约翰福音 15 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

约翰福音 15:1-27

真葡萄树

1耶稣说:“我是真葡萄树,我父是栽培的人。 2属于我的枝子如果不结果子,祂就把它剪掉;如果结果子,祂便修剪它,让它结更多的果子。 3我对你们所讲的道已经使你们洁净了。 4你们要常在我里面,我就常在你们里面。枝子若离开葡萄树,就不能结果子。同样,你们若不常在我里面,也不能结果子。

5“我是葡萄树,你们是枝子。常在我里面的,我也常在他里面,他就会多结果子,因为你们离开了我什么都不能做。 6不常在我里面的人就像丢在外面枯干的枝子,最后只有被人拾起来丢在火里烧掉。 7如果你们常在我里面,我的话也常在你们里面,无论你们求什么,都会得到应允。 8你们多结果子,证明自己是我的门徒,就会给我父带来荣耀。 9父怎样爱我,我也怎样爱你们。你们要常在我的爱中。 10你们若遵守我的命令,就必常在我的爱中,正如我遵守了父的命令,常在父的爱中一样。

11“我把这些事告诉你们,是要叫你们心里有我的喜乐,让你们的喜乐满溢。 12你们要彼此相爱,像我爱你们一样,这就是我的命令。 13为朋友舍命可以说是人间最伟大的爱了。 14你们如果照我的吩咐去做,就是我的朋友。 15我不再称你们为奴仆,因为奴仆不知道主人的事。我称你们为朋友,因为我把从父那里听见的一切都告诉了你们。 16不是你们拣选了我,而是我拣选了你们,并且派你们出去结永存的果子。这样,你们奉我的名无论向父求什么,祂都会赐给你们。 17我把这些事吩咐你们,是要叫你们彼此相爱。

被世人憎恶

18“如果世人恨你们,要知道,他们恨你们以前已经恨我了。 19如果你们属于这个世界,世人一定会爱你们。可是你们不属于这世界,我已经把你们拣选出来,因此世人恨你们。 20你们要记住我说的话,‘奴仆不能大过主人。’他们若迫害我,也必迫害你们;他们若遵行我的话,也必遵行你们的话。 21世人将因为我的名而这样对待你们,因为他们不认识差我来的那位。 22我如果没有来教导他们,他们就没有罪了,但现在他们的罪无可推诿。 23恨我的,也恨我的父。 24我如果没有在他们当中行过空前的神迹,他们就没有罪了。然而,他们亲眼看见了,竟然还恨我和我的父。 25这是要应验他们律法书上的话,‘他们无故地恨我。’

26“我要从父那里为你们差护慰者来,祂就是从父而来的真理之灵。祂来了要为我做见证。 27你们也要为我做见证,因为你们从开始就与我在一起。

Hausa Contemporary Bible

Yohanna 15:1-27

Itacen inabi da kuma rassa

1“Ni ne kuringar inabi na gaskiya, Ubana kuwa shi ne manomin. 2Yakan sare kowane reshe a cikina da ba ya ’ya’ya, amma yakan ƙundume kowane reshe da yake ba da ’ya’ya, domin yă ƙara ba da ’ya’ya. 3Kun riga kun zama masu tsabta saboda maganar da na yi muku. 4Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.

5“Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba. 6Duk wanda bai kasance a cikina ba, yana kamar reshen da aka jefar yă bushe; irin waɗannan rassan ne akan tattara, a jefa cikin wuta a ƙone. 7In kun kasance a cikina kalmomina kuma suka kasance a cikinku, ku roƙi kome da kuke so, za a kuwa ba ku. 8Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.

9“Kamar yadda Uba ya ƙaunace ni, haka ni ma na ƙaunace ku. To, fa, ku kasance cikin ƙaunata. 10In kuka yi biyayya da umarnaina, za ku kasance a cikin ƙaunata, kamar dai yadda na yi biyayya da umarnan Ubana na kuma kasance a cikin ƙaunarsa. 11Na gaya muku wannan domin murnata ta kasance a cikinku, murnanku kuma ta zama cikakkiya. 12Umarnina shi ne, Ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku. 13Babu ƙaunar da ta fi wannan, a ce mutum ya ba da ransa saboda abokansa. 14Ku abokaina ne, in kun yi abin da na umarta. 15Ba zan ƙara ce da ku bayi ba, don bawa bai san abin da maigidansa yake yi ba. A maimako in ce da ku abokai, domin na sanar da ku duk abin da na ji daga wurin Ubana. 16Ba ku kuka zaɓe ni ba, a’a, ni ne na zaɓe ku na kuma naɗa ku ku je ku ba da ’ya’ya-’ya’yan da za su dawwama. Uba kuwa zai ba ku duk abin da kuka roƙa cikin sunana. 17Umarnina ke nan. Ku ƙaunaci juna.

Duniya ta ƙi jinin almajirai

18“In duniya ta ƙi ku, ku san cewa ta fara ƙin na ne. 19Da ku na duniya ne, da ta ƙaunaci abinta. Kamar yadda yake, ku ba na duniya ba ne, na zaɓe ku daga duniya, shi ya sa duniya take ƙinku. 20Ku tuna da kalmomin da na yi muku cewa, ‘Ba bawan da ya fi maigidansa,’15.20 Yoh 13.16 In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun yi biyayya da koyarwata, da za su yi biyayya da taku ma. 21Za su yi muku haka saboda sunana, gama ba su san Wannan da ya aiko ni ba. 22Da a ce ban zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Yanzu kam, ba su da wata hujja a kan zunubinsu. 23Wanda ya ƙi ni ya ƙi ya ƙi Ubana ma. 24Da a ce ban yi ayyuka a cikinsu waɗanda babu wani da ya taɓa yi ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu sun ga waɗannan ayyukan banmamaki, duk da haka sun ƙi ni sun kuma ƙi Ubana. 25Amma wannan ya faru ne domin a cika abin da yake a rubuce cikin Dokarsu cewa, ‘Sun ƙi ni ba dalili.’15.25 Zab 35.19; Zab 69.4

Aikin Ruhu Mai Tsarki

26“Sa’ad da Mai Taimako ya zo, wanda zan aiko muku daga wurin Uba, Ruhun gaskiya wanda yake fitowa daga wurin Uba, zai ba da shaida game da ni. 27Ku ma dole ku ba da shaida, domin kun kasance tare da ni tun daga farko.