使徒行傳 20 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

使徒行傳 20:1-38

保羅再訪馬其頓和希臘

1這場風波平息後,保羅召集眾門徒勉勵一番後,便辭別他們去了馬其頓2他走遍那一帶,用許多勸勉的話鼓勵當地的門徒。之後,他又去希臘3在那裡逗留了三個月。當保羅正要乘船去敘利亞時,聽聞猶太人計劃要害他,就決定經馬其頓回去。 4同他到亞細亞去的人有庇哩亞畢羅斯的兒子所巴特帖撒羅尼迦亞里達古西公都,還有特庇該猶提摩太亞細亞推基古特羅非摩5他們先到特羅亞等候我們。 6除酵節過後,我們從腓立比啟航,五天後在特羅亞和他們會合,大家同住了七天。

猶推古死而復活

7七日的第一日20·7 照猶太人的算法,太陽下山後為一日的開始,基督徒又以禮拜天為一周之始,所以七日的第一日很有可能是禮拜六晚上。,我們聚會掰餅,保羅因為次日要離開,就向他們講道,直到深夜。 8我們聚會的樓上整夜燈火通明。 9有個名叫猶推古的青年坐在窗臺上聽道。保羅講了許久,猶推古不勝困倦睡著了,竟從三樓掉了下去。別人將他抱起來時,他已經死了。 10保羅下去伏在他身上,抱著他對眾人說:「不要驚慌,他還活著!」 11保羅說完就回到樓上,與大家一同掰餅、用餐,又談了很久,直到天亮才離去。 12大家非常欣慰地把活過來的猶推古送回了家。

保羅告別以弗所的眾長老

13我們照保羅的吩咐先乘船到亞朔預備在那裡接他,他打算由陸路步行到那裡。 14他到了亞朔,我們接他上船,一同前往米推利尼15我們從米推利尼啟航,第二天到了基阿附近,第三天到達撒摩,第四天在米利都停泊。 16保羅急於趕回耶路撒冷,希望在五旬節前趕到,所以決定不去以弗所,免得在亞細亞境內耽誤太久。

17保羅米利都派人到以弗所請教會的長老前來與他相會。 18他們都來了,保羅說:「各位,自從我踏進亞細亞那天起,在你們當中為人如何,你們都很清楚。 19我含著眼淚謙卑地事奉主,又遭到猶太人的迫害,歷盡艱辛。 20你們也知道,凡是對你們有益的事,我沒有避而不宣,我總是在公開場合和各人家中教導你們。 21我勸猶太人和希臘人都要悔改,歸向上帝,信靠主耶穌基督。 22現在,我在聖靈的催促下去耶路撒冷,不知道在那裡會發生什麼事, 23只知道聖靈在各城鎮指示我,前面必有監禁和苦難等著我。 24不過,哪怕是犧牲性命,我也在所不辭,只盼望我能跑完當跑的路程,完成主耶穌交託給我的使命,為上帝充滿恩典的福音做見證。

25「我一向在你們中間傳揚上帝的國,如今我知道,以後你們再也見不到我的面了。 26所以今天我向你們聲明,將來你們有誰滅亡,與我無關。 27因為上帝的整個計劃,我沒有向你們避而不宣。 28你們要為自己,也要為教會的群羊警醒,因為聖靈已經任命你們做群羊的監督,牧養上帝的教會。教會是主用自己的血贖回來的。 29我知道,在我離開以後,一定會有兇惡的豺狼闖進你們中間,殘害羊群。 30就是你們中間也會有人起來歪曲真理,引誘門徒跟隨他們。 31所以你們一定要警醒,牢記這三年來我怎樣晝夜不住地流著淚勸誡你們。

32「現在,我把你們交託給上帝和祂充滿恩典的道,這道能造就你們,使你們與一切聖潔的人同得產業。 33我從未貪圖別人的金銀和衣服, 34你們都知道,我親手做工養活自己和同工。 35我凡事以身作則,教導你們勤奮工作,幫助軟弱的人,並牢記主耶穌的話,『施比受更有福。』」

36保羅說完這番話,就和大家一同跪下禱告。 37眾人都哭了,抱著保羅與他親吻, 38最使他們傷心的就是他說「你們再也見不到我的面了」。最後,眾人送他上了船。

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 20:1-38

Bulus ya ratsa Makidoniya da Giris

1Sa’ad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya. 2Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris, 3inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yă koma ta Makidoniya. 4Sai Sofater ɗan Fairrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tessalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi. 5Waɗannan mutane suka sha gaba suka kuma jira mu a Toruwas. 6Amma muka tashi daga Filibbi a jirgin ruwa bayan Bikin Burodi Marar Yisti bayan kuma kwana biyar muka sadu da sauran a Toruwas, inda muka zauna kwana bakwai.

