马太福音 24 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

马太福音 24:1-51

预言圣殿被毁

1耶稣离开圣殿时,门徒上前把宏伟的圣殿指给祂看。 2耶稣对他们说:“你们看见这殿宇了吗?我实在告诉你们,将来它要被完全拆毁,在这里找不到两块叠在一起的石头。”

世界末日的预兆

3耶稣正坐在橄榄山上,门徒私下来问祂:“请告诉我们,这事什么时候会发生?你再来和世界末日的时候会有什么预兆?”

4耶稣回答说:“你们要小心,免得被人迷惑。 5因为将来会有许多人冒我的名而来,说,‘我是基督’欺骗许多人。 6你们听见战争爆发、战讯频传时,不要惊慌,因为这些事必然发生,只是末日还没有到。 7民族将与民族互斗,国家将与国家相争,各处将有饥荒和地震。 8这些只是灾难24:8 灾难”希腊文是“生产之痛”。的开始。

9“那时,你们将遭人迫害、杀害,并因我的名而被万民憎恨。 10那时,许多人会放弃信仰,互相出卖,彼此憎恨。 11许多假先知也会出现,迷惑许多人。 12由于罪恶泛滥,许多人的爱逐渐冷淡。 13但坚忍到底的必定得救。 14这天国的福音将传遍天下,让万民都听见,然后末日才会来临。

15“当你们看见但以理先知所说的‘那带来毁灭的可憎之物’站立在圣地的时候(读者须会意), 16住在犹太地区的人要赶快逃到山上去, 17在屋顶上的人不要下来进屋收拾行李, 18在田间工作的人也不要回家取外衣。 19那时,孕妇和哺育婴儿的母亲们可就遭殃了! 20你们要祈求上帝,不要让你们在冬天或安息日逃难。 21因为那时世上将有空前绝后的大灾难。 22如果不缩短灾期,恐怕没有人能活命。但为了选民的缘故,灾期必被缩短。

23“那时,如果有人对你们说,‘看啊!基督在这里’,或说,‘基督在那里’,你们不要相信。 24因为假基督和假先知将出现,行很大的神迹奇事来迷惑人,如果可能,甚至要迷惑上帝拣选的子民。 25你们要记住,我已经预先告诉你们了。

26“因此,如果有人对你们说,‘看啊!基督在旷野’,你们不要出去;或者说,‘看啊!基督在屋里’,你们也不要相信。 27人子降临时的情形就像闪电从东方发出一直照到西方。 28尸体在哪里,秃鹰就会聚集在哪里。

29“当灾难的日子一过,

“‘太阳变黑,

月亮无光,

众星陨落,

天体震动。’

30“那时,天上会出现人子降临的预兆,地上的万族都要哀哭,他们将看见人子带着能力和极大的荣耀驾着天上的云降临。 31在响亮的号声中,祂将差遣天使从四面八方、天涯海角招聚祂拣选的人。

无花果树的比喻

32“你们可以从无花果树学个道理。当无花果树发芽长叶的时候,你们就知道夏天快来了。 33同样,当你们看见这一切事发生时,就知道人子快来了,就在门口。 34我实在告诉你们,这个世代还没有过去,这一切都要发生。 35天地都要过去,但我的话永远长存。

警醒准备

36“但没有人知道那日子和时辰何时来到,连天上的天使也不知道,人子24:36 人子”希腊文是“子”。也不知道,只有天父知道。 37人子降临时的情形就像挪亚的时代。 38洪水来临之前,人们吃吃喝喝,男婚女嫁,一直到挪亚进方舟那天; 39他们懵然不知,直到洪水来把他们全冲走了。人子降临时的情形也是这样。 40那时,两个人在田里,一个将被接去,一个将被撇下; 41两个妇人推磨,一个将被接去,一个将被撇下。 42所以,你们要警醒,因为你们不知道你们的主会在哪一天来。 43你们都知道,如果一家的主人知道贼会在半夜几点来,就必警醒,不让贼入屋偷窃。 44同样,你们也要做好准备,因为在你们意想不到的时候,人子就来了。

两种奴仆

45“谁是那个受主人委托管理家中大小仆役、按时分粮食给他们、又忠心又精明的奴仆呢? 46主人回家时,看见他尽忠职守,他就有福了。 47我实在告诉你们,主人一定会把所有产业都交给他管理。 48但如果奴仆邪恶,以为主人不会那么快回来, 49就殴打同伴,跟醉汉一起吃喝玩乐, 50主人会在他想不到的日子、不知道的时辰回来, 51严厉地惩罚24:51 严厉地惩罚”或作“腰斩”。他,判他和伪君子同样的罪。他必在那里哀哭切齿。

Hausa Contemporary Bible

Mattiyu 24:1-51

Alamun ƙarshen zamani

(Markus 13.1,2; Luka 21.5,6)

1Yesu ya bar haikali ke nan, yana cikin tafiya sai almajiransa suka zo wurinsa don su ja hankalinsa ga gine-ginen haikali. 2Sai Yesu ya ce, “Kun ga duk waɗannan abubuwa? Gaskiya nake gaya muku, ba wani dutse a nan da za a bari a kan wani; duk za a rushe.”

(Markus 13.3-13; Luka 21.7-19)

3Da Yesu yana zaune a Dutsen Zaitun, almajiran suka zo wurinsa a ɓoye. Suka ce, “Gaya mana, yaushe ne wannan zai faru, mece ce alamar zuwanka da kuma ta ƙarshen zamani?”

