提多書 3 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

提多書 3:1-15

專心行善

1你要提醒眾人順服執政掌權者,遵守法令,隨時準備做善事。 2不要毀謗,不要爭吵,要謙和、恭敬地對待每一個人。 3從前我們也愚蠢、悖逆、易受迷惑,受各種私慾和享樂的驅使,心裡充滿了嫉妒和惡念,令人憎惡,也彼此憎恨。 4但我們的救主上帝向人彰顯了祂的恩慈和仁愛, 5藉著重生之洗和聖靈的更新拯救了我們,這並非因為我們有義行,而是因為祂的憐憫。 6上帝藉著我們的救主耶穌基督把聖靈豐豐富富地澆灌在我們身上。 7這樣,我們既然靠著祂的恩典而被稱為義人,就可以成為後嗣,有永生的盼望。 8以上這些話是可信的,希望你認真教導,使信上帝的人專心行善。這都是造福眾人的美事。

9要避免愚昧的爭論、有關家譜的辯駁和律法上的爭執,因為這些毫無益處。 10對於製造分裂的人,警告過一兩次後,要和他斷絕來往。 11因為你知道這種人已經背道犯罪,自定己罪。

信末的囑咐與問候

12我會派亞提馬或者推基古去見你。到時候,你要立刻到尼哥波立來見我,因為我決定在那裡過冬。 13你要為西納律師和亞波羅送行,盡力幫助他們,讓他們路上一無所缺。 14我們的弟兄姊妹也要學習行善,供應有急需的人,免得毫無貢獻。

15這裡的弟兄姊妹都問候你,也請你問候那些因信仰而愛我們的人。

願恩典常與你們眾人同在!

Hausa Contemporary Bible

Titus 3:1-15

Yin abin da yake mai kyau

1Ka tuna wa mutane su zama masu biyayya ga masu mulki da kuma hukumomi, su zama masu biyayya suna kuma a shirye su yi kowane abin da yake mai kyau, 2kada su zama masu ɓata sunan kowa, su zama masu salama da kulawa, su kuma zama masu matuƙar tawali’u ga dukan mutane.

3A wani lokaci can baya mu ma wawaye ne, marasa biyayya, aka ruɗe mu, sha’awace-sha’awace da kwaɗayi iri-iri suka daure mu, muka yi zaman ƙiyayya da kishi, aka ƙi mu, mu kuma muka ƙi juna. 4Amma da alheri da kuma ƙaunar Allah Mai Cetonmu suka bayyana, 5sai ya cece mu, ba saboda abubuwan adalcin da muka aikata ba, sai dai saboda jinƙansa. Ya cece mu ta wurin wankan nan na sāke haihuwa da kuma sabuntawan nan ta Ruhu Mai Tsarki, 6wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Kiristi Mai Cetonmu, 7wannan fa domin an kuɓutar da mu ne ta wurin alherinsa, don mu zama magāda masu begen ga rai madawwami. 8Wannan magana tabbatacciya ce, ina kuma so ka nanata waɗannan abubuwa ƙwarai, domin waɗanda suka dogara ga Allah su himmantu ga aiki mai kyau. Waɗannan abubuwa suna da kyau sosai suna kuma da amfani ga kowane mutum.

9Amma ka guji jayayyar banza da ƙididdigar asali da gardandami da faɗace-faɗace game da Doka, gama ba su da riba kuma aikin banza ne. 10Ka gargaɗe mutumin da yake kawo tsattsaguwa sau ɗaya, ka kuma gargaɗe shi sau na biyu. Bayan haka, kada wani abu yă haɗa ka da shi. 11Ka dai san cewa irin mutumin nan ya taurare kuma mai zunubi ne; ya yanke wa kansa hukunci.

Maganar ƙarshe

12Da zarar na aika Artemas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina a Nikofolis, domin na yanke shawara in ci damina a can. 13Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka taimaki Zenas lauyan nan da Afollos a hanyarsu ka kuma tabbata ba su rasa kome ba.

14Dole mutanenmu su koyi ba da kansu ga aikata abin da yake nagari, domin su iya biyan bukatunsu na yau da kullum kada kuma su yi rayuwar marar amfani.

15Dukan waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka.

Ka gaggai mini da masoyanmu, masu bangaskiya.

Alheri yă kasance tare da ku duka.