使徒行傳 13 – CCBT & HCB

Chinese Contemporary Bible (Traditional)

使徒行傳 13:1-52

巴拿巴和掃羅接受差遣

1安提阿教會中有幾位先知和教師,就是巴拿巴、綽號「黑人」的希緬古利奈路求、與分封王希律一同長大的馬念以及掃羅2一天,他們正在敬拜主、禁食的時候,聖靈對他們說:「要為我把巴拿巴掃羅分別出來,好讓他們做我呼召他們去做的事。」 3於是,他們禁食禱告並把手按在巴拿巴掃羅身上,然後差遣他們出去。

4二人受聖靈差遣,下到西流基,從那裡乘船去塞浦路斯5他們到了撒拉米,就在當地的猶太會堂傳講上帝的道。約翰·馬可作他們的助手。

6他們走遍全島,遠至帕弗,在那裡遇見一個冒充先知的猶太術士巴·耶穌7這人和當地的士求·保羅總督常有來往。士求·保羅是個聰明人,他邀請了巴拿巴掃羅來,要聽上帝的道。 8希臘名字叫以呂馬的那個術士反對使徒,試圖攔阻總督信主。 9又名保羅掃羅被聖靈充滿,盯著他說: 10「你這魔鬼的兒子,充滿了詭詐和邪惡,是一切正義之敵,到現在還想歪曲主的正道嗎? 11現在主要親手懲罰你,使你瞎眼,暫時不見天日!」

他頓覺眼前一片漆黑,只好四處摸索,求人領他走路。 12總督看見所發生的事,對主的道感到驚奇,就信了。

保羅傳揚基督

13保羅和同伴從帕弗乘船到旁非利亞別加約翰·馬可在那裡離開他們回耶路撒冷去了。 14他們由別加繼續前行,來到彼西底區的安提阿。在安息日那天,他們進了會堂坐下來。 15讀完律法書和先知書後,會堂主管派人告訴他們:「弟兄們,如果你們有什麼勸勉眾人的話,請講。」

16保羅站起來向大家揮手示意,說:「各位以色列同胞和各位敬畏上帝的外族朋友們,請聽我說。 17以色列的上帝揀選了我們的祖先,讓他們在埃及寄居期間人丁興旺成為大族,後來祂伸出臂膀帶領他們離開埃及18他們在曠野漂泊的那四十年間,上帝一直照顧、容忍他們。 19後來上帝又滅了迦南境內的七族,把土地分給他們作產業。 20前後歷時約四百五十年。之後,上帝又為他們設立士師,直到撒母耳先知的時代。

21「後來,他們求上帝為他們立一位王,上帝就選立便雅憫支派中基士的兒子掃羅為王,執政四十年。 22之後,上帝廢掉掃羅,選立大衛作王,並為他作證說,『我找到了耶西的兒子大衛,他是合我心意的人,他必遵行我一切的旨意。』 23上帝照自己的應許,從大衛的後裔中為以色列人立了一位救主,就是耶穌。 24在耶穌還未公開露面以前,約翰已經勸告以色列人要悔改,接受洗禮。 25約翰在工作快要完成的時候說,『你們以為我是誰?我不是基督。在我之後來的那位,我連給祂解鞋帶也不配。』

26「弟兄們,各位亞伯拉罕的子孫和敬畏上帝的外族人啊,這救恩之道原是傳給我們的。 27可是耶路撒冷的人和他們的官長不知道耶穌是基督,雖然每個安息日都誦讀先知的信息,卻把基督判死罪。這正應驗了先知們的話。 28他們雖然找不到判祂死罪的理由,卻強求彼拉多將祂處死。 29祂受死的記載全部應驗之後,有人把祂從十字架上取下來,安放在石墓裡。 30但上帝卻使祂從死裡復活。 31之後有許多天,那些從加利利跟隨祂上耶路撒冷的人都看見過祂,他們如今在百姓中都是祂的見證人。 32我們要報給你們一個好消息,上帝給我們祖先的應許, 33祂藉著使耶穌復活已為我們做子孫的成就了。正如詩篇第二篇所說,

『你是我的兒子,

我今日成為你父親。』

34聖經曾這樣記載上帝使祂從死裡復活、永不朽壞的事,

『我必將應許大衛的聖潔、

可靠的恩福賜給你們。』

35又在詩篇上說,

『你必不讓你的聖者身體朽壞。』

36大衛在世時遵行上帝的旨意,最後死了,葬在他祖先那裡,肉身也朽壞了。 37然而,上帝使之復活的那位卻沒有朽壞。 38所以,弟兄們,你們應該知道,赦罪的信息是藉著耶穌傳給你們的。 39你們靠遵行摩西律法不能被稱為義人,只有信靠耶穌才能被稱為義人。 40你們要當心,免得先知說的話應驗在你們身上,

41『藐視真理的人啊,看吧!

