提摩太前书 4 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

提摩太前书 4:1-16

谨防伪君子

1圣灵明确地说,日后必有人离弃真道,去追随那些迷惑人的邪灵和鬼魔的学说。 2这些学说是出自假冒伪善的骗子,他们良心丧尽,麻木不仁4:2 良心丧尽,麻木不仁”希腊文是“良心被烙铁烫过”。3禁止人结婚和吃某些食物。其实那些食物是上帝创造的,为了让相信并且明白真理的人存感谢的心领受。 4上帝所造的一切都是美好的,若以感恩的心去领受,就无需任何禁忌, 5因为上帝的道和人的祷告可以使食物圣洁。

6你要提醒弟兄姊妹这些事,这样你就是基督耶稣的好仆人,会不断地从你所信的真道和所遵行的美好教导上得到造就。

做信徒的榜样

7但你要弃绝世俗、荒诞的传说,要训练自己做个敬虔的人。 8锻炼体魄益处还少,敬虔生活受益无穷,拥有今生和永世的应许。 9这话真实可信,值得完全接受。 10我们努力奋斗正是为了这个目的,因为我们的盼望在于永活的上帝。祂是全人类的救主,更是信徒的救主。 11你要吩咐和教导这些事。

12不要因为年轻而叫人小看你,总要在言语、行为、爱心、信心和纯洁各方面做信徒的榜样。 13在我来之前,你要专心宣读圣经,勉励会众,教导真理。 14不要忽略你的恩赐,那是借着预言在众长老把手按在你身上时赐给你的。 15你要全心全意地做这些事,让大家都看到你的长进。 16你要注意自己的言行和教导,要持之以恒。这样,你不但能救自己,也能救那些听你教导的人。

Hausa Contemporary Bible

1 Timoti 4:1-16

Umarnai ga Timoti

1Ruhu a sarari ya faɗa cewa a kwanakin ƙarshe waɗansu za su watsar da bangaskiya su bi ruhohi masu ruɗu da kuma abubuwan da aljanu suke koyarwa. 2Irin koyarwan nan tana zuwa ne daga waɗansu munafukai maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu kaca-kaca. 3Suna hana mutane yin aure suna kuma umarce su kada su ci waɗansu irin abinci, waɗanda Allah ya halitta don waɗanda suka gaskata suka kuma san gaskiya, su karɓa da godiya. 4Gama duk abin da Allah ya halitta yana da kyau, kada kuma a ƙi kome in dai an karɓe shi da godiya, 5domin an tsarkake shi ta wurin maganar Allah da kuma addu’a.

6In ka nuna wa ’yan’uwa waɗannan abubuwa, za ka zama mai hidima mai kyau na Kiristi Yesu, wanda aka goya cikin gaskiyar bangaskiya da kuma koyarwa mai kyau wadda ka bi. 7Ka kiyaye kanka daga tatsuniyoyi na rashin tsoron Allah da labaru banza na tsofaffin mata; a maimako, ka hori kanka ga zama mai tsoron Allah. 8Gama horon jiki yana da amfani, amma tsoron Allah yana da amfani ga kowane abu, yana da albarka ga rai na yanzu da kuma rai mai zuwa. 9Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa. 10Saboda wannan kuwa muke wahala da kuma fama, domin mun sa begenmu ga Allah mai rai, wanda yake Mai Ceton dukan mutane, musamman na waɗanda suka ba da gaskiya.

11Ka umarta ka kuma koyar da waɗannan abubuwa. 12Kada ka bar wani yă rena ka domin kai matashi ne, sai dai ka zama gurbi ga masu bi cikin magana, cikin rayuwa, cikin ƙauna, cikin bangaskiya da kuma cikin zaman tsarki. 13Kafin in zo, ka ci gaba da karanta wa mutane Nassi, da yin wa’azi, da kuma koyarwa. 14Kada ka yi sakaci da baiwarka, wadda aka ba ka ta wurin saƙon annabci sa’ad da ƙungiyar dattawa suka ɗibiya hannuwa a kanka.

15Ka yi ƙwazo cikin waɗannan batuttuwa; ka ba da kanka gaba ɗaya gare su, don kowa yă ga ci gabanka. 16Ka kula da rayuwarka da kuma koyarwarka da kyau. Ka daure a cikinsu, domin in ka yi, za ka ceci kanka da kuma masu sauraronka.