提多书 1 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

提多书 1:1-16

问候

1保罗做上帝的奴仆和耶稣基督的使徒,是为了使上帝拣选的人有信心、明白真理,从而过敬虔的生活, 2有永生的盼望。这永生是从不说谎的上帝在亘古以前应许的。 3祂在所定的时候,借着人的传扬将自己的道显明出来。我奉我们救主上帝的命令传扬这道。

4提多啊,我写信给你,就我们共同的信仰来说,你是我真正的儿子。

愿父上帝和我们的救主基督耶稣赐给你恩典和平安!

长老的资格

5当初,我把你留在克里特岛,是要你完成未办完的事工,并照我的指示在各城选立长老。 6做长老的必须无可指责,只有一位妻子,儿女都信主、没有放荡不羁的行为。 7身为上帝的管家,做监督的必须无可指责,不傲慢,不暴躁,不酗酒,不好斗,不贪财。 8他必须好客、乐善、自制、正直、圣洁、自律, 9持守所领受的真道,以便能够以纯正的教导劝勉人,驳倒那些反对的人。

10因为有许多悖逆之人喜欢空谈,善于欺骗,尤其是那些奉行割礼的人。 11你一定要堵住他们的口,因为他们为了不义之财教不该教的,误导了别人全家。 12克里特人自己的一位先知说:“克里特人说谎成性,邪恶如兽,好吃懒做。” 13这话是真的。因此你要严正地斥责他们,使他们有纯正的信仰, 14不理会犹太人荒诞的传说和那些违背真理之人的诫律。 15对洁净的人而言,一切都是洁净的;对污秽不信的人而言,什么都不洁净,连他们的思想和良心都是污秽的。 16他们自称认识上帝,在行为上却否认祂。他们令人可憎,悖逆成性,一无是处。

Hausa Contemporary Bible

Titus 1:1-16

1Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah 2duk wannan kuwa saboda begen nan ne ga rai madawwami da Allah ya yi alkawari tun fil azal, shi wanda ƙarya ba ta a gare shi, 3da lokacin da Allah ya zaɓa ya cika sai ya bayyana maganarsa a sarari ta wurin wa’azin da aka danƙa mini amana ta wurin umarnin Allah Mai Cetonmu,

4Zuwa ga Titus, ɗana na gaske a tarayyarmu cikin bangaskiya.

Alheri da salama daga Allah Uba da kuma Kiristi Yesu Mai Cetonmu, su kasance tare da kai.

Aikin Titus a Kirit

5Dalilin da ya sa na bar ka a Kirit shi ne don ka daidaita abubuwan da suka rage da ba a kammala ba, ka kuma naɗa dattawa a kowane gari, yadda na umarce ka. 6Dole dattijo yă kasance marar aibi, mijin mace guda, mutumin da ’ya’yansa masu bi ne, waɗanda kuma ba a san su da lalata ko rashin biyayya ba. 7Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba. 8A maimakon haka dole yă zama mai karɓan baƙi, mai son abu nagari, mai kamunkai, mai adalci, mai tsarki da kuma natsattse. 9Dole yă riƙe tabbataccen saƙon nan kam-kam yadda aka koyar, don yă iya ƙarfafa waɗansu da sahihiyar koyarwa yă kuma ƙaryata waɗanda suke gāba da shi.

Tsawata wa waɗanda suka ƙi yin nagarta

10Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya. 11Dole a hana su yin magana, domin suna kawo rushewar iyalai ta wurin koyar da abubuwan da bai kamata su koyar ba don neman ƙazamar riba. 12Wani daga cikin annabawansu ma ya ce, “Kiretawa a kullum maƙaryata ne, mugayen dabbobi, ragwaye haɗamammu.” 13Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsawata musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya, 14ba za su kuma mai da hankalinsu ga tatsuniyoyin Yahudawa ko ga umarnan waɗanda suke ƙin gaskiya ba. 15Ga tsarkaka kuwa, kome mai tsarki ne, amma ga waɗanda suke marasa tsarki da kuma marasa ba da gaskiya, ba abin da yake da tsarki. Gaskiya dai, hankulansu da lamirinsu duk marasa tsarki ne. 16Sun ɗauka cewa sun san Allah, amma ta wurin ayyukansu suna mūsunsa. Sun zama abin ƙyama, marasa biyayya, ba su ma isa su yi aiki nagari ba.