你們要在驚懼中滅亡,

因為我要在你們的時代行一件事,

即使有人告訴你們,

你們也不會信。』」

42保羅巴拿巴離開會堂時,會堂裡的人請求他們下一個安息日再來講道。 43許多猶太人和誠心改信猶太教的外族人都跟隨保羅巴拿巴,二人就與他們談論,勸勉他們要堅定不移地信靠上帝的恩典。

44到了下一個安息日,幾乎全城的人都聚集起來,要聽上帝的道。 45猶太人看見那麼多人聚集,充滿嫉妒,便反駁保羅所講的,誹謗他。 46保羅巴拿巴毫不畏懼地說:「上帝的道本該先傳給你們,你們既然拒絕接受,認為自己不配得永生,我們現在就把這道傳給外族人。 47因為主這樣吩咐我們,

『我已使你成為外族人的光,

好把救恩帶到地極。』」

48外族人聽後,非常歡喜,頌讚主的道。凡被選定得永生的人都信了主。 49主的道傳遍了那個地方。

50猶太人煽動虔誠的貴婦和城中顯要迫害保羅巴拿巴,將二人趕出城去。 51保羅巴拿巴便當眾跺掉腳上的塵土13·51 表示兩不相干,參見馬太福音10·14,去了以哥念52門徒滿心喜樂,被聖靈充滿。

Hausa Contemporary Bible

Ayyukan Manzanni 13:1-52

1A ikkilisiyar da take a Antiyok akwai waɗansu annabawa da malamai. Barnabas, Siman wanda ake kira Baƙi, Lusiyus mutumin Sairin, Manayen (wanda aka goya tare da Hiridus mai mulki), da kuma Shawulu. 2Yayinda suna cikin sujada da azumi ga Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Ku keɓe mini Barnabas da Shawulu domin aikin da na kira su.” 3Saboda haka bayan suka yi azumi da addu’a, sai suka ɗibiya musu hannuwansu a kansu suka sallame su.

A Saifurus

4Sai su biyu da Ruhu Mai Tsarki ya aika suka gangara zuwa Selusiya suka shiga jirgin ruwa daga can zuwa Saifurus. 5Da suka isa Salamis, sai suka yi shelar maganar Allah a majami’un Yahudawa. Yohanna yana tare da su a matsayin mai taimakonsu.

6Suka zaga dukan tsibirin har sai da suka kai Bafos. A can suka sadu da wani mutumin Yahuda mai sihiri, annabin ƙarya, mai suna Bar-Yesu, 7wanda yake ma’aikacin muƙaddas Sergiyus Bulus ne. Muƙaddas ɗin kuwa mai azanci ne ƙwarai, ya sa aka kira Barnabas da Shawulu don yana so ya ji maganar Allah. 8Amma Elimas mai sihirin nan (domin ma’anar sunansa ke nan) ya yi hamayya da maganarsu ya kuma yi ƙoƙari ya juyar da muƙaddas ɗin daga bangaskiya. 9Sai Shawulu, wanda kuma ake kira Bulus, cike da Ruhu Mai Tsarki, ya kafa wa Elimas ido ya ce, 10“Kai ɗan Iblis ne abokin gāban dukan abin da yake daidai! Kana cike da kowane irin ruɗi da munafunci. Ba za ka daina karkata hanyoyin da suke daidai na Ubangiji ba? 11Ga shi hannun Ubangiji yana gāba da kai. Za ka makance, kuma ba za ka ga rana ba har na wani lokaci.”

Nan take, hazo da duhu suka sauko a kansa, ya yi ta lallubawa, yana neman wanda zai yi masa jagora. 12Sa’ad da muƙaddas ɗin ya ga abin da ya faru, sai ya ba da gaskiya, gama ya yi mamaki a kan da koyarwa game Ubangiji.

A Antiyok na Fisidiya

13Bulus da abokan tafiyarsa suka tashi daga Bafos a jirgin ruwa zuwa Ferga a Famfiliya inda Yohanna ya bar su ya koma Urushalima. 14Daga Ferga kuwa suka ci gaba zuwa Antiyok na Fisidiya. A ranar Asabbaci sai suka shiga majami’a suka zauna. 15Bayan an yi karatu daga cikin Doka, da kuma Annabawa, sai shugabannin majami’ar suka aika musu suka ce, “’Yan’uwa, in kuna da wani saƙon ƙarfafawa domin jama’a, sai ku yi.”

16Yana miƙewa tsaye, sai Bulus ya yi musu alama da hannu ya ce, “Mutanen Isra’ila da kuma ku Al’ummai da kuke wa Allah sujada, ku saurare ni! 17Allahn mutanen Isra’ila ya zaɓi kakanninmu; ya kuma sa mutanen suka yi bunkasa yayinda suke zama a ƙasar Masar, da iko mai girma ya fitar da su daga ƙasar, 18ya kuma jure da halinsu har shekara arba’in a cikin hamada, 19ya tumɓuke ƙasashe bakwai a Kan’ana ya kuma ba da ƙasarsu gādo ga mutanensa. 20Dukan wannan ya ɗauki kusan shekaru 450.

