馬可福音 10 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

馬可福音 10:1-52

論婚姻

1耶穌離開那裡,來到猶太地區和約旦河河東岸,人群又聚集到祂那裡。耶穌像往常一樣教導他們。 2一些法利賽人想試探耶穌,就來問祂:「男人可以休妻嗎?」 3耶穌反問道:「摩西怎麼吩咐你們的?」

4他們說:「摩西准許人寫休書休妻。」

5耶穌說:「摩西因為你們心硬,才給你們寫了這條誡命。 6太初創造時,『上帝造了男人和女人。』 7『因此,人要離開父母,與妻子結合, 8二人成為一體。』這樣,夫妻不再是兩個人,而是一體了。 9因此,上帝配合的,人不可分開。」

10回到屋裡後,門徒追問耶穌這件事。 11耶穌說:「任何人休妻另娶,就是對妻子不忠,是犯通姦罪。 12同樣,妻子若離棄丈夫另嫁,也是犯通姦罪。」

祝福孩童

13有人帶著小孩子來要讓耶穌摸一摸,門徒卻責備他們。 14耶穌看見後很生氣,對門徒說:「讓小孩子到我這裡來,不要阻止他們,因為上帝的國屬於這樣的人。 15我實在告訴你們,人若不像小孩子一樣接受上帝的國,絕不能進去。」 16於是,耶穌抱起小孩子,把手按在他們身上,為他們祝福。

永生的代價

17耶穌正要上路,有一個人跑來跪在祂跟前,問祂:「良善的老師,我該做什麼才能承受永生?」

18耶穌說:「你為什麼稱呼我『良善的老師』呢?只有上帝是良善的。 19你知道『不可殺人,不可通姦,不可偷盜,不可作偽證,不可欺詐,要孝敬父母』這些誡命。」

20那人說:「老師,我從小就遵行這些誡命。」

21耶穌望著他,心中愛他,便說:「你還有一件事沒有做,就是變賣你所有的產業,送給窮人,你必有財寶存在天上,然後你還要來跟從我。」

22那人聽了,臉色驟變,便沮喪地走了,因為他有許多產業。 23耶穌看看周圍的人,對門徒說:「有錢人進上帝的國真難啊!」

24門徒聽了感到驚奇,耶穌便再次對他們說:「孩子們,10·24 有古卷此處有「依靠錢財的人」。進上帝的國多麼難啊! 25駱駝穿過針眼比有錢人進上帝的國還容易呢!」

26門徒更加驚奇,便議論說:「這樣,誰能得救呢?」

27耶穌看著他們說:「對人而言,這不可能,但對上帝而言,凡事都可能。」

28彼得說:「你看,我們已經撇下一切來跟從你了。」

29耶穌說:「我實在告訴你們,任何人為了我和福音而撇下房屋、弟兄、姊妹、父母、兒女或田地, 30今世必在房屋、弟兄、姊妹、父母、兒女或田地方面獲得百倍的回報,來世必得永生。當然他也會受到迫害。 31然而,許多為首的將要殿後,殿後的將要為首。」

耶穌第三次預言自己的受難

32在前往耶路撒冷的路上,耶穌走在眾人前面,門徒感到驚奇,其他跟隨的人也很害怕。

耶穌把十二個門徒叫到一旁,再把自己將要遭遇的事告訴他們,說: 33「聽著,我們現在前往耶路撒冷。人子將被交在祭司長和律法教師的手中,他們要判祂死刑,把祂交給外族人。 34他們會嘲弄祂,向祂吐唾沫,鞭打祂,殺害祂。但是,三天之後祂必復活!」

雅各與約翰的請求

35西庇太的兩個兒子雅各約翰上前對耶穌說:「老師,請你答應我們一個要求。」

36耶穌問:「什麼要求?」

37他們說:「在你的榮耀中,求你讓我們一個坐在你右邊,一個坐在你左邊。」

38耶穌說:「你們不知道自己在求什麼。我要喝的那杯,你們能喝嗎?我要受的洗,你們能受嗎?」

39他們說:「我們能。」

耶穌說:「我要喝的那杯,你們也要喝;我所受的洗,你們也要受。 40不過誰坐在我的左右不是我來定,而是為誰預備的,就讓誰坐。」

41其他十個門徒聽見這事後,很生雅各約翰的氣。 42於是,耶穌把他們叫來,對他們說:「你們知道,外族人有君王統治他們,有大臣管理他們, 43但你們不可這樣。你們中間誰要當首領,誰就要做大家的僕人; 44誰要居首位,誰就要做大家的奴僕。 45因為就連人子也不是來受人服侍,而是來服侍人,並且犧牲性命,作許多人的贖價。」

