约翰一书 2 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

约翰一书 2:1-29

1我的孩子们,我写这些话给你们是为了叫你们不要犯罪。如果有人犯了罪,在父那里我们有一位护慰者,就是那位义者——耶稣基督。 2祂为我们的罪作了赎罪祭,不只是为我们的罪,也是为全人类的罪。

3我们若遵行上帝的命令,就知道自己认识祂。 4若有人说“我认识祂”,却不遵行祂的命令,这人是说谎的,他心中没有真理。 5遵行主话语的人是真正全心爱上帝的人,我们借此知道自己是在主里面。 6所以,自称住在主里面的,就该在生活中效法基督。

新命令

7亲爱的弟兄姊妹,我写给你们的并不是一条新命令,而是你们起初接受的旧命令,这旧命令就是你们已经听过的真道。 8然而,我写给你们的也是新命令,在基督和你们身上都显明是真实的,因为黑暗渐渐过去,真光已经照耀出来。

9若有人说自己在光明中,却恨他的弟兄姊妹,他就仍然活在黑暗里。 10爱弟兄姊妹的人活在光明中,没有什么可以绊倒他2:10 没有什么可以绊倒他”或译“他也不会绊倒别人”。11恨弟兄姊妹的人活在黑暗中,走在黑暗中,不知何去何从,因为黑暗弄瞎了他的眼睛。

12孩子们,我写信给你们,因为靠着祂的名,你们的罪已经得到赦免。 13父老们,我写信给你们,因为你们认识了从太初就存在的那位。年轻人,我写信给你们,因为你们已经战胜了那恶者。

14孩子们,我曾写信给你们,因为你们认识了父。父老们,我曾写信给你们,因为你们认识了从太初就存在的那位。年轻人,我曾写信给你们,因为你们刚强,上帝的道常存在你们心里,并且你们战胜了那恶者。

15不要爱世界和世上的事,因为人若爱世界,就不会再有爱父的心了。 16凡属世界的,如肉体的私欲、眼目的私欲和今生的骄傲都不是从父那里来的,而是从世界来的。 17这世界和其中一切的私欲都要过去,但遵守上帝旨意的人永远长存。

防备敌基督者

18孩子们,现在是末世了。你们从前听说敌基督者要来,其实现在许多敌基督者已经出现了,由此可知,现在是末世了。 19这些人是从我们中间出去的,但他们不属于我们。他们如果属于我们,就会留在我们当中了。他们的离去表明他们都不属于我们。

20你们从那位圣者领受了圣灵2:20 圣灵”希腊文指“膏抹”。,所以你们明白真理。 21我写信给你们不是因为你们不明白真理,而是因为你们明白真理,并且知道真理里面绝对没有谎言。 22谁是说谎的呢?不就是那否认耶稣是基督的吗?那不承认父和子的就是敌基督者。 23凡否认子的,也否认了父;凡承认子的,也承认了父。

24你们务要把起初所听见的教导谨记在心,这样,你们必住在子和父里面。 25主应许给我们的是永生。 26以上的话是针对那些引诱你们离开正道的人写的。

顺从圣灵

27你们既然从主领受了圣灵,圣灵又住在你们心中,就不需要其他人来教导你们,因为圣灵必会在一切事上指引你们。圣灵的教导是真实的,没有虚假,你们要按圣灵的教导住在主里面。 28孩子们,你们要住在主里面。这样,当主显现的时候,就是祂再来的时候,我们便能坦然无惧,不会在祂面前羞愧。 29既然你们知道主是公义的,也该知道所有按公义行事的人都是上帝的儿女。

Hausa Contemporary Bible

1 Yohanna 2:1-29

1’Ya’yana ƙaunatattu, ina rubuta muku wannan ne don kada ku yi zunubi. Amma in wani ya yi zunubi, muna da wani wanda yake magana da Uba don taimakonmu, wato, Yesu Kiristi, Mai Adalci. 2Shi ne hadayar kafara saboda zunubanmu, kuma ba don namu kaɗai ba amma har ma da zunuban duniya duka.

3Ta haka za mu tabbata cewa mun san shi in muna yin biyayya da umarnansa. 4Mutumin da ya ce, “Na san shi,” amma ba ya yin abin da ya umarta, maƙaryaci ne, gaskiya kuwa ba ta cikinsa. 5Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa. 6Duk wanda ya ce yana rayuwa a cikinsa dole yă yi tafiya kamar yadda Yesu ya yi.