“Bayan wannan, Allah ya ba su alƙalai har zuwa zamanin annabi Sama’ila. 21Sa’an nan mutanen suka nemi a ba su sarki, Allah kuwa ya ba su Shawulu ɗan Kish, na kabilar Benyamin, wanda ya yi mulki shekaru arba’in. 22Bayan an kau da Shawulu, sai ya naɗa Dawuda ya zama sarkinsu. Ya kuma yi shaida game da shi cewa, ‘Na sami Dawuda ɗan Yesse, mutum ne da nake so a zuciyata; shi zai aikata dukan abin da nake so.’

23“Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari. 24Kafin zuwan Yesu, Yohanna ya yi wa’azin tuba da baftisma ga dukan mutanen Isra’ila. 25Yayinda Yohanna yake kammala aikinsa ya ce, ‘Wa kuke tsammani ni nake? Ba ni ne shi ba. A’a, amma yana zuwa bayana, wanda ko takalmansa ma ban isa in kunce ba.’

26“Ya ku ’yan’uwa, ’ya’yan Ibrahim, da ku kuma Al’ummai masu tsoron Allah, a gare mu ne fa aka aiko wannan saƙon ceto. 27Mutanen Urushalima da masu mulkinsu ba su gane da Yesu ba, duk da haka cikin hukunta shi suka cika kalmomin annabawan da ake karantawa kowane Asabbaci. 28Ko da yake ba su same shi da wani dalilin da ya kai ga hukuncin kisa ba, suka roƙi Bilatus yă sa a kashe shi. 29Sa’ad da suka aikata duk abin da aka rubuta game da shi, sai suka saukar da shi daga itacen suka kuma sa shi a kabari. 30Amma Allah ya tashe shi daga matattu, 31kuma kwanaki da yawa waɗanda suka yi tafiya tare da shi daga Galili zuwa Urushalima suka gan shi. Su ne yanzu shaidu ga mutanenmu.

32“Muna gaya muku labari mai daɗi cewa abin da Allah ya yi wa kakanninmu alkawari, 33ya cika mana, mu zuriyarsu, ta wurin tā da Yesu daga matattu. Kamar yadda yake a rubuce a cikin Zabura ta biyu cewa,

“ ‘Kai Ɗana ne,

yau na zama Uba a gare ka.’13.33 Zab 2.7

34Gaskiyar cewa Allah ya tā da shi daga matattu, a kan ba zai taɓa ruɓewa ba, an faɗe shi a cikin waɗannan kalmomi.

“ ‘Zan ba ku tsarki da kuma tabbatattun albarkun da na yi wa Dawuda alkawari.’13.34 Ish 55.3

35Haka kuma aka faɗa a wani wuri.

“ ‘Ba za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.’13.35 Zab 16.10

36“Gama sa’ad da Dawuda ya gama hidimar nufin Allah a zamaninsa, sai ya yi barci; aka binne shi tare da kakanninsa jikinsa kuwa ya ruɓe. 37Amma wanda Allah ya tā da daga matattu bai ruɓa ba.

38“Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi. 39Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba. 40Ku lura kada abubuwan da annabawa suka faɗa su faru muku.

41“ ‘Ku duba, ku masu ba’a,

ku yi mamaki, ku hallaka,

gama zan yi wani abu a zamaninku

da ba za ku taɓa gaskatawa ba

ko da wani ya gaya muku.’13.41 Hab 1.5

42Bulus da Barnabas suna fita daga majami’ar ke nan, sai mutane suka gayyace su su ƙara yin maganan nan a kan waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci mai zuwa. 43Da aka sallami jama’a, Yahudawa da yawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci masu ibada suka bi Bulus da Barnabas, waɗanda suka yi magana musu suka kuma ƙarfafa su su ci gaba a cikin alherin Allah.

44A ranar Asabbaci na biye kusan dukan birnin suka taru don su ji maganar Ubangiji. 45Sa’ad da Yahudawa suka ga taron mutanen, sai suka cika da kishi suka yi ta munanan maganganu a kan abin da Bulus yake faɗi.

46Sai Bulus da Barnabas suka amsa musu gabagadi, suka ce, “Ya zama mana dole mu yi muku maganar Allah da farko. Da yake kun ƙi ta ba ku kuma ga kun cancanci rai madawwami ba, to, za mu juya ga Al’ummai. 47Gama abin da Allah ya umarce mu ke nan cewa,

“ ‘Na sa ka zama haske ga Al’ummai,

don ka kawo cetona zuwa iyakokin duniya.’13.47 Ish 49.6

48Sa’ad da Al’ummai suka ji haka, sai suka yi farin ciki suka ɗaukaka maganar Ubangiji; kuma duk waɗanda aka zaɓa don samun rai madawwami, suka gaskata.

49Maganar Ubangiji kuwa ta bazu a dukan yankin. 50Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu tsoron Allah masu martaba da kuma waɗansu maza masu matsayi a gari. Suka tā da tsanani ga Bulus da Barnabas, suka kore su daga yankinsu. 51Saboda haka suka karkaɗe ƙurar ƙafafunsu don shaidar a kansu suka kuwa tafi Ikoniyum. 52Masu bi kuwa suka cika da farin ciki da kuma Ruhu Mai Tsarki.