罗马书 9 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

罗马书 9:1-33

上帝的选民

1我在基督里说真话,绝无谎言。我被圣灵感动的良心可以作证, 2我心里极为忧愁,痛苦不止! 3为了我的弟兄——我的同胞以色列人,即使我自己被咒诅、与基督隔绝,我也愿意! 4身为以色列人,他们拥有上帝儿子的名分、上帝的荣耀、诸约、律法、圣殿敬拜和各种应许。 5蒙拣选的族长是他们的先祖,基督降世为人也是做以色列人。祂是至大至尊,永远当受称颂的上帝。阿们!

6当然,这并不表示上帝的话落了空,因为从以色列生的,不一定都是以色列人, 7亚伯拉罕的后裔不一定都是亚伯拉罕的儿女,圣经上说:“以撒生的才可算为你的后裔。” 8这话的意思是:亚伯拉罕凭血气所生的儿女并不是上帝的儿女,只有凭应许所生的才算是他的后裔。 9因为上帝曾这样应许他:“明年这时候,我会再来,撒拉必生一个儿子。”

10后来,利百加和我们的先祖以撒结婚,怀了双胞胎。 11在这对孩子还未出生,还没有显出谁善谁恶之前,上帝为了显明自己拣选人并不是按人的行为,而是按祂自己的旨意, 12便对利百加说:“将来大的要服侍小的。” 13正如圣经上说:“我爱雅各,厌恶以扫。”

14这样看来,我们该怎么下结论呢?难道上帝不公平吗?当然不是! 15祂曾对摩西说:

“我要怜悯谁就怜悯谁,

要恩待谁就恩待谁。”

16可见这并不在于人的意志和努力,而在于祂的怜悯。 17圣经记载着上帝对法老说的话:“我使你兴起是为了在你身上彰显我的权能,使我的名传遍天下。” 18总之,上帝要怜悯谁,就怜悯谁;要叫谁顽固,就叫谁顽固。

上帝的烈怒和怜悯

19这样,你肯定会对我说:“为什么上帝还指责人呢?谁能抗拒祂的旨意呢?” 20你这个人啊!你是谁啊?竟敢顶撞上帝!受造之物怎能对造物主说:“你为什么把我造成这样?” 21陶匠难道不可以从一团泥中拿一部分造贵重的器皿,又拿一部分造平凡的器皿吗?

22倘若上帝要显示祂的烈怒和权能,就尽量容忍那些祂预备要毁灭的器皿, 23以便在那些祂怜悯并预备赐予荣耀的器皿上彰显祂丰盛的荣耀,这难道不可以吗? 24那些蒙怜悯的器皿就是我们这些从犹太人和外族人中被上帝呼召的人。 25正如上帝在《何西阿书》上说:

“本来不是我子民的,

我要称他们为‘我的子民’;

本来不是我所爱的,

我要称他们为‘我所爱的’。

26从前我在什么地方对他们说,

‘你们不是我的子民。’

将来也要在那里对他们说,

‘你们是永活上帝的儿女。’”

27关于以色列人,以赛亚先知曾疾呼:

以色列人虽多如海沙,

但得救的只是剩余的人,

28因为上帝要在世上迅速、

彻底地执行祂的判决。”

29以赛亚又说:

“若不是万军之主给我们存留后裔,

我们早就像所多玛蛾摩拉一样灭亡了。”

以色列人和福音

30这样看来,我们该说什么呢?本来不追求义的外族人却因信而得到了义。 31以色列人靠遵行律法追求义,却徒劳无功。 32为什么会这样呢?因为他们不凭信心,只靠自己的行为去追求义,结果就在那块“绊脚石”上跌倒了。 33正如圣经上说:

“看啊!我在锡安放了一块绊脚石,

一块使人跌倒的磐石。

但信靠祂的人必不致蒙羞。”

Hausa Contemporary Bible

Romawa 9:1-33

Zaɓen Allah mai iko duka

1Ina faɗin gaskiya a cikin Kiristi ba ƙarya nake yi ba, lamirina ya tabbatar da wannan a cikin Ruhu Mai Tsarki. 2Ina da baƙin ciki mai yawa da kuma rashin kwanciyar rai marar ƙarewa a zuciyata. 3Gama da so na ne, sai a la’anta ni a kuma raba ni da Kiristi saboda ’yan’uwana, waɗannan na kabilata, 4mutanen Isra’ila. Su ne Allah ya mai da su ’ya’yansa, ya bayyana musu ɗaukakarsa, ya ba su alkawarinsa da Dokarsa, ya nuna musu hanyar sujada ta gaske, ya kuma ba su sauran alkawura. 5Kakannin-kakannin nan kuma nasu ne, Kiristi kuma, ta wurin zamansa mutum, na kabilarsu ne. Yabo ya tabbata ga Allah har abada, shi da yake bisa kome! Amin.

