馬可福音 6 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

馬可福音 6:1-56

拿撒勒人厭棄耶穌

1耶穌帶著門徒離開那地方,回到自己的家鄉。 2到了安息日,祂開始在會堂裡教導人,眾人聽了都很驚奇,說:「這個人從哪裡學來這些本領?祂怎麼會有這種智慧?祂怎麼能行這樣的神蹟? 3這不是那個木匠嗎?祂不是瑪麗亞的兒子嗎?祂不是雅各約西猶大西門的大哥嗎?祂的妹妹們不也住在我們這裡嗎?」他們就對祂很反感。

4耶穌對他們說:「先知到處受人尊敬,只有在本鄉、本族、本家例外。」 5耶穌不能在那裡行任何神蹟,只把手按在幾個病人身上,醫治了他們。 6他們的不信令耶穌詫異,於是祂就去周圍的村莊教導人。

差遣十二使徒

7耶穌召集了十二個使徒,差遣他們兩個兩個地出去,賜給他們制伏污鬼的權柄, 8又吩咐他們除了手杖之外,不用帶食物和背囊,腰包裡也不要帶錢, 9只穿一雙鞋子和一套衣服就夠了。 10祂說:「你們無論到哪裡,就住在那些接待你們的人家裡,一直住到離開。 11如果某地方的人不接待你們,不聽你們傳的道,你們在離開之前要跺掉腳上的塵土,作為對他們的警告!」

12使徒便出去傳道,勸人悔改, 13趕出許多鬼,為許多病人抹油,治好他們。

施洗者約翰遇害

14耶穌聲名遠播,希律王也聽說了祂的事。有人說:「施洗者約翰從死裡復活了,所以能夠行這些神蹟。」

15也有人說:「祂是先知以利亞。」

還有人說:「祂是個先知,跟古代的一位先知相似。」

16希律聽到這些議論,就說:「祂一定是被我斬了頭的約翰從死裡復活了。」 17原來希律娶了他兄弟腓力的妻子希羅底,並為她的緣故而派人逮捕了約翰,把他關押在監牢裡。 18因為約翰屢次對希律說:「你娶弟弟的妻子不合法。」

19希羅底約翰懷恨在心,想要殺掉他,只是不能得逞。 20因為希律知道約翰是個公義聖潔的人,所以敬畏他,並對他加以保護。儘管約翰所講的道理令他困惑不安,他仍然喜歡聽。

21機會終於來了。希律在自己的生日那天設宴招待文武百官和加利利的顯要。 22希羅底的女兒進來跳舞,甚得希律和客人的歡心。王對她說:「你想要什麼,只管說。」 23王還對她起誓說:「無論你要什麼,哪怕是我的半壁江山,我都會給你。」

24她便出去問她母親:「我應該要什麼呢?」

她母親說:「要施洗者約翰的頭!」

25她馬上回去對王說:「願王立刻把施洗者約翰的頭放在盤子裡送給我。」

26王聽了這個請求,感到十分為難,但因為在賓客面前起了誓言,就不好拒絕。 27他立刻命令衛兵進監牢砍了約翰的頭, 28放在盤子裡送給這女子,她又轉送給她母親。 29約翰的門徒聽到這個消息,就來把約翰的屍體領回去,安葬在墳墓裡。

耶穌使五千人吃飽

30使徒們聚集在耶穌身邊,向祂報告事工和傳道的經過。 31耶穌對他們說:「你們私下跟我到僻靜的地方去歇一會兒吧。」因為當時來來往往找他們的人實在太多,他們連吃飯的時間都沒有。

32他們乘船悄悄地到了一處僻靜的地方。 33可是有許多人看見他們離開,認出了他們,便從各城鎮步行趕往那裡,比他們先到達。 34耶穌一下船,看見這一大群人好像沒有牧人的羊,心裡憐憫他們,於是教導了他們許多道理。

