使徒行傳 23 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

使徒行傳 23:1-35

1保羅注視著公會的人,說:「弟兄們,我在上帝面前行事為人一向問心無愧。」 2大祭司亞拿尼亞一聽,就命那些站在旁邊的人打保羅的嘴。 3保羅亞拿尼亞說:「你這偽君子23·3 偽君子」希臘文是「粉飾的牆」。,上帝要擊打你!你坐在那裡不是應當依法審問我嗎?你怎麼違法叫人打我?」

4站在旁邊的人說:「你竟敢辱罵上帝的大祭司?」 5保羅說:「弟兄們,我不知道他是大祭司。我知道聖經上說,『不可咒詛百姓的官長。』」

6保羅發現他們一些是法利賽人,一些是撒都該人,就在公會中高聲說:「弟兄們,我是法利賽人,也是法利賽人的子孫。我因為盼望死人復活,才在這裡受審!」 7這句話立刻引起法利賽人和撒都該人之間的爭論,公會分成了兩派。 8因為撒都該人認為沒有復活,也沒有天使和靈,而法利賽人認為這些都有。

9眾人大聲喧嚷,有幾個法利賽派的律法教師站起來爭辯說:「我們找不出這人有什麼錯處,也許真的有靈或天使跟他說過話。」 10爭論越來越激烈,千夫長怕保羅會被他們扯碎了,就派人把他從人群中救出來,帶回軍營。

11當天晚上,主站在保羅身旁對他說:「要勇敢!正如你在耶路撒冷為我作了見證,你也必須在羅馬為我做見證。」

陰謀殺害保羅

12天亮後,猶太人設下陰謀,並起誓說:「不殺保羅,誓不吃喝!」 13有四十多人參與了這個陰謀。 14他們去見祭司長和長老,說:「我們已經發了誓,不殺保羅不吃飯。 15請你們和公會出面通知千夫長,請他把保羅押到你們這裡來,就說要進一步審訊他。我們準備在他到達之前殺掉他!」

16保羅的外甥聽到這一陰謀,就去軍營通知保羅17保羅請來一位百夫長,說:「請趕快帶這青年去見千夫長,他有要事稟告!」 18百夫長領那青年去見千夫長,說:「那囚犯保羅叫我帶這青年來,說有要事稟告。」

19千夫長就拉著那青年的手走到一旁,私下問他:「你有什麼事要告訴我?」 20他說:「那些猶太人約好了,要請求你明天帶保羅到公會受審,假裝要詳細審問他的事。 21你不要答應他們,因為他們有四十多個人會埋伏在半路,並且還起誓說,『不殺保羅就不吃不喝』。他們現在已經準備就緒,就等你答應了。」

22千夫長聽後,就叫他回去,並叮囑道:「你向我稟告的事,不要告訴別人。」

保羅被押往凱撒利亞

23於是,千夫長召來兩名百夫長,吩咐道:「預備二百名步兵、七十名騎兵、二百名長槍手,今晚九時出發去凱撒利亞24要給保羅預備坐騎,護送他安全抵達腓利斯總督那裡。」

25千夫長寫了公文給腓利斯總督,內容如下: 26克勞狄·呂西亞敬問腓利斯總督大人安。 27這人被猶太人抓住,險些被他們殺害。我得知他是羅馬公民,便帶兵去救了他。 28為了弄清楚他們控告他的緣由,我押他到猶太人的公會受審, 29發現他被控告與他們的律法有關,他並沒有犯該被監禁或處死的罪。 30我得知有人準備暗殺他,便立即護送他到你那裡,並通知他的控告者去你那裡告他。」

31軍兵奉命行事,連夜護送保羅安提帕底32第二天,由騎兵繼續護送,其餘軍兵返回軍營。 33他們到了凱撒利亞,將公文呈交總督,把保羅交給他。 34總督看過公文,便問保羅是哪省的人,得知保羅基利迦人,就說: 35「等告你的人來了,我會審理你的案子。」於是下令把保羅關在希律的王府裡。

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 23:1-35

1Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.” 2Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa. 3Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!”

4Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”

5Bulus ya amsa ya ce, “’Yan’uwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa, ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’23.5 Fit 22.28

6Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.” 7Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu. 8(Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.)

9Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?” 10Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja.

11Kashegari da dare Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus ya ce, “Ka yi ƙarfin hali! Don kamar yadda ka yi shaida game da ni a Urushalima, haka kuma lalle, za ka yi shaidata a Roma.”

Ƙulla shawara don a kashe Bulus

12Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus. 13Fiye da mutane arba’in ne suka ƙulla wannan makirci. 14Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus. 15Saboda haka, sai ku da Majalisa sai ku roƙi shugaban ƙungiyar sojan yă kawo shi a gabanku kamar kuna so ku ƙara samun cikakken bayani game da zancensa. Mu kuwa muna a shirye mu kashe shi kafin yă iso nan.”

16Amma da ɗan ’yar’uwar Bulus ya ji wannan makirci, sai ya tafi cikin barikin soja ya gaya wa Bulus.

17Sai Bulus ya kira ɗaya daga cikin jarumawan ya ce, “Ka kai wannan saurayi wurin shugaban ƙungiyar soja; yana da wani abin da zai faɗa masa.” 18Saboda haka ya ɗauke shi ya kai wajen shugaban ƙungiyar sojan.

Jarumin ya ce, “Bulus, ɗan kurkukun nan ya kira ni, ya roƙe ni in kawo wannan saurayi a wurinka domin yana da wani abin da zai faɗa maka.”

19Sai shugaban ƙungiyar sojan ya kama hannun saurayin ya ja shi gefe, ya tambaye shi cewa, “Mene ne kake so ka gaya mini?”

20Saurayin ya ce, “Yahudawa sun ƙulla za su roƙe ka ka kawo Bulus a gaban Majalisa gobe kamar suna neman ƙarin cikakken bayani game da Bulus. 21Kada ka yarda da su, domin fiye da mutum arba’in daga cikinsu suna fakonsa. Sun yi rantsuwa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe shi. Suna nan a shirye yanzu, suna jira ka amince da roƙonsu.”

22Sai shugaban ƙungiyar sojan ya sallami saurayin ya kwaɓe shi ya ce, “Kada ka gaya wa kowa cewa ka faɗa mini wannan.”

An tura Bulus zuwa Kaisariya

23Sai ya kira biyu daga cikin jarumawansa, ya umarce su cewa, “Ku shirya sojoji ɗari biyu, da masu hawan dawakai saba’in da kuma masu māsu ɗari biyu su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan. 24Ku shirya wa Bulus dawakai da zai hau don a kai shi wurin Gwamna Felis lafiya.”

25Ya kuma rubuta wasiƙa kamar haka,

26Kalaudiyus Lisiyas.

Zuwa ga Mai Girma, Gwamna Felis.

Gaisuwa.

27Yahudawa sun kama wannan mutum suna kuma dab da kashe shi, amma na zo da sojojina na ƙwato shi, saboda na ji shi ɗan ƙasar Roma ne. 28Na so in san abin da ya sa suke zarginsa, saboda haka na kawo shi a gaban Majalisarsu. 29Na tarar cewa zargin da ake masa ya shafi waɗansu abubuwan da suka shafi dokarsu ne, amma ba wani zargi a kansa da ya isa kisa ko a daure shi. 30Sa’ad da na sami labari cewa akwai wani makircin da aka ƙulla masa, sai na aika shi wurinka nan da nan. Na kuma umarci masu zarginsa su kai ƙararsu gare ka.

31Saboda haka sojojin, don cika umarni, suka ɗauki Bulus da dad dare suka kawo shi har Antifatiris. 32Kashegari suka bar masu hawan dawakai suka ci gaba da shi, yayinda sojojin suka koma barikin soja. 33Sa’ad da masu hawan dawakai suka isa Kaisariya, sai suka ba wa gwamna wasiƙar suka kuma miƙa masa Bulus. 34Gwamna ya karanta wasiƙar ya kuma tambaya ko daga wanda lardi ne ya fito. Da ya ji cewa shi daga Silisiya ne, 35sai ya ce, “Zan ji batunka lokacin da masu zarginka suka iso.” Sa’an nan ya ba da umarni a kai Bulus a tsare shi a fadar Hiridus.