Zaɓin Allah mai iko duka

6Ba cewa maganar Allah ta kāsa ba ne. Gama ba duk waɗanda suke zuriyar Isra’ila ne suke Isra’ila na gaske ba. 7Ba kuwa don su zuriyarsa ne dukansu suka zama ’ya’yan Ibrahim ba. A maimako, “Ta wurin Ishaku ne za a lissafta zuriyarka.” 8Ana iya cewa zaman zuriyar Ibrahim, ba shi ne zama ’ya’yan Allah ba, a’a, zuriya ta alkawarin nan su ne ake lasaftawa zuriyar Ibrahim. 9Ga yadda aka yi alkawarin nan, “A ƙayyadadden lokaci zan dawo, Saratu kuma za tă haifi ɗa.”9.9 Far 18.10,14

10Ba ma haka kaɗai ba, ’ya’yan Rifkatu suna da mahaifi guda ne, wato, mahaifinmu Ishaku. 11Duk da haka, tun ba a haifi tagwayen nan ba, balle su yi wani abu mai kyau ko marar kyau don nufin Allah bisa ga zaɓensa ya tabbata, ba ga aikin lada ba, sai dai ga kiransa, 12ba ta wurin ayyuka ba sai dai ta wurin shi wanda ya kira, aka faɗa mata cewa, “Babban zai bauta wa ƙaramin.”9.12 Far 25.23 13Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaƙub ne na so, amma Isuwa ne na ƙi.”9.13 Mal 1.2,3

14Me za mu ce ke nan? Allah marar adalci ne? Sam, ko kaɗan! 15Gama ya ce wa Musa,

“Zan nuna jinƙai ga wanda zan nuna jinƙai,

zan kuma ji tausayin wanda zan ji tausayi.”9.15 Fit 33.19

16Saboda haka, bai danganta ga sha’awar mutum ko ƙoƙarinsa ba, sai dai ga jinƙan Allah. 17Gama Nassi ya ce wa Fir’auna, “Na ɗaga ka saboda wannan manufa, saboda in nuna ikona a cikinka domin kuma a shaida sunana a duniya duka.”9.17 Fit 9.16 18Saboda haka Allah yana nuna jinƙai ga wanda yake so, yana kuma taurara zuciyar wanda yake so.

19Waninku zai iya ce mini, “To, don me har yanzu Allah yake ganin laifinmu? Gama wa zai iya tsayayya da nufinsa?” 20Amma wane ne kai, ya mutum, da za ka mayar wa Allah magana? “Ashe, abin da aka gina zai iya ce wa wanda ya gina shi, ‘Don me ka gina ni haka?’ ”9.20 Ish 29.16; Ish 45.9 21Ashe, mai ginin tukwane ba shi da iko yin amfani da yumɓu guda yă gina tukunya domin ayyuka masu daraja da kuma waɗansu don ayyuka marasa daraja?

22Haka ma aikin Allah yake. Ya so yă nuna fushinsa yă kuma sanar da ikonsa, ya yi haka cikin haƙuri ƙwarai ga waɗanda suka cancanci fushinsa, waɗanda aka shirya domin hallaka? 23Haka kuma ya so yă sanar da wadatar ɗaukakarsa ga waɗanda suka cancanci jinƙansa, waɗanda ya shirya tun kafin lokaci don ɗaukaka 24har da mu ma, mu da ya kira, ba daga cikin Yahudawa kaɗai ba amma har ma daga cikin Al’ummai? 25Kamar yadda ya faɗa a Hosiya.

“Zan kira su ‘mutanena,’ su da ba mutanena ba;

zan kuma kira ta ‘ƙaunatacciyata,’ ita da ba ƙaunatacciyata ba,”9.25 Hos 2.23

26kuma,

“Zai zama cewa a daidai inda aka ce musu,

‘Ku ba mutanena ba,’

za a ce da su, ‘’ya’yan Allah mai rai.’ ”9.26 Hos 1.10

27Ishaya ya ɗaga murya game da Isra’ila ya ce,

“Ko da yake yawan Isra’ilawa yana kama da yashi a bakin teku,

ragowa ce kaɗai za su sami ceto.

28Gama Ubangiji zai zartar da

hukuncinsa a bisan duniya da sauri kuma ba da ɓata lokaci ba.”9.28 Ish 10.22,23

29Yana nan kamar yadda Ishaya ya riga ya faɗa.

“Da ba don Ubangiji Maɗaukaki

ya bar mana zuriya ba,

da mun zama kamar Sodom,

da mun kuma zama kamar Gomorra.”9.29 Ish 1.9

Rashin bangaskiyar Isra’ila

30Me za mu ce ke nan? Ai, Al’ummai da ba su nemi adalci ba, sun same shi, adalcin da yake ta wurin bangaskiya; 31amma Isra’ila da suka yi ƙwazo wajen bin Dokar adalci, ba su same shi ba. 32Don me? Domin sun yi ƙwazo wajen binta ba ta wurin bangaskiya ba sai dai ta wurin ayyuka. Sun yi tuntuɓe a kan “dutsen sa tuntuɓe.” 33Kamar yadda yake a rubuce,

“Ga shi, na sa dutse a Sihiyona da yake sa mutane yin tuntuɓe

da kuma dutsen da yake sa su fāɗi

wanda kuwa ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.”9.33 Ish 8.14; Ish 28.16