35天色晚了,門徒過來對耶穌說:「時候已經不早了,這裡又是荒郊野外, 36請遣散眾人,好讓他們到周圍的村莊去自己買些吃的。」

37耶穌說:「你們給他們吃的吧。」

門徒說:「我們哪來這麼多錢買東西給他們吃啊?」

38耶穌說:「看看你們有多少餅。」

他們察看後,說:「有五個餅和兩條魚。」

39耶穌吩咐門徒叫大家分組坐在草地上。 40於是眾人坐下,有的五十人一組,有的一百人一組。 41耶穌拿起那五個餅、兩條魚,舉目望著天祝謝後,掰開遞給門徒,讓他們分給眾人。祂又照樣把那兩條魚分給眾人。 42大家都吃了,並且吃飽了。 43門徒把剩下的碎餅、碎魚收拾起來,裝滿了十二個籃子。 44當時吃餅的男人有五千。

耶穌在湖面上行走

45隨後,耶穌催門徒上船,叫他們先渡到湖對岸的伯賽大,祂則遣散眾人。 46祂辭別了眾人後,就上山去禱告。 47到了晚上,門徒的船在湖中心,耶穌獨自留在岸上。 48大約凌晨三點鐘,祂看見門徒在逆風中搖櫓,非常吃力,就從水面上朝門徒走去,想要從他們旁邊經過。 49門徒看見有人在湖面上走,以為是幽靈,嚇得驚叫起來。 50全船的人看見祂,都嚇壞了,耶穌立刻對他們說:「放心吧,是我,不要怕!」

51耶穌上了船,來到他們那裡,風便停了。門徒心裡十分驚奇, 52因為他們仍然不明白耶穌分餅那件事的意義,心裡還是愚頑。 53他們渡到湖對岸,來到革尼撒勒,在那裡靠岸, 54剛一下船,眾人立刻認出了耶穌。 55他們跑遍那一帶地方,用墊子把生病的人抬來,聽到耶穌在哪裡,就把病人抬到哪裡。 56耶穌不論到哪一個城市、鄉鎮和村莊,人們總是把病人抬到街市上,求耶穌讓他們摸一摸祂衣裳的穗邊,所有摸過的病人都好了。

Hausa Contemporary Bible

Markus 6:1-56

Annabi marar daraja

(Mattiyu 13.53-58; Luka 4.16-30)

1Yesu ya tashi daga can ya tafi garinsa, tare da almajiransa. 2Da Asabbaci ya kewayo, sai ya fara koyarwa a cikin majami’a, mutane da yawa da suka saurare shi, suka yi mamaki.

Suna tambaya, “Ina mutumin nan ya sami waɗannan abubuwa? Wace hikima ce wannan da aka ba shi, har da yana yin ayyukan banmamaki haka! 3Ashe, wannan ba shi ne kafinta nan ba? Shin, ba shi ne ɗan Maryamu ba, ba shi ne ɗan’uwan su Yaƙub, Yusuf, Yahuda da kuma Siman ba? Ashe, ’yan’uwansa mata kuma ba suna nan tare da mu ba?” Sai suka ji haushinsa.

4Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa kaɗai, da kuma cikin ’yan’uwansa, da cikin gidansa ne, annabi ba shi da daraja.” 5Bai iya yin ayyukan banmamaki a wurin ba, sai dai ɗibiya hannuwansa da ya yi a kan mutane kima da suke da cututtuka, ya kuwa warkar da su. 6Ya kuwa yi mamaki ƙwarai don rashin bangaskiyarsu.

Yesu ya aiki sha biyun

(Mattiyu 10.5-15; Luka 9.1-6)

Sai ya Yesu zazzaga ƙauyuka yana koyarwa. 7Ya kira Sha Biyun nan wurinsa, ya aike su biyu-biyu, ya kuma ba su iko bisa mugayen ruhohi.

