馬太福音 1 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

馬太福音 1:1-25

耶穌基督的家譜

1耶穌基督是亞伯拉罕的子孫、大衛的後裔,以下是祂的家譜:

2亞伯拉罕以撒

以撒雅各

雅各猶大和他的兄弟,

3猶大她瑪法勒斯謝拉

法勒斯希斯崙1·3 」希臘文是「亞蘭」。

希斯崙

4亞米拿達

亞米拿達拿順

拿順撒門

5撒門喇合波阿斯

波阿斯路得俄備得

俄備得耶西

6耶西大衛王。

大衛烏利亞的妻子生所羅門

7所羅門羅波安

羅波安亞比雅

亞比雅亞撒

8亞撒約沙法

約沙法約蘭

約蘭烏西雅

9烏西雅約坦

約坦亞哈斯

亞哈斯希西迦

10希西迦瑪拿西

瑪拿西亞們

亞們約西亞

11約西亞耶哥尼雅和他的兄弟,

那時以色列人被擄往巴比倫

12被擄到巴比倫以後,

耶哥尼雅撒拉鐵

撒拉鐵所羅巴伯

13所羅巴伯亞比玉

亞比玉以利亞敬

以利亞敬亞所

14亞所撒督

撒督亞金

亞金以律

15以律以利亞撒

以利亞撒馬但

馬但雅各

16雅各約瑟

約瑟就是瑪麗亞的丈夫,

那被稱為基督1·16 基督」意思是「受膏者」。的耶穌就是瑪麗亞生的。

17這樣,從亞伯拉罕大衛共有十四代,從大衛到被擄至巴比倫也是十四代,從被擄至巴比倫到基督降生也是十四代。

耶穌的降生

18以下是耶穌基督降生的經過。

耶穌的母親瑪麗亞約瑟訂了婚,還沒有成親就從聖靈懷了孕。 19約瑟是個義人,不願公開地羞辱她,便決定暗中和她解除婚約。 20他正在考慮這事的時候,主的一位天使在夢中向他顯現,說:「大衛的後裔約瑟,不要怕,把瑪麗亞娶過來,因為她所懷的孕是從聖靈來的。 21她將生一個兒子,你要給祂取名叫耶穌1·21 耶穌」意思是「救主」。,因為祂要把自己的子民從罪惡中救出來。」

22這一切應驗了主藉著先知所說的話: 23「必有童貞女懷孕生子,祂的名字要叫以馬內利,意思是『上帝與我們同在』。」 24約瑟醒來,就遵從主的天使的吩咐和瑪麗亞結婚, 25只是在她生下孩子之前沒有與她同房。約瑟給孩子取名叫耶穌。

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 1:1-25

Asalin Yesu Kiristi

(Luka 3.23-38)

1Tarihin da aka rubuta game da asalin Yesu Kiristi ɗan Dawuda, ɗan Ibrahim.

2Ibrahim ya haifi Ishaku,

Ishaku ya haifi Yaƙub,

Yaƙub ya haifi Yahuda da ’yan’uwansa,

3Yahuda ya haifi Ferez da Zera, waɗanda Tamar ce mahaifiyarsu;

Ferez ya haifi Hezron,

Hezron ya haifi Ram,

4Ram ya haifi Amminadab,

Amminadab ya haifi Nashon,

Nashon ya haifi Salmon,

5Salmon ya haifi Bowaz, wanda Rahab ce mahaifiyarsa,

Bowaz ya haifi Obed, wanda Rut ce mahaifiyarsa,

Obed ya haifi Yesse,

6Yesse kuwa ya haifi Sarki Dawuda.

Dawuda ya haifi Solomon, wanda matar Uriya ce mahaifiyarsa.

7Solomon ya haifi Rehobowam,

Rehobowam ya haifi Abiya,

Abiya ya haifi Asa,

8Asa ya haifi Yehoshafat,

Yehoshafat ya haifi Yehoram,

Yehoram ya haifi Azariya,

9Azariya ya haifi Yotam,

Yotam ya haifi Ahaz,

Ahaz ya haifi Hezekiya,

10Hezekiya ya haifi Manasse,

Manasse ya haifi Amon,

Amon ya haifi Yosiya,

11Yosiya kuma ya haifi Yekoniya1.11 Wato, Jehohiyachin; haka ma a aya 12 da ’yan’uwansa a lokacin da aka kwashe su zuwa bauta a Babilon.

12Bayan an kwashe su zuwa bauta a Babilon.

Yekoniya ya haifi Sheyaltiyel,

Sheyaltiyel ya haifi Zerubbabel,

13Zerubbabel ya haifi Abiyud,

Abiyud ya haifi Eliyakim,

Eliyakim ya haifi Azor,

14Azor ya haifi Zadok,

Zadok ya haifi Akim,

Akim kuma ya haifi Eliyud,

15Eliyud ya haifi Eleyazar,

Eleyazar ya haifi Mattan,

Mattan ya haifi Yaƙub,

16Yaƙub ya haifi Yusuf, mijin Maryamu, wadda ta haifi Yesu, wanda ake kira Kiristi.

17Ta haka akwai zuriya goma sha huɗu ke nan duka-duka daga lokacin Ibrahim zuwa lokacin Dawuda, goma sha huɗu kuma daga Dawuda zuwa bauta a Babilon, goma sha huɗu kuma daga bauta a Babilon zuwa Kiristi.1.17 Ko kuwa Kiristi. Kiristi (Da Girik) Almasihu (Da Ibraniyanci) duk suna nufin “Shafaffe.”

Haihuwar Yesu Kiristi

(Luka 2.1-7)

18Ga yadda haihuwar Yesu Kiristi ta kasance. An yi alkawarin auren mahaifiyarsa Maryamu, ga Yusuf. Amma tun kafin su zama miji da mata, sai aka tarar Maryamu tana da ciki, ta wurin Ruhu Mai Tsarki. 19Yusuf mijinta, da yake shi mai adalci ne, bai so yă ba ta kunya, yă tone mata asiri a fili ba, sai ya yi tunani yă sake ta a ɓoye.

20Amma yana cikin wannan tunani, sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana masa cikin mafarki ya ce, “Yusuf ɗan Dawuda, kada ka ji tsoron ɗaukan Maryamu zuwa gidanka a matsayin matarka, gama cikin nan nata, daga wurin Ruhu Mai Tsarki ne. 21Za tă haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu,1.21 Yesu da Girik shi ne Yoshuwa da Ibraniyanci, wanda yake nufin Ubangiji yana ceto. gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu.”

22Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, 23“Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel”1.23 Ish 7.14 (wanda yake nufin “Allah tare da mu”).

24Da Yusuf ya farka daga barci, sai ya bi umarnin mala’ikan Ubangiji, ya ɗauki Maryamu zuwa gida a matsayin matarsa. 25Amma bai kwana da ita ba, sai bayan da ta haifi ɗan. Ya kuwa sa masa suna Yesu.