7Abokaina ƙaunatattu, ba sabon umarni nake rubuta muku ba, a’a, daɗaɗɗen umarnin nan ne, wanda kuke da shi tun farko. Wannan tsohon umarni shi ne saƙon da kuka riga kuka ji. 8Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma cikinku, gama duhu yana shuɗewa, haske na gaskiya kuwa yana haskakawa.

9Duk wanda ya ce yana cikin haske yana kuma ƙin ɗan’uwansa, ashe a duhu yake har yanzu. 10Duk wanda yake ƙaunar ɗan’uwansa, a cikin hasken yake rayuwa ke nan, kuma babu wani abin da yake cikinsa da zai sa yă yi tuntuɓe. 11Amma duk wanda yake ƙin ɗan’uwansa, cikin duhu yake, yana kuma tafiya cikin duhu ke nan; bai ma san inda za shi ba, domin duhun ya makanta shi.

12Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu,

domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.

13Ina rubuta muku, ubanni,

domin kun san shi wanda yake tun farko.

Ina rubuta muku, samari,

domin kun ci nasara a kan mugun nan.

14Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu,

domin kun san Uba.

Ina rubuta muku, ubanni,

domin kun san shi wanda yake tun farko.

Ina rubuta muku, samari,

domin kuna da ƙarfi,

maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku,

kun kuma ci nasara a kan mugun nan.

Kada ku ƙaunaci duniya

15Kada ku ƙaunaci duniya, ko wani abin da yake cikinta. In wani yana ƙaunar duniya, ƙaunar Uba ba ta cikinsa. 16Gama duk abin da yake na duniya, kamar sha’awace-sha’awacen mutuntaka, sha’awar idanunsa, da kuma taƙama da abin da yake da shi, yake kuma yi, ba daga wurin Uba suke fitowa ba sai dai daga duniya. 17Duniya da sha’awace-sha’awacenta suna shuɗewa, amma mutumin da yake aikata nufin Allah, zai rayu har abada.

Gargaɗi a kan magabcin Kiristi

18’Ya’yana ƙaunatattu, waɗannan su ne kwanakin ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma abokan gāban Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa kwanakin ƙarshe sun iso. 19Waɗannan masu gāba da Kiristi suna cikinmu a dā, amma sun bar mu, don tun dā ma su ba namu ba ne. Ai, da su namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun bar mu, wannan ya nuna a fili cewa su ba namu ba ne.

20Amma ku kam, kuna da shafewa daga wurin Mai Tsarkin nan, kuma dukanku kun san gaskiya. 21Ina rubuta muku ba domin ba ku san gaskiya ba ne, a’a, sai dai domin kun santa, kun kuma san cewa babu yadda ƙarya za tă fito daga gaskiya. 22Wane ne maƙaryaci? Ai, shi ne mutumin da yake mūsun cewa Yesu shi ne Kiristi. Irin wannan mutum shi ne magabcin Kiristi, ya yi mūsun Uban da kuma Ɗan. 23Ba wanda yake mūsun Ɗan, sa’an nan yă ce yana da Uban; duk wanda ya yarda da Ɗan, yana da Uban a cikinsa ke nan.

24Ku lura fa cewa abin da kuka ji daga farko, bari yă ci gaba da kasance a cikinku. In kuwa ya ci gaba da zama a cikinku, za ku kasance a cikin Ɗan, da kuma a cikin Uban. 25Wannan shi ne abin da ya yi mana alkawari, wato, rai madawwami.

26Ina rubuta muku waɗannan abubuwa ne game da waɗanda suke ƙoƙari su sa ku kauce. 27Game da ku kuwa, shafan nan da kuka karɓa daga gare shi tana nan a cikinku, ba kwa kuma bukata wani yă koyar da ku. Amma kamar yadda shafan nan tasa tana koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.

’Ya’yan Allah

28Yanzu fa, ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, sai ku ci gaba a cikinsa, domin sa’ad da ya bayyana, mu iya tsaya gabagadi babu kunya a dawowarsa.

29In kun san cewa shi mai adalci ne, to, kun dai san cewa duk mai aikata abin da yake daidai haifaffensa ne.