8Ga dai umarnansa, “Kada ku ɗauki kome don tafiyar, sai dai sanda ba burodi, ba jaka, ba kuɗi a ɗamararku. 9Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa. 10Duk sa’ad da kuka shiga wani gida, ku zauna nan sai kun bar garin. 11In kuwa a wani wuri ba a karɓe ku, ba a kuwa saurare ku ba, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita, a matsayin shaida a kansu.”

12Suka fita, suna yi wa’azi, suna ce wa mutane su tuba. 13Suka fitar da aljanu da yawa, suka shafa wa marasa lafiya da yawa mai, suka kuwa warkar da su.

An yanke kan Yohanna Mai Baftisma

(Mattiyu 14.1-12; Luka 9.7-9)

14Sarki Hiridus ya ji wannan labari, gama sunan Yesu ya bazu a ko’ina. Waɗansu suna cewa, “An tashe Yohanna Mai Baftisma daga matattu ne, shi ya sa yana da ikon yin ayyukan banmamakin nan.”

15Waɗansu suka ce, “Ai, Iliya ne.”

Har wa yau waɗansu suka ce, “Ai, annabi ne, kamar ɗaya daga cikin annabawan dā.”

16Amma da Hiridus ya ji haka, sai ya ce, “Ai, Yohanna ne, mutumin da na yanke masa kai, shi ne ya tashi daga matattu!”

17Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura. 18Gama Yohanna ya yi ta ce wa Hiridus, “Ba daidai ba ne bisa ga doka, ka ɗauki matar ɗan’uwanka.” 19Saboda haka, Hiridiyas ta ƙulla munafunci game da Yohanna, ta kuma so ta kashe shi. Amma ba tă iya ba, 20domin Hiridus yana jin tsoron Yohanna, ya kuma kāre shi sosai, da sanin cewa shi mutum ne mai adalci da kuma mai tsarki. Duk sa’ad da Hiridus ya saurari Yohanna, yakan damu ƙwarai, duk da haka, yakan so yă ji shi.

21A ƙarshe, ta sami zarafi. A ranar murnar haihuwar Hiridus, ya yi biki domin hakimansa, da shugabannin sojojinsa, da kuma manyan mutanen Galili. 22Sa’ad da diyar Hiridiyas ta shigo, ta kuma yi rawa, sai ta gamshi Hiridus tare da baƙinsa.

Sai Sarkin ya ce wa yarinyar, “Ki tambaye ni kome da kike so, ni kuwa zan ba ki.” 23Ya yi mata alkawari da rantsuwa cewa, “Duk abin da kika roƙa, zan ba ki, ko da rabin mulkina ne.”

24Sai ta fita ta ce wa mahaifiyarta, “Me zan roƙa?”

Ta ce, “Kan Yohanna Mai Baftisma.”

25Nan da nan, sai yarinyar ta yi hanzari zuwa wajen sarki da roƙon, “Ina so ka ba ni kan Yohanna Mai Baftisma a cikin tasa, yanzu-yanzu nan.”

26Sai sarki ya yi baƙin ciki ƙwarai, amma saboda rantsuwar da kuma baƙinsa, bai so yă hana ta ba. 27Nan take, sai ya aiki mai aiwatar da kisa da umarni ya kawo kan Yohanna. Mutumin ya je ya yanke kan Yohanna a kurkuku. 28Ya kuma kawo kan a tasa ya ba yarinyar. Ita kuma ta ba wa mahaifiyarta. 29Da almajiran Yohanna suka sami labari, sai suka zo suka ɗauki jikinsa suka binne a kabari.

Yesu ya ciyar da dubu biyar

(Mattiyu 14.13-21; Luka 9.10-17; Yohanna 6.1-14)

30Manzannin suka taru kewaye da Yesu, suka ba shi rahoton duk abin da suka yi, da kuma suka koyar. 31To, saboda mutane da yawa suna kai da kawowa, har ma ba su sami damar cin abinci ba, sai ya ce musu, “Ku zo mu kaɗaita inda ba kowa don ku ɗan huta.”

