希伯来书 13 – CCB & HCB

Chinese Contemporary Bible (Simplified)

希伯来书 13:1-25

做上帝喜悦的事

1你们要继续彼此相爱,情同手足。 2不要忘记款待客旅,因为曾经有人接待客旅时不知不觉接待了天使。 3要设身处地地顾念那些被囚禁的人,要感同身受地顾念那些遭遇苦难的人。

4人人都要尊重婚姻,不可玷污夫妻关系13:4 夫妻关系”希腊文是“婚姻的床”。,因为上帝必审判淫乱和通奸的人。

5不要贪爱钱财,要对自己拥有的知足,因为上帝说过:

“我永不撇下你,也不离弃你。”

6这样,我们可以放胆地说:

“主是我的帮助,

我必不惧怕,

人能把我怎么样?”

7你们要记住从前带领你们、把上帝的道传给你们的人,留心观察他们一生如何行事为人,效法他们的信心。 8耶稣基督昨日、今日、直到永远都不改变。 9你们不要被五花八门的异端邪说勾引了去,因为心中得到力量是靠上帝的恩典,而不是靠饮食上的礼仪,这些礼仪从未使遵守的人受益。

10我们有一座祭坛,坛上的祭物是那些在圣幕里工作的人没有权利吃的。 11大祭司把祭牲的血带进圣所作为赎罪祭献上,而祭牲的身体则在营外烧掉。 12同样,耶稣也在城门外受难,为要用自己的血使祂的子民圣洁。 13因此,让我们也走出营外到祂那里,忍受祂所忍受的凌辱吧! 14我们在地上没有永远的城,我们寻求的是那将来的城。

15让我们靠着基督,常常开口以颂赞为祭献给上帝,这是承认主名的人13:15 承认主名的人”希腊文是“承认主名的嘴唇”。所结的果子。 16不可忘记行善和帮补别人,因为这样的祭是上帝所喜悦的。

17要顺服引导你们的人,因为他们为你们的灵魂时刻警醒,将来要向上帝交账。你们要听从他们,使他们满心喜乐地尽此职责,不致忧愁,否则对你们毫无益处。

18请为我们祷告,因为我们自信良心无愧,凡事都愿意遵行正道。 19也请你们特别为我祷告,使我能够早日回到你们那里。

祝福与问安

20愿赐平安的上帝,就是那位凭着立永恒之约的血使群羊的大牧人——我主耶稣从死里复活的上帝, 21在各样善事上成全你们,好使你们遵行祂的旨意,并借着主耶稣在你们心中动工,使你们做祂喜悦的事!愿荣耀归给上帝,直到永永远远。阿们!

22弟兄姊妹,我简短地写信给你们,希望你们听我劝勉的话。 23你们知道,我们的弟兄提摩太已经被释放了。如果他及时来到,我会与他一起去看你们。

24请代我问候所有带领你们的人以及众圣徒。从意大利来的人也问候你们。

25愿恩典与你们众人同在!

Hausa Contemporary Bible

Ibraniyawa 13:1-25

Gargaɗin ƙarshe

1Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar ’yan’uwa. 2Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba. 3Ku riƙa tunawa da waɗanda suke a kurkuku kamar tare kuke a kurkuku, da kuma waɗanda ake gwada musu azaba, kamar ku ake yi wa.

4Aure yă zama abin girmamawa ga kowa, a kuma kiyaye gadon aure da tsabta, gama Allah zai hukunta masu zina da kuma dukan masu fasikanci. 5Ku kiyaye kanku daga yawan son kuɗi, ku kuma gamsu da abin da kuke da shi, gama Allah ya ce,

“Ba zan taɓa bar ka ba;

ba zan taɓa yashe ka ba.”13.5 M Sh 31.6

6Saboda haka muna iya fitowa gabagadi, mu ce,

“Ubangiji ne mai taimakona; ba zan ji tsoro ba.

Me mutum zai iya yi mini?”13.6 Zab 118.6,7

7Ku tuna da shugabanninku, waɗanda suka faɗa muku maganar Allah. Ku dubi irin rayuwar da suka yi ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu. 8Yesu Kiristi ba ya sākewa, shi ne a jiya, shi ne a yau, shi ne kuma har abada.

9Kada a ɗauke muku hankali da sababbin koyarwa dabam-dabam. Yana da kyau zukatanmu su ƙarfafa ta wurin alheri, ba ta wurin abinci waɗanda ba su da amfani ga waɗanda suke cinsu. 10Muna da bagade inda firistocin da suka yi hidima a tabanakul ba su da izini su ci.

11Babban firist yakan ɗauki jinin dabbobi yă shiga cikin Wuri Mafi Tsarki a matsayin hadaya ta zunubi, amma jikunan dabbobin akan ƙone su a bayan sansani. 12Haka ma Yesu ya sha wahala a bayan gari don yă tsarkake mutane ta wurin jininsa. 13Saboda haka, sai mu fita mu je wajensa a bayan sansani, muna ɗaukar kunyar da ya sha. 14Gama a nan ba mu da dawwammamen birni, sai dai muna zuba ido a kan birnin nan mai zuwa.

15Saboda haka, ta wurin Yesu, bari mu ci gaba da miƙa hadaya ta yabo ga Allah, yabon leɓuna da yake shaidar sunansa. 16Kada kuma ku manta yin aikin nagari da kuma taimakon waɗansu, gama da irin waɗannan hadayu ne Allah yake jin daɗi.

17Ku yi wa shugabanninku biyayya ku kuma miƙa kanku ga ikonsu. Suna lura da ku kuma za su ba da lissafi a gaban Allah. Saboda haka kada ku sa su yi fushi saboda aikinsu, ku sa su yi farin ciki. In ba haka ba za su iya taimakonku ba ko kaɗan.

18Ku yi mana addu’a. Mun tabbata cewa muna da lamiri mai kyau, kuma muna da marmari mu yi rayuwa ta bangirma a ta kowace hanya. 19Ni musamman, ina roƙonku ku yi addu’a, don a komo da ni a gare ku ba da daɗewa ba.

Albarka da kuma gaisuwa ta ƙarshe

20Bari Allah na salama, wanda ta wurin jinin madawwamin alkawari ya tā da Ubangijinmu Yesu daga matattu, wannan Makiyayin tumaki mai girma, 21yă kintsa ku da kowane abu mai kyau domin aikata nufinsa, bari kuma yă aikata abin da zai gamshe shi cikinmu, ta wurin Yesu Kiristi, a gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada. Amin.

22’Yan’uwa, ina roƙonku ku yi haƙuri da wannan gargaɗi, don ba wata doguwar wasiƙa ce na rubuta muku ba.

23Ina so ku san cewa an saki ɗan’uwanmu Timoti. In ya iso da wuri, zan zo tare da shi in gan ku.

24Ku gai da dukan shugabanninku da kuma dukan mutanen Allah.

Waɗanda suke Italiya suna gaishe ku.

25Alheri yă kasance da ku duka.