɓa ganinsa ba, kuna ƙaunarsa; kuma ko da yake ba kwa ganinsa yanzu, kun gaskata shi, kun kuma cika da farin ciki ƙwarai, wanda ya fi gaban faɗi, 9gama kuna samun sakamakon bangaskiyarku, ceton rayukanku ke nan.

10Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse, 11suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi. 12Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.

Ku zama masu tsarki

13Saboda haka, ku shirya kanku don aiki; ku zama masu kamunkai; ku kafa begenku duka a kan alherin da za a ba ku sa’ad da aka bayyana Yesu Kiristi. 14Kamar ’ya’ya masu biyayya, kada ku bi mugayen sha’awace-sha’awacen da dā kuke da su sa’ad da kuke rayuwa a cikin jahilci. 15Amma kamar yadda wanda ya kira ku yake mai tsarki, haka ku ma sai ku kasance masu tsarki cikin dukan abubuwan da kuke yi; 16gama a rubuce yake cewa, “Ku zama masu tsarki, domin ni mai tsarki ne.”1.16 Fir 11.44,45; Fir 19.2; Fir 20.7

17Tun da yake kuna kira ga Uba wanda yake yin wa kowane mutum shari’a bisa ga ayyukansa ba bambanci, sai ku yi rayuwarku a nan kamar baƙi cikin tsoro mai bangirma. 18Gama kun san cewa ba da abubuwa masu lalacewa kamar azurfa ko zinariya ce aka fanshe ku daga rayuwar banza da kuka karɓa daga kakanni-kakanninku ba, 19sai dai an fanshe ku da jini mai daraja na Kiristi, ɗan rago marar aibi ko lahani. 20An zaɓe shi kafin halittar duniya, amma an bayyana shi a zamanin ƙarshe saboda ku. 21Ta gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya tā da shi daga matattu, aka kuma ɗaukaka shi, ta haka bari bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.

22Yanzu da kuka tsarkake kanku ta wurin yin biyayya ga gaskiyan nan, don ku kasance da ƙauna mai gaskiya wa ’yan’uwanku, sai ku ƙaunaci juna ƙwarai, daga zuciya. 23Gama an sāke haihuwarku, ba da iri da yake lalacewa ba, sai dai marar lalacewa, ta wurin rayayyiya da kuma madawwamiyar maganar Allah. 24Gama,

“Dukan mutane kamar ciyawa suke,

darajarsu kuma kamar furannin jeji ne;

ciyawa takan yanƙwane furannin kuma su kakkaɓe,

25amma maganar Ubangiji tana nan har abada.”1.25 Ish 40.6-8

Wannan kuwa ita ce kalmar da aka yi muku wa’azi.

O Livro

1 Pedro 1:1-25

1Pedro, apóstolo de Jesus Cristo, aos que vivem como estrangeiros no mundo, espalhados pelo Ponto, Galácia, Capadócia, província da Ásia e Bitínia.

2Deus o Pai escolheu-vos, sabendo que haveriam de tornar-se seus. E o Espírito Santo tem-vos santificado, pelo sangue de Jesus Cristo, tornando-vos capazes de lhe obedecer.

Que Deus vos dê a sua graça e a sua paz em abundância.

A esperança da vida eterna

3Toda a honra seja dada a Deus e Pai de nosso Senhor Jesus Cristo. Pois foi a sua grande misericórdia que nos fez nascer de novo para uma esperança viva, pela ressurreição de Cristo de entre os mortos, 4para a posse da herança que Deus vos reservou nos céus, que não poderá nem alterar-se, nem deteriorar-se, nem desaparecer. 5Por meio da fé, Deus guarda-vos pelo seu poder para a salvação que há de manisfestar-se antes do fim dos tempos. 6É caso para estarem bem alegres com isso, ainda que por algum tempo sofram provações diversas.

7Estas tribulações são apenas para provar a vossa fé, para mostrar que é forte e genuína. Está a ser testada como ouro que é purificado pelo fogo. Mas a vossa fé é muito mais preciosa do que o simples ouro. Por isso, se a vossa fé permanecer forte, depois de testada pelo fogo, resultará em louvor, glória e honra no dia da vinda de Jesus Cristo.

8Vocês amam a Cristo sem nunca o terem visto. Mesmo agora, não o vendo, mas crendo nele, alegram-se com uma felicidade indescritível e cheia de glória, 9porque estão a receber a salvação das vossas almas, que é o resultado da vossa fé nele.

10Esta salvação foi algo que os profetas investigaram e procuraram conhecer, ao referir-se à graça que vos é dada, 11interrogando-se sobre o tempo e a que circunstâncias o Espírito de Cristo, que estava neles, se referia. Porque os levava a escrever sobre acontecimentos que haveriam de ter lugar com Cristo, os seus sofrimentos e a glória que haveria de seguir-se. 12Foi-lhes assim revelado que essas coisas não teriam lugar naquele tempo, mas nos nossos dias. E agora estas boas novas têm-vos sido anunciadas por aqueles que vos pregaram pelo Espírito Santo enviado do céu. Para elas os anjos no céu desejam bem atentar.

Sejam santos

13Portanto, com um espírito alerta e com sobriedade, coloquem a vossa esperança na graça que será vossa quando Jesus Cristo voltar. 14Como filhos obedientes de Deus, não se conformem com a maldade de quando viviam na ignorância. 15Mas tal como é santo aquele que vos chamou sejam também santos em toda a vossa maneira de viver. 16Porque ele próprio disse: “Sejam santos, porque eu sou santo.”1.16 Lv 11.44-45; 19.2.

17E lembrem-se de que o vosso Pai divino, a quem oram, não julga com favoritismos. Ele vos julgará com perfeita justiça por tudo o que tiverem feito. Por isso, conduzam-se com temor reverente para com Deus, durante a vossa passagem aqui na Terra. 18Sabem que Deus pagou um preço para vos resgatar daquela forma inútil de vida que receberam, por tradição, dos vossos pais. E esse resgate pagou-o não com ouro ou prata, 19mas com o precioso sangue de Cristo, o cordeiro de Deus, sem pecado e sem mancha. 20Deus designou-o com esse propósito, ainda antes da criação do mundo, mas foi agora manifestado, nesta fase final da história, para vosso bem. 21Por seu intermédio, confiam em Deus que o ressuscitou da morte e o glorificou, para que a vossa fé e esperança descansem em Deus.

22Agora podem sentir um amor fraterno, não fingido, porque as vossas almas foram purificadas pela obediência à verdade. Amem-se pois uns aos outros de todo o coração. 23Porque nasceram de novo, não de uma semente perecível, mas de uma semente imortal, pela palavra de Deus viva e que permanece para sempre. 24Como o profeta diz:

“O ser humano é como a erva,

e todo o seu esplendor é como as flores que morrem.

A erva seca e as flores caem,

25mas a palavra do Senhor permanece para sempre.”1.25 Is 40.6-8.

E esta palavra é a boa nova que vos foi anunciada.