32Sai suka tafi a jirgin ruwa su kaɗai, inda ba kowa. 33Amma mutane da yawa waɗanda suka ga tashinsu, sun gane su, sai suka ruga da gudu a ƙafa daga dukan birane, suka riga su kaiwa can. 34Da Yesu ya sauka, ya ga taro mai yawa, sai ya ji tausayinsu, gama kamar tumaki suke waɗanda ba su da makiyayi. Sai ya fara koya musu abubuwa da yawa.

35A lokacin nan yamma ta yi, sai almajiransa suka zo wurinsa suka ce masa, “Wurin nan ƙauye ne, ga shi kuma lokaci ya ƙure. 36Ka sallami mutanen su shiga ƙauyukan da suke kurkusa, su sayi wa kansu wani abu, su ci.”

37Sai ya amsa ya ce, “Ku, ku ba su wani abu su ci.”

Suka ce masa, “Ai, wannan zai ɗauki albashin wata takwas na mutum!6.37 Girik zai ci dinari ɗari biyu Mu je mu kashe yawan kuɗin nan a burodi mu ba su su ci?”

38Sai ya yi tambaya ya ce, “Burodi nawa kuke da su? Je ku duba.”

Da suka duba, sai suka ce, “Biyar da kifi biyu.”

39Sa’an nan Yesu ya umarce su su sa dukan mutanen su zazzauna ƙungiya-ƙungiya a kan ɗanyar ciyawa. 40Haka suka zazzauna a ƙungiyar ɗari-ɗari, da kuma hamsin-hamsin. 41Ya ɗauki burodi guda biyar da kifin nan biyu, ya ɗaga kai sama, ya yi godiya, ya kakkarya burodin. Sai ya ba wa almajiransa su rarraba wa mutane. Ya kuma rarraba kifi biyun a tsakaninsu duka. 42Kowa ya ci, ya ƙoshi, 43almajiran suka kwashe gutsattsarin burodin da na kifin cike da kwanduna goma sha biyu. 44Yawan mutanen da suka ci kuwa maza dubu biyar ne.

Yesu ya yi tafiya kan ruwa

(Mattiyu 14.22-33; Yohanna 6.15-21)

45Nan da nan Yesu ya sa almajiransa su shiga jirgin ruwa, su sha gabansa zuwa Betsaida, shi kuma yă sallami taron. 46Bayan ya bar su, sai ya hau kan dutse don yă yi addu’a.

47Da yamma ta yi, jirgin ruwan yana tsakiyar tafkin, Yesu kuma yana can a ƙasa shi kaɗai. 48Ya ga almajiran suna fama da tuƙi saboda iska tana gāba da su. Wajen tsara ta huɗu na dare, sai ya tafi wurinsu, yana takawa a kan tafkin. Ya yi kamar zai wuce su, 49amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, 50domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.

Nan da nan ya yi magana da su ya ce, “Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro.” 51Sai ya shiga jirgin ruwan tare da su, iskar kuma ta kwanta. Dukansu suka yi mamaki, 52gama ba su fahimci al’amarin burodin nan ba, don zuciyarsu ta taurare.

(Mattiyu 14.34-36)

53Da suka haye, sai suka sauka a Gennesaret, suka daure jirgin a ƙugiya. 54Da fitowarsu daga jirgin, sai mutane suka gane Yesu. 55Suka gama yankin da gudu, suna ɗaukan marasa lafiya a kan tabarmai zuwa duk inda suka ji yake. 56Duk inda ya shiga, cikin ƙauyuka, birane ko karkara, sai su kwantar da marasa lafiya a bakin kasuwa. Suka roƙe shi yă bari su taɓa gefen rigarsa kawai, kuma duk waɗanda suka taɓa shi kuwa, suka warke.