治好瞎子巴底買

46耶穌和門徒來到耶利哥。當耶穌和門徒及眾人出城的時候,碰到一個瞎眼的乞丐坐在路旁乞討,他的名字叫巴底買,是底買的兒子。 47巴底買一聽到經過的是拿撒勒人耶穌,就喊道:「大衛的後裔耶穌啊,可憐我吧!」

48許多人都責備他,叫他不要吵,但他卻更加大聲喊道:「大衛的後裔啊,可憐我吧!」

49耶穌停下腳步,叫人帶他過來。

他們就對瞎子巴底買說:「好了,起來吧,祂叫你呢。」

50巴底買丟下外衣,跳了起來,走到耶穌面前。

51耶穌問他:「你要我為你做什麼?」

瞎子說:「老師,我想能夠看見。」

52耶穌說:「回去吧!你的信心救10·52 」或譯「醫治」。了你。」那人立刻得見光明,在路上跟從了耶穌。

Hausa Contemporary Bible

Markus 10:1-52

Kashen aure

(Mattiyu 19.1-12; Luka 16.18)

1Sai Yesu ya tashi daga nan ya tafi yankin Yahudiya, da kuma ƙetaren Urdun. Taron mutane suka sāke zuwa wurinsa, ya kuma koya musu kamar yadda ya saba.

2Waɗansu Farisiyawa suka zo suka gwada shi, ta wurin yin masa tambaya cewa, “Daidai ne bisa ga doka, mutum yă saki matarsa?”

3Ya amsa ya ce, “Me Musa ya umarce ku?”

4Suka ce, “Musa ya ba da izini mutum yă rubuta takardar saki, yă kuma kore ta.”

5Yesu ya ce, “Saboda taurin kanku ne, Musa ya rubuta muku wannan doka. 6Amma a farkon halitta, Allah ya ‘halicce su miji da mace.’10.6 Far 1.27 7‘Saboda wannan dalili, mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, 8su biyun kuma za su zama jiki ɗaya.’10.8 Far 2.24 Saboda haka, su ba mutum biyu ba ne, amma mutum ɗaya. 9Domin haka, abin da Allah ya haɗa, kada mutum yă raba.”

10Da suna cikin gida kuma, sai almajiran suka tambayi Yesu game da wannan. 11Ya amsa ya ce, “Duk wanda ya saki matarsa, ya auri wata, yana da laifin aikata zina a kan matar da ya saki. 12In kuma ta saki mijinta ta auri wani, ta yi zina ke nan.”

Yesu da ƙananan yara

(Mattiyu 19.13-15; Luka 18.15-17)

13Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su. 14Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 15Gaskiya nake gaya muku, duk wanda bai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.” 16Sai ya ɗauki yaran a hannuwansa, ya ɗibiya musu hannuwansa, ya kuma albarkace su.

Saurayi mai arziki

(Mattiyu 19.16-30; Luka 18.18-30)

17Da Yesu ya kama hanya, sai wani mutum ya ruga da gudu ya zo wajensa, ya durƙusa a gabansa ya ce, “Malam nagari, me zan yi domin in gāji rai madawwami?”

18Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake ce da ni mai nagarta? Ai, ba wani nagari, sai Allah kaɗai. 19Ka san dokokin da suka ce, ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta ƙarya, kada ka cuci wani, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’10.19 Fit 20.12; M Sh 5.16-20

20Mutumin ya ce, “Malam, ai, tun ina yaro na kiyaye duk waɗannan.”

21Yesu ya kalle shi da ƙauna ya ce, “Abu ɗaya ka rasa, ka tafi ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo ka bi ni.”

22Da jin wannan, sai mutumin ya ɓata fuskarsa, ya tafi da baƙin ciki, gama yana da arziki sosai.