Ta da Yutikus daga matattu a Toruwas

7A ranar farko ta mako muka taru wuri ɗaya don gutsuttsura burodi. Bulus ya yi wa mutane magana, don yana niyyar tashi kashegari, sai ya yi ta yin magana har tsakar dare. 8Akwai fitilu da yawa a ɗakin gidan saman da muka taru. 9Akwai wani saurayi zaune a taga mai suna Yitikus, wanda barci mai nauyi ya ɗauke shi yayinda Bulus yake ta tsawaita magana. Sa’ad da yake barci, sai ya fāɗi daga gidan sama a hawa ta uku aka kuma ɗauke shi matacce. 10Sai Bulus ya sauka, ya miƙe a kan saurayin ya rungume shi ya ce, “Kada ku damu, yana da rai!” 11Sai ya koma ɗakin da yake a gidan sama, ya gutsuttsura burodi ya kuma ci. Bayan ya yi magana har gari ya waye, sai ya tafi. 12Mutanen suka ɗauki saurayin da rai zuwa gida suka kuma ta’azantu ƙwarai da gaske.

Bankwanan Bulus ga dattawan Afisa

13Mu kuwa muka ci gaba zuwa jirgin ruwan muka tashi muka nufi Assos inda za mu ɗauki Bulus. Ya yi wannan shirin don zai tafi can da ƙafa. 14Da ya same mu a Assos, sai muka ɗauke shi a jirgin ruwan muka zo Mitilen. 15Kashegari muka tashi cikin jirgin ruwa daga can muka zo gefen Kiyos. Kwana ɗaya bayan wannan, sai muka ƙetare zuwa Samos, kashegari kuma muka iso Miletus. 16Bulus ya yanke shawara yă wuce Afisa a jirgin ruwa don kada yă ɓata lokaci a lardin Asiya, gama yana sauri yă kai Urushalima, in ya yiwu ma, a ranar Fentekos.

17Daga Miletus, Bulus ya aika zuwa Afisa a kira dattawan ikkilisiya. 18Da suka iso, sai ya ce musu, “Kun san irin zaman da na yi tun lokacin da na zauna da ku, daga ranar farkon da na zo cikin lardin Asiya. 19Na bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali’u har da hawaye, da gwagwarmaya iri-irin da na sha game da makircin Yahudawa. 20Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida. 21Na yi shela ga Yahudawa da Hellenawa cewa dole su juye ga Allah cikin tuba su kuma amince da Ubangijinmu Yesu.

22“Yanzu kuma Ruhu ya tilasta ni, za ni Urushalima, ba tare da sanin abin da zai faru da ni a can ba. 23Na dai san cewa a kowace birni Ruhu Mai Tsarki yakan gargaɗe ni cewa kurkuku da shan wuya suna jirana. 24Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.

25“Yanzu na san cewa ba ko ɗaya daga cikinku wanda na zazzaga ina muku wa’azin mulkin Allah da zai sāke ganina. 26Saboda haka, ina muku shela a yau cewa ba ni da alhakin kowa a kaina. 27Gama ban yi wata-wata a sanar muku dukan nufin Allah ba. 28Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa. 29Na san cewa bayan na tafi, mugayen kyarketai za su shigo cikinku ba za su kuwa ƙyale garken ba. 30Ko cikinku ma mutane za su taso su karkatar da gaskiya don su jawo wa kansu almajirai. 31Saboda haka ku zauna a faɗake! Ku tuna cewa shekara uku, dare da rana ban taɓa fasa yin wa kowannenku gargaɗi ba, har da hawaye.

32“To, yanzu na danƙa ku ga Allah da kuma ga maganar alherinsa, wadda za tă iya gina ku ta kuma ba ku gādo a cikin dukan waɗanda aka tsarkake. 33Ban yi ƙyashin azurfa ko zinariya ko tufafin kowa ba. 34Ku kanku kun san cewa hannuwan nan nawa sun biya mini bukatuna da kuma na abokan aikina. 35Cikin kowane abin da na yi, na nuna muku cewa da irin wannan aiki tuƙuru don mu taimaki marasa ƙarfi, muna tunawa da kalmomin da Ubangiji Yesu kansa ya ce, ‘Bayarwa ta fi karɓa albarka.’ ”

36Da ya faɗi haka, ya durƙusa tare da dukansu ya yi addu’a. 37Sai dukansu suka yi kuka suka rungume shi, suka kuma yi masa sumba. 38Abin da ya fi sa su baƙin ciki shi ne maganarsa da ya ce, ba za su ƙara ganin fuskarsa ba. Sai suka raka shi zuwa wajen jirgin ruwa.