哥林多前書 2 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

哥林多前書 2:1-16

信仰的基礎

1弟兄姊妹,我當初到你們那裡傳揚上帝的奧祕,並沒有用高深的言論或哲理。 2因為我已決定在你們當中不談別的,只講耶穌基督和祂被釘十字架的事。 3那時我在你們當中很軟弱,害怕,戰戰兢兢。 4我說話、講道不是靠充滿智慧的雄辯之詞,而是靠聖靈的能力作明證, 5好使你們的信仰不是以人的智慧為基礎,而是以上帝的能力為基礎。

6當然我們也跟成熟的人談論智慧,不過並非這個世代的智慧,也不是那些在世上當權、將來要衰亡之人的智慧。 7我們所講的是上帝隱藏在奧祕中的智慧,是祂為了使我們得榮耀而在萬世以前定好的智慧。 8只可惜世上當權的人沒有一個明白這智慧。他們要是明白,就不會把榮耀的主釘在十字架上了。 9正如聖經上說:

「上帝為愛祂的人所預備的,

是眼睛未曾見過,

耳朵未曾聽聞,

人心也未曾想到的。」

10然而,上帝藉著聖靈將這一切啟示給我們,因為聖靈洞悉萬事,連上帝深奧的事都瞭若指掌。 11除了人裡面的靈,誰能瞭解人的事呢?照樣,除了上帝的聖靈,誰也不能瞭解上帝的事。 12我們接受的不是這世界的靈,而是上帝的聖靈,使我們可以領會上帝開恩啟示給我們的事。 13我們講述這些事,不是用人類智慧所教的話,而是用聖靈所教的話,用屬靈的話解釋屬靈的事2·13 用屬靈的話解釋屬靈的事」或譯「向屬靈的人解釋屬靈的事」。

14然而,屬血氣的人不接受從上帝來的聖靈的教導,認為愚不可及,無法明白,因為只有屬靈的人才能參透。 15屬靈的人能夠參透萬事,但沒有人能參透他。

16「誰曾知道主的心意,

能夠指教祂呢?」

但我們明白基督的心意。

Hausa Contemporary Bible

1 Korintiyawa 2:1-16

1Da na zo wurinku ’yan’uwa, ban zo da iya magana ko wani mafificin hikima yayinda na yi muku shelar shaida game da Allah ba. 2Don na ƙudura a raina sa’ad da nake tare da ku cewa ba zan mai da hankali ga kome ba sai dai Yesu Kiristi wanda aka gicciye. 3Na zo wurinku cikin rashin ƙarfi da tsoro, da rawan jiki ƙwarai. 4Saƙona da wa’azina ba su zo cikin hikima da kalmomin lallashi ba, sai dai da nuna ikon Ruhu, 5domin kada bangaskiyarku ta dogara a kan hikimar mutane, sai dai a kan ikon Allah.

Hikima daga Ruhu

6Duk da haka, muna sanar da saƙon hikima cikin waɗanda suka balaga, amma ba hikima irin ta wannan zamani ba ne, ko kuwa irin ta masu mulkin zamanin nan, waɗanda za su shuɗe ba. 7A’a, muna magana ne a kan asirin hikimar Allah, hikimar da tun dā, take a ɓoye, wadda Allah ya ƙaddara domin ɗaukakarmu, tun kafin farkon zamanai. 8Ba ko ɗaya daga cikin masu mulkin wannan zamani da ya fahimce ta, gama da a ce sun fahimce ta, da ba su gicciye Ubangiji mai ɗaukaka ba. 9Duk da haka, kamar yadda yake a rubuce cewa,

“Ba idon da ya taɓa gani,

ba kunnen da ya taɓa ji,

ba kuma zuciyar da ta taɓa tunanin

abin da Allah ya shirya wa masu ƙaunarsa.”2.9 Ish 64.4

10Amma Allah ya bayyana mana shi ta wurin Ruhunsa.

Ruhu yana bincika dukan abubuwa, har ma da abubuwa masu zurfi na Allah. 11Wane ne a cikin mutane ya san tunanin mutum, in ba ruhun mutumin da yake cikinsa ba? Haka kuma ba wanda ya san tunanin Allah, sai dai Ruhun Allah. 12Ba mu karɓi ruhun duniya ba, sai dai Ruhun da yake daga Allah, domin mu fahimci abin da Allah ya ba mu hannu sake. 13Wannan shi ne abin da muke sanarwa, ba da kalmomin da muka koya ta wurin hikimar mutum ba, amma da kalmomin da Ruhu yake koyarwa, muna faɗin gaskiya ta ruhaniya da kalmomin ruhaniya. 14Mutumin da ba shi da Ruhu, ba ya yarda da abubuwan da suka fita daga Ruhun Allah, domin wauta ce a gare shi. Ba kuwa zai fahimce su ba, domin ta Ruhu ne ake fahimtarsu. 15Mutumin ruhaniya yakan gwada dukan abubuwa, amma shi kansa ba ya ƙarƙashin shari’ar mutum.

16“Wa ya taɓa sanin hankalin Ubangiji,

har da zai koya masa?”2.16 Ish 40.13

Amma muna da tunani iri na Kiristi ne.