23Yesu ya dudduba, sai ya ce wa almajiransa, “Yana da wuya fa masu arziki su shiga mulkin Allah!”

24Almajiransa suka yi mamakin kalmominsa. Amma Yesu ya sāke ce musu, “’Ya’yana, yana da wuya fa a shiga mulkin Allah! 25Ya fi sauƙi raƙumi yă shiga ta kafar allura, da mai arziki yă shiga mulkin Allah.”

26Almajiran suka yi mamaki ƙwarai, suka ce wa juna, “To, wa zai sami ceto ke nan?”

27Yesu ya kalle su ya ce, “Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah.”

28Bitrus ya ce, “Mun bar kome domin mu bi ka!”

29Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko ’yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ’ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, 30sa’an nan yă kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da ’yan’uwa mata, da ’yan’uwa maza, da uwaye, da ’ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma yă sami rai madawwami. 31Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma, za su zama na farko.”

Yesu ya sāke yin zancen mutuwarsa

(Mattiyu 20.17-19; Luka 18.31-34)

32Suna haurawa a hanyarsu zuwa Urushalima ke nan, Yesu yana a gaba, almajiran suna bin sa suna mamaki, waɗanda suke bi kuma suna ji tsoro. Ya sāke kai Sha Biyun nan gefe, ya gaya musu abin da zai faru da shi. 33Ya ce, “Za mu haura zuwa Urushalima, za a bashe Ɗan Mutum, ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa, a kuma ba da shi ga Al’ummai, 34waɗanda za su yi masa ba’a, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi. Bayan kwana uku kuma yă tashi.”

Roƙon Yaƙub da Yohanna

(Mattiyu 20.20-28)

35Sai Yaƙub da Yohanna, ’ya’yan Zebedi maza suka zo wurinsa suka ce, “Malam, muna so ka yi mana duk abin da muka roƙa.”

36Ya tambaye su ya ce, “Me kuke so in yi muku?”

37Suka amsa suka ce, “Ka bar ɗayanmu yă zauna a damarka, ɗayan kuma a hagunka, a cikin ɗaukakarka.”

38Yesu ya ce, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya shan kwaf da zan sha, ko a yi muku baftisma da baftismar da aka yi mini?”

39Suka ce, “Za mu iya.”

Yesu ya ce musu, “Za ku sha kwaf da zan sha, a kuma yi muku baftisma da aka yi mini, 40amma zama a damana ko haguna, ba ni nake ba da izinin ba. Waɗannan wurare na waɗanda aka riga aka shirya musu ne.”

41Da sauran goman suka ji wannan, sai suka yi fushi da Yaƙub da Yohanna. 42Yesu ya kira su ya ce musu, “Kun sani waɗanda aka san su da mulkin al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu ma sukan gasa musu iko. 43Ba haka ya kamata yă zama da ku ba. A maimakon, duk wanda yake so yă zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku. 44Duk wanda kuma yake so yă zama na farko, dole yă zama bawan kowa. 45Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”

Bartimawus makaho ya sami gani

(Mattiyu 20.29-34; Luka 18.35-43)

46Sai suka iso Yeriko. Sa’ad da Yesu da almajiransa tare da taro mai yawa suke barin birnin, wani makaho da ake kira Bartimawus kuwa (wato, “ɗan Timawus”), yana zaune a gefen hanya yana bara. 47Da ya ji cewa Yesu Banazare ne, sai ya ɗaga murya, yana cewa, “Yesu Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

48Mutane da yawa suka kwaɓe shi, suka ce yă yi shiru, amma ya ƙara ɗaga murya yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

49Yesu ya tsaya ya ce, “Ku kira shi.”

Sai suka kira makahon suka ce, “Ka yi farin ciki! Tashi tsaye! Yana kiranka.” 50Ya jefar da mayafinsa waje ɗaya, ya yi wuf, ya zo wurin Yesu.

51Yesu ya tambaye shi ya ce, “Me kake so in yi maka?”

Makahon ya ce, “Rabbi, ina so in sami ganin gari.”

52Yesu ya ce, “Je ka, bangaskiyarka ta warkar da kai.” Nan da nan, ya sami ganin gari, ya kuma bi Yesu suka tafi.