希伯來書 5 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

希伯來書 5:1-14

1從人間選出來的大祭司,都是受委任代表人辦理與上帝有關的事,為人的罪向上帝獻上禮物和贖罪祭。 2他能體諒那些無知和迷失的人,因為他自己也有人性的軟弱。 3所以,他不但要為眾人的罪獻祭,也要為自己的罪獻祭。 4沒有人能自取這大祭司的尊榮,只有像亞倫一樣蒙上帝呼召的人才可以做大祭司。

5同樣,基督也沒有自取榮耀做大祭司,是上帝對祂說:

「你是我的兒子,

我今日成為你父親。」

6在聖經的另一處,上帝又說:

「你照麥基洗德的模式永遠做祭司。」

7基督在世為人的時候,曾經聲淚俱下地祈求能救祂脫離死亡的上帝。祂因為敬虔而蒙了應允。 8基督雖然是上帝的兒子,仍然從所受的苦難中學習了順服。 9祂既然達到了純全的地步,就成了永恆救恩的源頭,使所有順服祂的人都得到拯救。 10上帝照著麥基洗德的模式立祂做大祭司。

信徒要長進

11關於這方面的事,我們還有很多話要說,但因為你們已經聽不進去,很難向你們解釋。 12按你們學習的時間來算,你們本該做別人的老師了,可惜你們還需要別人向你們傳授上帝話語的基本道理,成了不能吃乾糧、只能吃奶的人。 13因為只能吃奶的人還是嬰孩,不熟習仁義的道理。 14乾糧是給成年人吃的,他們的心思歷經鍛煉,能夠分辨善惡。

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 5:1-14

1Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai. 2Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali. 3Shi ya sa dole yă miƙa hadayu domin zunubansa, da kuma domin zunuban mutane.

4Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna. 5Haka ma Kiristi bai kai kansa neman ɗaukaka na zama babban firist ba. Allah ne dai ya ce masa,

“Kai Ɗana ne;

yau na zama Uba a gare ka.”5.5 Zab 2.7

6Ya kuma ya ce a wani wuri,

“Kai firist ne na har abada,

bisa ga tsarin Melkizedek.”5.6 Zab 110.4

7A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi. 8Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala 9kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya. 10Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.

Gargaɗi game da kaucewa

11Muna da abubuwa masu yawa da za mu faɗa game da wannan batu, sai dai yana da wuya a bayyana, da yake ba ku da saurin ganewa. 12Gaskiya, a yanzu ya kamata a ce kun zama malamai, sai ga shi kuna bukatar wani yă sāke koya muku abubuwa masu sauƙi game da abin da Allah ya faɗa. Kuna bukatar madara, ba abinci mai kauri ba! 13Duk wanda yake rayuwa a kan madara, shi kamar jariri ne har yanzu, kuma bai san ainihi mene ne ya dace ba. 14Amma abinci mai kauri na balagaggu ne, waɗanda suka hori kansu don su bambanta tsakanin nagarta da mugunta.