4Yesu ya amsa, “Ku lura fa, kada wani yă ruɗe ku. 5Gama mutane da yawa za su zo cikin sunana, suna cewa, ‘Ni ne Kiristi,’ za su kuwa ruɗi mutane da yawa. 6Za ku ji labarin yaƙe-yaƙe da kuma jita-jitarsu, sai dai ku lura kada hankalinku yă tashi. Dole irin waɗannan abubuwa su faru, amma ƙarshen tukuna. 7Al’umma za tă tasar wa al’umma, mulki yă tasar wa mulki. Za a yi yunwa da girgizar ƙasa a wurare dabam-dabam. 8Dukan waɗannan fa, mafarin azabar naƙudar haihuwa ne.

9“Sa’an nan za a bashe ku don a tsananta muku a kuma kashe ku, dukan al’ummai za su ƙi ku saboda ni. 10A wannan lokaci, da yawa za su juya daga bangaskiya, su ci amana su kuma ƙi juna, 11annabawan ƙarya da yawa za su firfito su kuma ruɗi mutane da yawa. 12Saboda ƙaruwar mugunta, ƙaunar yawanci za tă yi sanyi, 13amma duk wanda ya tsaya da ƙarfi har ƙarshe, zai sami ceto. 14Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.

(Markus 13.14-23; Luka 21.20-24)

15“Saboda haka sa’ad da kuka ga ‘abin ƙyama mai kawo hallaka,’24.15 Dan 9.27; Dan 11.31; Dan 12.11 wanda annabi Daniyel ya yi magana a kai, yana tsaye a tsattsarkan wuri (mai karatu yă gane), 16to, sai waɗanda suke cikin Yahudiya, su gudu zuwa cikin duwatsu. 17Kada wani da yake a kan rufin gidansa, yă sauko don ɗaukar wani abu a gida. 18Kada wani da yake gona kuma yă komo don ɗaukar rigarsa. 19Kaiton mata masu ciki da mata masu renon ’ya’ya a waɗancan kwanakin! 20Ku yi addu’a, kada gudunku yă zama a lokacin sanyi ko a ranar Asabbaci. 21Gama a lokacin za a yi wata matsananciyar wahala, wadda ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har ya zuwa yanzu ba kuwa za a ƙara yi ba.

22“Da ba don an taƙaita kwanakin nan ba, da babu wani da zai tsira, amma saboda zaɓaɓɓun nan, za a taƙaita kwanakin. 23A lokacin in wani ya ce muku, ‘Duba, ga Kiristi nan!’ Ko, ‘Ga shi can!’ Kada ku gaskata. 24Gama Kiristi masu yawa na ƙarya, da annabawan ƙarya za su firfito, su kuma aikata manyan alamu da ayyukan banmamaki don su ruɗi har da zaɓaɓɓu ma in zai yiwu. 25Ga shi, na faɗa muku tun da wuri.

26“Saboda haka in wani ya ce muku, ‘Ga shi can a hamada,’ kada ku fita; ko, ‘Ga shi nan a ɗakunan ciki,’ kada ku gaskata. 27Gama kamar yadda walƙiya take wulgawa walai daga gabas zuwa yamma, haka dawowar Ɗan Mutum zai kasance. 28Duk inda mushe yake, can ungulai za su taru.

(Markus 13.24-27; Luka 21.25-28)

29“Nan da nan bayan tsabar wahalan nan

“ ‘sai a duhunta rana,

wata kuma ba zai ba da haskensa ba;

taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama,

za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’24.29 Ish 13.10; Ish 34.4

30“A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma. 31Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.

(Markus 13.28-31; Luka 21.29-33)

32“Yanzu fa, sai ku koyi wannan darasi daga itacen ɓaure. Da zarar rassansa suka yi taushi ganyayensa kuma suka toho, kun san damina ta kusa. 33Haka kuma, sa’ad da kun ga dukan waɗannan abubuwa, ku sani ya yi kusan zuwa, yana ma dab da bakin ƙofa. 34Gaskiya nake gaya muku, wannan zamani ba zai shuɗe ba sai dukan abubuwan nan sun faru. 35Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za tă taɓa shuɗe ba.

Rana ko sa’a ba a sani ba

(Markus 13.32-37; Luka 17.26-30,34-35)

36“Babu wanda ya san wannan rana ko sa’a, ko mala’ikun da suke sama ma, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai. 37Kamar yadda ya faru a zamanin Nuhu, haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 38Gama a kwanaki kafin ruwan tsufana, mutane sun yi ta ci, sun kuma yi ta sha, suna aure, suna kuma aurarwa, har zuwa ranar da Nuhu ya shiga jirgi; 39ba su kuwa san abin da yake faruwa ba sai da ruwan tsufana ya zo ya share su tas. Haka zai zama a dawowar Ɗan Mutum. 40Maza biyu za su kasance a gona; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya. 41Mata biyu za su kasance suna niƙa; za a ɗau ɗaya a bar ɗaya.

42“Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba. 43Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida. 44Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.

(Luka 12.35-48)

45“Wane ne bawan nan mai aminci da kuma mai hikima, wanda maigida ya sa yă lura da bayi a cikin gidansa, yă riƙa ba su abinci a daidai lokaci? 46Zai zama wa bawan nan da kyau in maigidan ya dawo ya same shi yana yin haka. 47Gaskiya nake gaya muku, zai sa shi yă lura da dukan dukiyarsa. 48Amma in wannan bawa mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Maigidana ba zai dawo da wuri ba.’ 49Sa’an nan yă fara dūkan ’yan’uwansa bayi, yana ci yana kuma sha tare da mashaya. 50Maigidan wannan bawa zai dawo a ranar da bai yi tsammani ba, a sa’ar kuma da bai sani ba. 51Maigidan zai farfasa masa jiki da bulala, yă kuma ba shi wuri tare da munafukai, inda za a yi kuka da cizon haƙora.